Page 47 and 48

1.7K 103 15
                                    

🌧🌧🌞🌞🌧🌧🌞🌞🌧🌧
*🙆‍♀🙆‍♀ MAGANIN MATA‍👩‍👩‍*
🌧🌧🌞🌞🌧🌧🌞🌞🌧🌧
🤦‍♀🤦‍♀'''Damuwa'''🤦‍♀🤦‍♀

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
©
*eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*

*Dedicated to my besty Firdausi Mainasara(Feeby)*

4⃣7⃣-4⃣8⃣

Gyara kwanciya ta yi kamar da gayya cibiyar ta ta bayyana a waje" wow", ya fad'a a k'asan zuciyar shi. Tsintar kan shi yayi da zuwa inda take, ya tsugunna a gefen ta yana k'are ma fuskarta kallo.
Da ma haka yarinyar take da kyau? Dubi surar jikin ta mai kyau da d'auke hankali, i'm carried away, abinda ya fad'a a k'asan zuciyan shi.
Heart d'in shi na raya mishi kamar ya tab'a lallausan fatar ta da tun d'azu suka d'auke mishi hankali suka hana shi katabus but sai bai yi hakan ba sabida sanin kan shi ne babu aure a tsakanin su.
Jikin ta ne ya bata kamar ana kallon ta, cikin magagin barshi ta bud'e ido a hankali tana turo baki cike da masifa zaton ta ko Hafsy ce.
Tana had'a ido da shi za ta kwala k'ara yayi saurin manna ta jikin shi tare da rufe bakin ta yace" keeee me ya haka"?
Niman raba jikin ta da nashi ta soma yi tana fidda kwalla".
K'aramin tsaki ya ja tare da ture ta gefe yace" me kike wani kuka dan an tab'a jikin ki ko kin manta samarin ki na can sun saba holewa da jikin ki? Ina fact ma me kike da shi ne?
Kallon shi tayi cike da tsiwar tace" ka bar jifa na da munanan kalamai, zama a outside country doesn't mean that mace y'ar iska ce,
" Ni kike d'aga ma murya ko?"
"eeyyyee an yi k'arshen ta dai ba kashe ni zaka yi ba.
Matse ta yayi a jikin bango tare da jan suman ta k'arfi yace" ku shirya za mu gidan su Abba yanzu and mind you kar ki sake ki k'arb'e tayin su, what ever abinda zai faru ya faru you hear?
Hawaye na bin fuskan ta ta d'aga mishi kai ba dan ran ta ya so ba.
Saurin sakin ta yayi ya fice daga d'akin ya yaye sama domin d'auko car key.
Shigowan Hafsy d'akin kenan ta fito daga kitchen ta tsare ta da tambayar me ya same ta.
K'asa bata amsa tayi, nan ta fad'a mata abinda ya'yan nasu yace. Sauya kaya suka yi suka fito su duka cikin sa'a suka tarar yana saukowa kenan daga matakalar benen, a tare suka fice daga gidan su duka.

A gidan Hussy kuwa tun da Luby ta k'ira ta a waya ta shaida mata ta dafa nata maganin hankalin ta ya tashi dan ita tsoro take ji kar ta yi amfani da maganin daddyn Saleem ya k'i yi mata.
Bud'ewa ta yi ta tafka uban tagumi tana kallo, tirkashi, wannan shi ake k'ira da ga k'oshi ga kwanan yunwa.
Da dai ta ga abin ba mai k'arewa bane ta rufe maganin, ta shige d'akin daddyn Saleem a kwance a kan bwd. Gwiwa zube a k'asa ta hau magiya" only please kar ka min haka, don't avoid me mana haba nawan.
Ko sauran ta bai tsaya yi ba ya gyara kwanciyar shi. "Look Hussy ki kyale ni mana wacce irin fitina ce haka kin manta tun d'azu nake fama da rashin lafiya? Me kike so na miki.
Kwantar da murya tayi cikin tsigar jan hankali" I'm surpriced baby ni kake k'ira?, Ohhhh come sweetheart let me feel you even once.
" Ke idan zaka fita ki fita, totally yau ba zan iya biya miki bukata ba i'am weak, ban da sauran k'arfi a jiki na".
Da ta ga abin ba mai k'arewa bane ta mik'e kamar wanda ruwa ya ci ta tayi hanyar d'akin ta dan bata jin za ta iya had'a shimfid'a da daddyn Saleem ba tare da wani abu ya shiga tsakanin su ba.
Cikin d'agun murya yayi magana da k'arfi ta yanda zata iya ji" idan kin fice ki k'ira min Murja ta bani magani na, and kuma ta gyara min bed nayi barci".
Takaici ne a ishe ta, me mutumin nan yake nufi da ita bayan ya k'i biya mata bukata kuma ya sending d'in ta k'iran Murja mtswww.
D'akin Murja ta nufa ba dan ran ta ya so ba, ta tarar da ita ta fito wanka kenan ta shafa mai tana kwalliya. Kallon ta ta tsaya yi for some minutes" Murja wannan kwalliyar fa sai kace wacce za ta party". Shu'umin murmushi Murja ta sakar mata tare da d'auko wata arniyar matsetsen rigar barci ta saka" auntyna kenan sai mai zuwa party zai yi kwalliya?
A zamanin nan namu mace bata zama haka sai tana tsaftace jikin ta.
"Yab'e baki tayi tace" uuhhmm ke kike san wannan, maza-maza hanzarta da sauri ki bar wannan shiriritar taki, daddyn Saleem tana neman ki ki gyara mishi d'aki.
"Oohhhh auntyna barci nake ji fa, ta fad'a tana marairaice fuska, this night zan je d'akin nashi?
"Me zai hana Murja ai an zama d'aya".
Matso hawayen munafurci tayi, Allah auntyna bana son nayi abinda zai kawo zargi tsakaninsa da ke".
Dafa ta tayi tana mai jin son ta a zuciyan ta, Murja kenan d'iyar kirki, na yaba da hankalin ki na san baza ki tab'a watsa min k'asa a ido ba.
D'auko hijabi tayi dogo har yana kan k'asa ta rufe jikin ta, a tare suka bar d'akin, Murja ta soma hawa matakalar d'akin daddyn Saleem Luby ta tsai da ita.
" Ki kula da aikin ki sosai Murja, make sure kin gyara mishi d'akin da kyau ta yanda zai ji dad'in barci, make sure kin mishi gyara da baki tab'a yi mishi ba.
Juyowa tayi tace" your wish is my command aunty na, idan dai wannan ne kar kiji komai, da ban kware a harkar gyara gado ba daddyn Saleem ba zai nemo miki ni ba,
"Haka ne, sai da safe".
" Alright mu kwana lafiya", Murja tayi saurin shigewa ta bar ta a wurin daga baya ita ma ta shige d'akin ta ta tarar da yaran ta suna barci.
Samo wuri tayi ta kwanta a gefen su hankali kwance, can barci yayi awon gaba da ita.

B'angaren su Khairy kuwa suna isowa gidan su Abba kamar dama jira iyayen nasu suke yi suka tarar da su a parlour.
Samo wuri suka yi suka zauna tare da gaishe su d'aya bayan d'aya suna amsawa.
Fira suke ta yi mai dad'i ban da Fudel da tun shigowan shi yake cikin tashin hankali.
Minti 10 suka d'auka suna hira kana dad ya dube Fudel yace" ina sako na hope dai ka taho min da shi".
" A'a Abba bamu samu daman tsayawa a hanya ba, kuma na ga kamar kar ayi ma yarinyar dole tana tukuna da k'uruciyar ta, da dai an bi abin a sannu in ya so zuwa gaba ayi.
" to uba na ji", to baza a bi ba.
Juyawa yayi kan Khairy yace" Ummulkhairi zo nan, matsa gare ni akwai wata muhimmiyar maganar da nake so muyi da kai".
"Kamar yanda ya ba ta umurni hakan ta yi".
"Idan na miki zab'in mijin aure zaki ammince?, ko dai kina da wanda kike so? ya tsare ta da ido.
Sosai abin ya d'aure mata kai ta rasa abin da zata ce, Fudel ya zuba mata ido cikin tashin hankali.
"Murmushi manyan mutane yayi mata, na san na d'aure miki kai bari na fito miki a mutum".
"Ummul Khairy". "Na'am Abba".
Wato Khairy aure muke so mu had'a ki da ya'yan ki Fudel, shine muka yanke hukuncin tunkarar ki mu ji ta bakin ki, shin zaki iya share mana hawaye ki aure d'an uwan ki Fudel?
Rasssss gaban ta ya fad'i cikin tashin hankali ta d'ago ido tana kallon Fudel da kallo d'aya zaka miki ka hango tsantsar bala'in ciki a fuskan shi, gefe kuwa tunanin maganar Ammin ta ya fad'o mata a rai, sai yanzu ta gane dalilin k'iran nata,hak'ik'a ta samu damar da zata kuntata ma Fudel, amsa tayin auren Fudel shine umurnin mahaifiyar ta da kuma rayuwar gayya a kan Fudel, amma yin hakan tamk'ar ta jefa kan ta a cikin rami mai cike da tarin macizai. Bijire ma bukatar su shine kad'ai hanyar da ta dace ta yi.
D'ago fuska tayi ido cikin ido suka kurawa wa juna ido ita da Fudel yayin da zuciyoyin su ke ta harbawa da sauri, suna mai fargaban abinda zai biyo baya.



*eedatou*

MAGANIN MATAOnde histórias criam vida. Descubra agora