Chapter One

91 4 1
                                    

Yau ma kamar kullum suna tsaye a kofar class bayan fitar malamin biology, Wanda ya kasance shine darasin su na ƙarshe a kowace ranar talata. Sun kusan ɗaukar a ƙalla mintina bakwai suna tattaunawa game da darasin da suka gudanar kafin suka miƙa zuwa bakin gate din makarantar.
Makaranta ce babba wanda ya amsa sunan sa sannan kuma sai 'ya'yan wane da wane ne suke samun damar karatu a wurin. Isar su keda wuya suka samu motar gidajensu sun zo ɗaukar su.
"Noor sai gobe kuma in Allah ya kaimu. Kuma Please kada ki manta da alƙawarin da kika mun yau. Sannan please poem din ya tsaru sosai duk da dai nasan cewa kedin ba baya ba wajen rubutun poems."
Wacce aka kira da Noor tayi murmushin da ya ƙawata kyakkyawar fuskar ta sannan tace
"Ke kam Hibba bakya gajiya da surutu na rantse. Jibi yadda kike ta zuba kamar 'ya'yan kurna."
"Noor yanzu ni ce mai surutu? Wai har kura ta ce da kare maye." Hibba ta faɗa tana nufar motar gidansu.
"Ki gaida mun da Ammiey da darling sweetheart ɗina." Ta ƙarasa faɗa tana bude motar.
Murmushi Noor tayi tana mamakin irin shakuwar dake tsakanin ƙaramin kaninta kuma autan gidansu da Hibba. Dan ko bata faɗa ba tasan Muhammad Jawad take nufi.
"Barka da rana yaya Auwalu." Ta gaisar da matashin drivern nasu dai-dai lokacin da ta zauna a mazaunin ta.
"Yawwa Noor ya makarantar?" Ya tambaye ta da sakin fuska. Shidai yarinyar tana matukar burge shi kasancewar ta mai girmama na gaba da ita. Shiyasa duk 'yan aikin gidan suke sonta sosai. Kasancewar Auwalu driver ya dan yi makaranta shima sai ya zamana duk lokacin da yaje daukar ta sai suyi ta hirar makaranta har su iso gidan. Yauma kuma hakan ce ta kasance.
Isar su gidan babu bata lokaci ta sauka daga motar tana masa godiya kamar yadda ta saba sannan ta shiga cikin gidan inda ta iske Ammiey wato mahaifiyar ta tana ta faman girke girke.
"Good afternoon Ammiey na." Ta faɗa tana zama a daya daga kujerun dan madaidaicin dining table din dake kitchen din.
"Afternoon Noorie ya makarantar?" Ta tambaya ba tare da ta kalli diyar tata ba which seems weird.
"Lafiya klau Ammiey. Mom ina Jay ban ganshi ba."
"Sun fita Masallaci da mahaifin ku." Ta bata amsa a takaice.
"Ok." Shine kawai abun da Noor ta faɗa tana ficewa daga kitchen din ganin mahaifiyar ta kamar bata son doguwar magana.
Tana shiga dakinta uniform Ta fara cirewa kamin ta shiga tayo wanka tare da dauro alwala. Kammala sallar ta keda wuya sai ga Jawad ya shigo da gudu ya faɗa jikinta.
Murmushi tayi ta hau tambayar sa ya makarantar su yana bata amsa. Zama sukayi daga ita har shi din suna hirarsu gwanin ban sha'awa. Sai kusan karfe biyu da rabi Ammiey ta aika aka kira su don cin abinci.

*****

"Amma baka ganin bamu kyauta wa Noor ba idan muka mata haka." Ammiey ta faɗa tana kallon mai gidan ta.
"No Juwairiya. Let's not do this now. Ba mun gama magana ba. Ki tuna fa Janna ta fara girma kuma kinsan hakan kawai shi zaisa muyi nasara wurin samun wannan contract din."
"Haba dear meyasa kake son saka rayuwar 'yarka a matsala saboda kasuwancin ka yayi karfi? Kar ka manta fa Noor is just 17 taya kake tunanin aurar da ita ga wanda bai san taba kuma itama bata san shi ba? Taya hakan zai kasance?" Ta faɗa daidai lokacin da wani siririn hawaye yake fita daga idon ta.
"Look sweetheart, kema kinsan bazan taba cutar da 'yata ba. Ni nasan wanene JUNAID kuma nasan ba zai taba cutar da ita ba. Besides mahaifin shi Alhaji Arabi is my friend and also a business partner. Saboda haka ina so ki kwantar da hankalin ki inshaallah babu abinda zai faru sai alkhairi." Ya faɗa trying his best to make her understand.
" Amma baka tunanin mu fara jin ra'ayin ta game da hakan?"
"Meyasa kike yi kamar baki san halin 'yar ki ba? Tana da biyayya na tabbatar zata amince da kudirin mu."
"Shike nan Allah ya shige mana gaba." Shine abun da tace ba wai dan ta yarda da abunda maigidan nata ya faɗa ba. Ita a ganin ta yakamata su nemi shawarar 'yarsu kafin zartar da irin wannan babban al'amari akan ta. Amma ba komai. Zata cigaba da mata addu'a dan tasan shine kadai abunda 'yar tasu tafi bukata.
Kitchen ta wuce direct don tabbatar da komai yana tafiya daidai yanda ya kamata kasancewar a yau ne Junaid da mahaifinsa zasu kawo musu ziyara.
Zuwa karfe shida komai ya kammala har an jera abinci bisa dining table kawai jiran bakin suke su iso.
Ammiey ce zaune ita da 'ya'yan ta bayan sallar isha a sitting room suna hirarsu kamar yadda suka saba. Amma yau hirar yawanci akan bin iyaye take yinshi wanda za'a iya kira kai tsaye da hannun ka mai sanda.
Ƙarar door bell suka ji wanda ko ba'a faɗa ba sun san dad ne ya dawo. Noor ce ta mike kai tsaye ta isa kofar tare da bude kofar. "Welcome da..." Maganar ce ta makale a makoshin ta daidai lokacin da idanun ta suka sauka a cikin nasa idanun...

Fateedau📌

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now