KYAN DAN MACIJI.........
By Zulaihat Aliyu Misau
Part 21
Wattpad@zulaihatualiyumisau
No comment, no vote, no update on time, eheee...
🐍. 🐍
Not Edited...........
Da sauri ya karaso gadon ya hau tare da tattaro Sabrina dake jijjige - jijjige zuwa jikinsa, kiranta ya fara ganin it's no used yasa ya fara karanto kula'uzai yana tofa mata. Anty fari tuni ta fashe da kuka ganin halinda Sabrina ke ciki. Hajiya ma sai yanzu hankalinta yaje kan addua, itama ta fara karanto duk wata adduar da taxo bakinta.
Wani ihu da gurnani Sabrina ta fara mai tsananin firgitarwa, da gudu Anty fari tayi waje cikin tashin hankali, kofar Muhd taje ta fara bugawa, cikin bacci ya fara jin nocking a gogon wayarsa ya duba 2:14 jin bugun kofar ba kakkautawa yasa ya mike a fusace. Ganin Anty fari yasa ya fito sosai, a rikice ta fara masa bayanin halinda ake ciki. Dakin ya koma ya zura jallabiyyarsa tare da yafa head scarf saman kansa zuwa kafadunsa. Har lokacin Anty fari na tsaye a waje tana jiransa, gaba tayi yana binta a baya har dakin Sabrina.
A bakin kofar dakin ya tsaya, lokacin gaba daya su yaya kuka suke duk da har lokacin sunata tofa mata addu'oi sai wani gurnani take tana tirje-tirje kamar mai son kwacewa daga hannun wani abu, Cikin kuka Yaya yacewa Muhd ya karaso. A hankali ya tako zuwa bakin gadon, kallonta ya tsaya yi for some second sannan ya sa hannunsa ya damki kanta hakan yasa yaya ya gyarata da kyau a jikinsa. Karatu ya fara yi, cikin zazzakar muryarsa da kwarewa da tsantsar fito da tajweed. Wani nishi ta fara, sai kuma ta fara ihu!!!! Still bai saki kanta ba, zuwa can kuma sai ta daina jijjige - jijjigen sai numfar-fashi, kallon yaya yayi " ina bukatar zam-zam in akwai?" Ya tambaya da sauri Anty fari ta fita don kawo zam-zam din. Hajiya kubra da gaba daya tashin hankali ya gama baibayeta ta mike tana nunawa Muhd dake tsaye yadan sun kuyo kan ya zauna, shiru yayi da kamar bazai zauna ba, sai kuma ya zauna still yana ci gaba da karatun. Tayi shiru kamar mai bacci sai idonta da suketa rawa duk da suna rufe, sai jikinta daya dau zafi sosai, tana sauke ajiyar xuciya. Sauke hannunsa yayi yama yaya alamar ya tasheta, sunanta yaya ya kira yana dan buga kumatunta kadan. A hankali ta fara bude idonta. Dai -dai shigowar Anty fari da jarkar zam-zam da cup. Amsa yayi ya tashi ya koma kujerar gaban mirror dinta ya zauna ya zuba zam-zam din ya fara karanto addu'oi a cikin.
Da kallo ta fara binsu idonta na zubar da hawaye. Hajiya kubra ta dawo wurin da Muhd ya tashi tana kallon Sabrina cike da tausayawa, Anty fari ma matsowa tayi tana mata sannu.
Anty fari ya mikawa zam-zam din da yayi addu'oi a ciki, yace ta bata tasha sannan ta shafa a jikinta. Ya mike zai fita, sai kuma ya dawo " tayi alwala kafin ta sake kwanciya bacci.'' Ko kafin su furta wani kalma ya fita a dakin. Hajiya kubra ce ta bata zam-zam din bayan Yaya ya tallabota, sannan ta koma ta kwanta. Minti kafan ta fara shakuwa can kuma sai ya tsaya. Alwala Yaya ya sata tayi kafin ta koma ta kwanta, Hajiya kubra nadan shafa kanta, minti kadan bacci mai cike da Niima da salama Wanda rabonta da irinsa har ta manta ya kwasheta. Hakan yasa hankalinsu yadan konta.
" tun yaushe hakan ke faruwa, aka rasa wanda zai gaya min?" Hajiya kubra ta tambaya tana kallon su Anty fari. " wallahi umma ban saniba, don ban taba ganin tayi hakan ba sai yau." Yaya ya fada. kallonsu Hajiya kubra keyi cike da mamaki " wane irin sakacine wannan? Kanwarka na irin wannan abun kace baka saniba? Ni dama tunda naga ramarta nasan akwai wani Abu a kasa." Ta fada cikin bacin rai
" Allah umma ban bamu taba sanin tanayin hakan ba, kuma wallahi kwana biyun nan ni kaina kusan kullun saina tambayeta, amma sai tace ba komai." Yaya ya fada

YOU ARE READING
KYAN DAN MACIJI ( Completed )
Romanceyana dauke da fada karwa, nishadan tarwa, ilmantarwa, soyayya. akwai sakonni da yawa a cikinsa. in bakya comments ko vote! please don't read my story.