Page 41 and 42

2.3K 94 10
                                    

🌧🌧🌞🌞🌧🌧🌞🌞🌧🌧
*🙆‍♀🙆‍♀ MAGANIN MATA‍👩‍👩‍*
🌧🌧🌞🌞🌧🌧🌞🌞🌧🌧
🤦‍♀🤦‍♀'''Damuwa'''🤦‍♀🤦‍♀

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
©
*eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*

*Dedicated to my besty Firdausi Mainasara(Feeby)*

4⃣1⃣-4⃣2⃣

Kusan kwana ammi tayi tana saka abubuwa da dama a zuciyan ta.
Ta saka wannan ta kwance wancan haka dai tayi ta yi tana neman mafitan yanda zata ankarar da Fudel daga wautan da take yi, idan ta tuno da abinda take shirin sakawa a zuciyan ta sai tausayin Khairy ya addabe ta, ta sani cewa abu ne mai matuk'ar wahala ga yarinya k'arama irin Khairy.
Kusan kwana uku take abu d'aya daga baya ta yanke hukuncin tunkarar Abba da maganar.
Yammacin asarar Abba ne zaune a parlour yana sauraran wa'azi dangane da zaman takewan ma'aura ta, Ammi na kitchen tana tuk'a tuwon semovita.
Sosai hankalin shi ya tafi ga talabijin d'in, a yanda baya nan malamin yake zuwa mishi tamk'ar ana bayani ne kan gidan d'an nashi.
Sallama aka mishi ya amsa tare da d'auke idon shi ya maida kan wacce ta shigo, murmushi yayi mata yana cewa" a'a ta k'arfen har kin fito ne?
"eee wallahi na kwaso wankin da nayi ne d'azu duk gajiya ta kamani shine ya koma d'aki na kwanta, yan zu ma gajiya nayi da zaman shiru nace bari na fito".
Babu wanin nan ragwanta yayi mishi yawa d'an wankin nan da kika yi shine kike cewa kin gaji?". Gyara zama tayi tace" uuhhmm haba!! haba!! dai malam ai ko Ammin yara baza ta gwada min zafin nama ba, tana murmushi k'asa-k'asa.
Ba dai matata ba kam amma zafin nama ai ba ki kaita ba, kin gan ta nan ko kwana zata yi tana aiki bata tab'a nuna gajiyan ta a fili".
Shigowan ammi kenan da try na abinci a gaban ta ta tarar suna hirar su, sallama ta yi musu tare da d'irewa a gaban Abba tana bud'e kulolin tana cewa" kai kam Abban Fudel baka gajiya da tsokana ji yanda ka sako min k'anwa a gaba da tsokana".
"Au haka ma zaki ce? ai k'anwar taki ce ta ga tamfatsetsen saurayi ta lik'e mishi".
Dariya suka saka su duka. Na zuba maka maka abincin ne yanzu? A'a da kin barci tukun naji ana k'iran sallar Magrib bari na hanzarta naje masallaci idan na dawo na ci".
"Au to shikenan". Mekewa suka yi su duka Abba ya nufi masallaci, suma suka d'aura alwala suka shige d'akunan su domin gabatar da tasu Sallar.
Abba ba shi da dawo ba sai da ya jira aka yi sallar Isha kana ya dawo gidan dan ya tsaya yayi karatun Qur'ani.
Bayan ya dawo aka gabatar mishi da abinci su Ammi kam tuni suka ci nasu. Sai da ya gama ya matsa kana small Ammi tace" ummmmm dama na zo maka da wata magana ce ko kuma wata shawara da ni a tunanina nake ganin zai amfane mu baki d'aya".
Tattara dukkan hankalin shi yayi ya maida kanta tare da tsare ta da ido yace" ina sauraren ki". Wato dama tunani nake me zai hana mu had'a Khairy da d'an uwanta Fudel aure ina ganin hakan zai sa ya samu nutsuwa". Murmushi Ammi tayi na nuna tsantsar farin cikin dan tun kallon da ta ma Khairy na farko ta kwad'aita ma d'an ta auren ta, amma tana ganin yarinyar tayi kankanta ta iya zama da Luby. Kina ganin bamu zalunce yarinyar nan ba idan muka had'a ta da wacce ta fita gogewa?
Da sannu za ta koya zama da ita, idan bamu yi amfani da Khairy ba wa kuke ganin zata jure ayi wannan gwagwarmayar da ita? Balle ma an tun-tub'e shi da ya fito da wacce yake so ya k'ara aure ya k'i so we don't have any other choice mu fawwala was Allah komai, shi ya san sirrin da ke tattare da zamantakewa na auratayya tsakanin su.
Kwarai wallahi na yaba da namijin k'ok'arin da kika yi, tabasss abu ne mai matuk'ar wahala ga Khairy amma ina da yakinin gaba zata ci ribar biyayyan da ta mana, to amma wani hanzari ba gudu ba ya kamata mu ji daga bakin Khairy kar mu yanke hukunci ita kuma tana da wanda take so, Abba ya fad'a.
"Hmmmm bana tunanin tana da wanda take so, kuma ko da tana da shi na san ita mai biyayyace a gare mu amma tunda kuka ce haka shikenan.
Haka dai suke ta tattaunawa daga baya small ammi tayi musu sai da safe ta shiga d'aki ta kwanta.

MAGANIN MATAWhere stories live. Discover now