Chapter Ten

18 3 0
                                    

Cikin sauri, ƙwarewa hadi da zafin nama ta fara aikin ta. Sam bata dauki girki a bakin komai ba dan sometimes ita take girkawa a can gidan su. Saboda haka cikin azama take aikin ta. Tana cikin yi taji har an fara kiraye kirayen sallar magrib.
"Wow har lokacin sallah yayi." Ta faɗa daidai tana daukar albasa ta daura shi a chopping board tana yankawa. Bayan ta kammala yankan albasa ta dauko carrots, green beans da green pepper ta yayyanka su ta ajiye a gefe sannan ta cigaba da hada abincin ta. Nan da nan kamshi mai dadi ya gauraye ko ina. Duk wanda yaji aroma din kuwa tabbas sai yaso dandana girkin.
Zuwa wani lokaci ta gama komai ta zube shi a wata hadaddiyar kula mai shegen kyau tare da kaiwa dining ta ajiye sannan ta jera plates da spoons sannan ta koma ta yayyanka fruits da sauri ta haɗa wata hadaddiyar fruits salad ta sa a fridge sai ta blending pineapple and coconut ta tace shi ta haɗa juice dinta mai shegen dadi shima ta sa a fridge daidai an idar da sallar isha. Plate ta dauka ta debi nata daidai yanda tasan zata iya cinye wa dan ba laifi Noor ma akwai ci sai dai ba na fitar hankali ba. Daki ta kai ta ajiye sannan tazo ta debi fruit salad din da juice sannan ta koma ta rufe komai ta shiga wanka. Bayan kusan mintuna ashirin ta fito babu bata lokaci ta shirya cikin kayan baccin ta riga da dogon wando masu kauri ruwan madara sannan ta daura hula shima ruwan madara. Sosai kayan suka sake fitar da kyaun ta tare da zallar kuruciyar ta. Zama tayi a bakin gadon ta fara cin abincin ta a natse. Cikin mintuna talatin ta gama sannan ta wuce bathroom tayi brush. Tana fitowa kuma ta kwashi plates din da tayi amfani ta kai kitchen tare da wanke duk wasu abubuwan da ta ɓata.
Fitowar ta daga kitchen din yayi daidai da shigowar Junaid wanda rai a hade ya karasa shiga direct kuma ya wuce ya zauna a kujera two seater. Ganin ya zauna din ne kuma yasa Noor ta je ta kawo masa ruwa.
Bai ko kalli inda take ba balle ya nuna alamun yasan da wanzuwar wata halitta a wurin har ma tayi tunanin zai dauki ruwan ya sha. Still bata yi kasa a gwiwa ba ta sake cewa:

"Abincin ka na dining."
Bai kula ta ba sai ma sake tamke fuska da yayi.
"Should I bring it here?" Ta tambaya innocently.
A harzuƙe ya dago ya zuba mata rikitattun idanunsa masu sa shakku a zukatan mutane wanda a take taji bazata iya cigaba da kallon shi ba sai kawai ta sunkuyar da kanta kasa ta riƙo kasan rigar ta tana wasa dashi sai dai bata san cewa hakan da tayi yasa gaba daya illahirin halittar cikin ta na waje. Lura da tayi cewar ya kawar da idon shi daga kanta ne kuma yasa ta dan saci kallon shi sai dai ganin direction din da yake kallo yasa ta kallon wurin itama. Aikuwa karaf idon ta ya sauka a kan naked skin dinta kuma ya tabbatar da wurin yake kallo. Kamar kiftawar ido ta sake rigar har da kokarin janshi kasa. Shi kuwa Junaid dauke kai yayi kamar babu abunda ya faru.
"Je ki kawo."
Ya faɗa can ƙasan makoshi daidai lokacin da yake kwantar da kanshi a kujera hadi da lumshe ido. Ba dan hankalin ta na kanshi ba da baza ta ma san yayi maganar ba. Junaid ya amsa ne kawai bawai dan zaici abincin ba. Shi dai yasan ko daga bacci ya tashi bazai iya cin jagwalgwalon yarinyar ba dan ya tsane ta ya kuma tsane duk wani abu nata. Direct kitchen ta wuce ta dauko tray mai shegen kyau da sheki ta daura chilled juice din da tayi tare da fruit salad a kai tazo ta jera a gaban shi sannan ta koma dining din ta jero abincin da plates ta sake dawowa ta ajiye sannan ta bude da niyyar zuba masa. Ƙamshin hadaddiyar fried rice din da yaji kayan lambu da nama ne ya daki hancinsa har sai da ya lumshe idonsa yana shaka. Zuba ido yayi yana kallon yanda abincin ke tiriri. Wayar sa dake gefe ce ta dau kara alamun shigowar kira. Ba tare da ya duba mai kiran ba kawai ya pick dan ya san caller saboda ringtone din na daban ne.
"Hey princess."
Shine abunda kunnuwan ta suka jiyo mata bayan ya kai wayar kunne. Kasancewar dare ne kuma ko'ina yayi shiru yasa har take iya jiyo muryar princess din tashi kamar yadda taji ya fada.
"Baby kwana biyu na jika shiru and I tried reaching out to you but I couldn't. I'm so worried that I couldn't even eat. Hope you are fine." Princess ta faɗa daga dayan bangaren.

"Ni I'm very fine kar ki damu kanki. I was a little bit busy ne shiyasa ban nemeki ba."

"Ok har hankali na ya kwanta. Baby what about the topic we've been discussing lately? Ka ce zaka turo and I even informed my parents." Princess ta faɗa sounding kamar zatayi kuka.

Nan take mood din Junaid ya canza dan abinda ta faɗa gaskiya ne. He promised akan zai tura iyayen shi gidansu princess sai dai a daidai wannan lokacin ne aka bijiro da zancen auren shi da Noor. Sai yaji ya sake tsanar yarinyar ma gaba daya ko ganinta bai son yi. Yanzu ya zaiyi da princess kenan? Me kuma zai ce mata dan bata ma san da zaman Noor ba. Infact ma bata san an mishi aure ba. Yeah an mishi aure mana tunda ba son yarinyar da aka aura masa yake ba.

"Are you there?"
Firgit ya dawo daga kogin nazarin da ya faɗa.
"Yeah princess. Ban manta ba just give me some time to sort out some things. Inshaallah I will get back to you." Da kyar yayi maganar dan ranshi ya gama ɓaci ganin giftawar Noor ta gaban shi dan sai yanzu ta gama serving dinshi.
"Take care of yourself. Gotta go do some work. Good night and sleep tight." Kitt ya kashe wayar bai jira amsar ta ba.
"Hey Bitch!" Ya daka wa Noor tsawa har sai da ta kusa cin karo da kofar dakinta.
Still tayi a wurin bata dawo ba kuma bata shiga ciki ba.

"Ina magana kina tsaye?"
Bata ce komai ba ta juyo ta dawo gudun kar tayi laifi ya mata wani abun dan ta lura ba mutunci ne dashi ba.

"Ki kwashe wannan tarkacen bazan ci ba. I want you to go in there ki mun pounded yam and egg sauce yanzu. And if you dare waste my time..." Ya sata aikin ne kawai dan ya wahalar da ita bawai dan zai ci ba. Moreover ma baya cin abu mai nauyi da dare so ina shi ina cin pounded yam.

Kamar ruwa ya cinye ta haka ta tsaya. Tunani take ta inda zata fara hada pounded yam a daren nan. Anya mutumin nan na da imani kuwa? Karfe nawa ne ma yanzu da zai ce ta masa sakwara? Dubanta ta kai kan agogon bangon dake manne a dakin. Gani tayi tara na dare har ya gota. A sanyaye ta kwashi kayan da ta kawo ta mayar kitchen din daga nan ta ɗora ruwa a gas sannan ta dauko doya ta fere ta zuba sannan ta koma dayan gefen ta sake kunna wani gas din ta fara haɗa egg sauce din.
Aiki takeyi cikeda gajiya dan babu karya ta gaji sosai ga kuma baccin da takeji. Zuwa sha daya da wani abu ta kammala sannan ta ɗebo komai gwanin burgewa da sha'awa ta fito dashi. Ganin baya parlon kawai ta yanke hukuncin kai masa har daki.
Kusan mintuna biyar tana knocking amma bai bude mata ba har ta gaji ta koma kasa ta jera masa su a dining ta wuce dakinta da niyyar wanka da ruwan zafi sosai ko gajiyan zai dan saketa ko da babu yawa.

_______

Short chapter right🤔
Kuyi hakuri I promised an update today shiyasa.
Next chapter is going to be more than this. Stay blessed😇
Not edited.

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now