Chapter Nine

14 2 0
                                    

Junaid bai dawo gidan ba sai kusan karfe uku. And thankfully, ya taho da boxes wanda ko ba'a faɗa ba tasan nata ne. Amma meyasa sai yanzu yake shigowa dasu bayan tun saura kwana 3 daurin aure aka tafi da akwatunan kayanta? Sannan wani abun da ya sake daure mata kai shine Ammiey ta bata pictures na furniture ta zaba and she chose sai dai basu ta gani a gidan nan da Junaid ya kawo ta ba. Me hakan ke nufi kenan?
Koda ya shigo gidan a parlor ya ajiye sannan ya juyo ya kalle ta. Duk ta fita hayyacin ta tayi wani iri. Fuska murtuke babu annuri ya nuna mata wani kofa dake parlon
"Wannan shine dakin ki."
Ya faɗa kamar ana masa dole wanda kuma kusan hakan ne dan tsakanin shi da Allah ya tsani kallon fuskar ta. Da zai samu dama wallahi har kashe ta zai iya yi dan duk lokacin da ya ganta ji yake kamar yayi ta dukan ta har sai ta dena numfashi. Jin idan ya cigaba da tsayuwa zai iya kikkifa mata mari yasa shi barin wurin ya haura sama. Tana jinshi ya banging kofar kamar zai balla ta.
Da sauri ta isa inda ya zuba boxes din ta shigar dakin da ya nuna mata. Daki ne madaidaici wanda yafi kowanne daki kankanta a gidan, sannan sai katifa da take saman gado shima madaidaici. Bayan nan babu komai a dakin sai kofar da zai leading dinka zuwa toilet. Daki ne da akayi shi purposely saboda mai aikin gida. Gefen gadon taje ta ajiye boxes dinta sannan ta bude ta ciro kayan buƙatar ta sannan ta wuce banɗakin. Ta dau kusan mintuna arba'in kafin ta fito. Godiya tayi wa Ubangiji dan sai yanzu taji kanta a daidai samun pad da tayi a cikin kayan ta dan dama duk a takure take saboda tissue paper sa take amfani dashi ya kare.
Parlon ta sake komawa inda ta hango jakar leda da yafi kama da na restaurant ta bude sai taga abinci ne a ciki. Allah sarki dama duk yunwa ya gama addabar ta dan komai cikin dauriya take yinsa. A wurin ta zauna ta fara aikawa cikin ta sako tanayi tana lumshe idanuwa har taji ta koshi. Tashi tayi ta dau sauran abincin ta wuce dashi daki ta ajiye dan zuciyarta ta bata ba lallai ya sake kawo wani abincin ba.
Ganin batada wani abun yi yasa ta kwanta ko bacci zai dauke ta. Wayar ta ta janyo dan tana son jin muryar Ammien ta da Hibba. Missed calls din Hibba ta gani har hudu wanda ta mata su a lokuta mabanbanta. Ammiey ta fara kira suka gaisa sannan ta daura mata da nasiha sannan sukayi sallama. Next ta Kira Hibba wacce sai da ya katse sannan ta sake kira kafin ta pick. Koda Hibba ta picking call din shiru tayi bata ce komai ba.
"Hibbaty I'm sorry nasan you are angry at me."
"Thank God kinsan abunda kika yi. Wato shine kika bi mijinki jiya ko sallama babu kin barni sai neman ki nake. Ba dan Allah ya hadani da wani abokin angonki ya fada min kun tafi ba da haka zan ta safa da marwa a titi ina neman ki. Kuma na dinga kiranki yau baki pick ba."
"Kin gama?" Cewar Noor cikin murmushi dan dama tasan dole ayi hakan.
"Au abunda ma zaki ce kenan? Good. Sai anjima." Hibban ta faɗa sounding pissed off.
"Sorry Hibba phone din baya kusa ne I'm sorry."
Haka ta cigaba da bata hakuri har ta sauka sannan suka daura da hira. Sai dai ko kadan Noor bata fadawa Hibba abinda ke faruwa ba. Sun dade suna hira kafin suyi sallama daga baya.
Ganin babu abinda zatayi ne kuma yasa ta kwanta dan bacci takeji sosai.
Cikin bacci taji ana bugun kofa tamkar za'a balle shi wanda hakan yasa cikin tsoro ta farka ya rarraba idanu. For a moment ta manta a ina take. Kallon dakin ta fara trying to remember where exactly take. Yanayin da ake buga kofar ne kuma cikin rashin sassauci yasa ta fara tunanin anya ba kidnapping dinta akayi ba? Then it dawned on her cewar gidan Junaid ne nan. Kuma dakin nan is her new room. Da sauri ta sauka ta isa kofar ta bude ta. Idanunsa sun gama rinewa tsabar baƙin cikin tsayuwar sa a wurin. Harara ya wurga mata kafin ya fara masifa hade da ihu
"Bakida hankali ne zanzo ina buga miki kofa amma kiyi banza da ni? Uban me kikeyi da kika rufe kofar?"
"I'm sorry Junaid bacci ne ya dauke ni." Janna ya bashi amsa innocently.
"Oh! Wato har kin samu bacci ko? To ba hutu kikazo yi ba aiki kikazo and if you don't have anything doing ki tsaya a parlor har sai in nine nace ki tafi. Useless brat."
Yana gama fada ya wuce ya fita ya barta a dakin. Da kyar ta koma kan gadon ta zauna jikinta duk yayi sanyi. Wannan wacce irin kaddara ce ta same ta? A ce washegarin auren ka yazo maka a haka? Tunani ta shiga yi lokacin da suke school inda take fantasizing rayuwar aurenta da wanda zata aura. Bata taɓa tunanin rayuwa zata juya mata haka ba cikin lokaci kankani. Hawayen idon ta ta share sannan ta mike ta fita.
Ledoji ta gani baje a parlon wanda hakan yasa cikin faduwar gaba da tsoron Junaid da take ji ta nufi ledojin. Shopping ne ta gani anyi na kayan abinci. Komai na bukatar yau da kullum a kitchen an hado babu abunda babu a ciki. Dauka tayi ta kai kitchen din ta jera komai a inda take buƙata kafin ta koma dakinta ta yi wanka ta kimtsa kanta sannan ta dawo kitchen din don ta girka abincin dare.
_______

Ga Noor a gidan Junaid. Wani irin rayuwa kuke tunanin zatayi? Shin zatayi rayuwar 'yanci kamar kowacce mace a gidan mijinta ko kuma akasin hakan ne zai kasance?

Sorry for the late update.
Taku har kullum, Fatima Dauda (Fateedau).
Not edited😲

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now