KYAN DAN MACIJI.........
By Zulaihat Aliyu Misau
Part 10
Wattpad@zulaihatualiyumisau
No comment, no vote, no update on time, eheee...
🐍. 🐍
Not edited.....
" sosai ma, wasu magan -ganun ma sai kinji, wa'annan ne sukafi min zafi."
Numfashi Haj Kubra taja " zan kuwa yi maganinsa, na taba min gudan jini na." " Ummi ki barni dashi, sai zaman gidan nan ya ga gareshi." " aa zan gayawa tsohonsa ya ja masa kunne, bashi ba shiga har kar ki. Har yaushe yayi ilmin da zai kira ki jahila? Ban san daya part din kakan nin saba ko akwai mayu, ya lakaba miki kyan dan maciji ina zan yi shiru a cuce ni.?" " shi kenan, amma nima sai na koya masa hankali."
" ya maganar da mukayi dake, naji shiru?" Haj Kubra ta tambaya dariya Sabrina tayi, ta rage muryarta sosai " ban masa maganar ba, na bari sai yazo tukun, da this week zai zo, amma yanzu sai next week, duk yadda mukayi zan kira na gaya miki." Murmushi Haj Kubra tayi, har Sabrina najin sautin murmushin nata. " yauwa yar' albarka, ki tabbatar kinyi duk abinda nace kiyi, ina fatan yayanki bai sani ba ko?" Rike baki Sabrina tayi, tare da zaro ido " wai!!!! Ina!!!! Ai da na shiga uku." " yauwa karki gaya masa, ni da kaina zan masa maganar bayan naji yadda kukayi." " shi kenan Ummi na, that why I love u so much. " haka suka ci gaba da tattaunawa Allah known what they discourse.
Muh'd yana isa wurin John, ya sameshi tare da Babangida. Babangida shi ya kewa wasu daga cikin yan compound din wanki da guga, sun saba sosai da muh'd. Jansa yayi suka fita, don yau yana da burin aikawa da sako arewa, babangida kuwa dan garine, a kalla yakai 10years a Lagos, shi yasa in fita irin haka ta kamashi tare suke fita.
***********"*****
" ka ja masa kunne sosai, bashi ba yarinyata, in ba haka ba ni da kaina zan iso har Lagos in ci ubansa. Sannan dama ina son in tambaye ka? Ka cemin goge- goge da shara ya keyi a ma'aikatar taku? A ina ya ke samun Kudin da ya kewa iyayensa hidima haka, kamar shine oga a wurin.?"Jibrin da tunda Haj Kubra ta fara zazzaga masa kansa na kasa, kamar yana a gabanta. Cikin damuwa " albashin sane, sai alkhairin da yake samu, musamman wurin ogansa, don yana son shi, yana jin dadin aikinsa, bayan nan kuma yana koyar da yaranmu muna biyansa duk wata." " ehhhh!!!! Ka mishi hanyar arzikin kuma ka biyashi Kudin karantar da ya'yanka karatu? a'a lallai ne kam, shi na haifawa kai kenan?" " haba Ummi me yayi zafi haka? Ki lura shi bashi da wani nauyi yanzu a kansa, banda iyayensa biyu, sai shi don haka be kamata kiyi mamakin abunda zai musu ba. International Company ne, salary din da ban- banci da sauran ma'aikatu, muh'd yarone mai natsuwa ba shashanci a al'amarinsa."
" Aifa naga alama, yanzu dai ya maganar aikin yaron kawata da na maka magana?." Ajiyar zuciya ya sauke " ta nanan, da zarar an samu vacant zan tura masa." " to shi kenan, shima ko sharar ne a nema masa, tunda naga akwai ci itama." Murmushi jibrin yayi, yana mamakin ummin nasa. " shi kenan. Amma kinsan yaranmu baza su iya wannan aikin ba, balle in sunga suna da kwalin degree, ga degree ga degree din girman kai." " kai dai kayi abinda na ce maka kawai." " shi kenan Ummi. "
" ka gaida yaran, Allah yayi albarka." Ta fada tare da katse kiran.Kanshi ya daura a kan table din gabansa, zuciyarsa na zafi, lamarin Sabrina ya fara damunsa, har yaushe komai ya faru zata kira Ummi ta gaya mata? Menene anfaninsa in har bazata kawo masa complain dinta ba? Yana iyaka kokarinsa wurin kaucewa bacin ran iyayensa, amma abun yaci tura, kuma duk Sabrina ce ke zama Ummul aba'is din komai. Da case din iman da Haj Kubra tayi tsalle ta dire kan bata yadda ya nema ma iman makaranta ba, sai dai in faridatou zata dauki nauyin karatun, kai bama ta yadda Iman ta zauna dasu ba, don a cewarta don ganin Sabrina ne a gabansu yasa faridatou ta dauko kanwarta, don tama Sabrina kishiya, to bata yadda ba, dole Iman ta koma Niger. bai gama da wannan ba ta kara kunno wani case din. Ya rasa yadda zai bullowa lamarin, shi ba abun ya kira Abunsu ya gaya masa ba, tunda shi yace yaji ya gani zai iya.
Ranar gaba daya haka yayi aiki sukuku cikin damuwa da neman mafita.

YOU ARE READING
KYAN DAN MACIJI ( Completed )
Romanceyana dauke da fada karwa, nishadan tarwa, ilmantarwa, soyayya. akwai sakonni da yawa a cikinsa. in bakya comments ko vote! please don't read my story.