Chapter Five

16 5 0
                                    

Ammiey ce ke driving din Jawad kuma na zaune a gefen mai zaman banza Noor kuwa ta kwanta a backseat. Cikeda kwarewa Ammiey ta karyo kwanar shiga anguwar su inda ta tsaya daidai wani katafaren gida mai dauke da golden coloured gate ga wasu furanni da suka ƙawata gaban gidan. Horn ta danna nan da nan gatekeeper yazo ya bude masu gate ɗin suka shiga ciki. Tsayawa kwatanta ƙawatuwar gidan ma wani bata lokaci ne mai zaman kansa. Jawad ne ya fara sauka daga motar sannan Ammiey ma ta fito ta budewa Noor kofa itama ta fita.
A hankali take tafiya har suka shiga cikin gidan inda Noor kai tsaye ta wuce dakinta cikin sanyin jiki. Kallo kawai Ammiey ta bita dashi tana jin tausayin ta na ratsa duk wani sassa na jikin ta. Ƙwallar da taji yana kawowa idanun ta ta mayar sannan ta wuce bedroom dinta jawad kuma dama yun shigowar su yabi bayan yayarsa.
Ganin rana yayi yasa Ammiey wucewa kitchen ta daura musu girki. Cikin lokaci kankani ta dafa white rice kasancewar tana da stew a fridge hakan yada tana kwashe rice dinta ta maida stew din wuta ta dumama. Da sauri ta haɗa salad ɗin fa yaji kwai da mayonnaise dan tasan Noor na so sosai. Ina less than 2 hours ya gama komai ta shirya a dining.
Koda ta gama bata zarce ko ina ba sai dakinta ta gabatar da Sallah don tuni aka fara kiraye kirayen sallah a masallatai sannan ta wuce dakin Noor din. Dakin ta shiga dauke da sallama a bakin ta ta samesu suna kan yin tasu sallar. Tarbiyyar Ammiey kenan duk inda kake kana jin an fara kiran sallah ka bar duk abin da kake yi duk muhimmancin sa kayi sallah tukun. Murmushi tayi ta samu gefen gado ta zauna tana jiran yaran nata su idar.
Mintuna kadan suka kara kamin suka kammala harda addu'o'in su sannan suka taso suka zauna a gefen ta. Noor na gefen dama Jawad kuma a hagun ta. Shafa kansu tayi ta sa musu albarka dukkansu suna murmushi gwanin ban sha'awa.
"Tunda kun idar da sallar muje kuci abinci barin ma ke Noor da babu abun da kika sawa cikin ki." Mahaifiyar tasu ta faɗa tana mikewa daga zaunen da take.
"To Ammiey." Suka amsa a lokaci guda.
Kofa suka nufa su duka ukun hannayen su sarke da juna suna tafiya suna hirar abun da ba'a rasa ba. Idan mai karatu ya gansu a wannan lokaci dole ne su burge ka.
Suna isa dining din Noor tayi sauri ta janyo wa Ammiey kujerar zama. Tana tsaye bayan kujerar har sai da ta zauna. Juyawa tayi da niyyar janyo nata kujerar sai taga Jawad standing like the perfect gentle guy he is a bayan kujerar ta yana jiran ta zauna kamar yadda tayiwa Ammiey. Murmushi tayi ta dafa kanshi sannan tace "bless you lil bro" sannan ta zauna shima ya zauna. Kaunar dake tsakanin wadannan 'yan uwa guda biyu daga Allah ne. He's just six years old amma he sometimes behave older than his age.
Cikin natsuwa Ammiey tayi serving dinsu suka fara ci a hankali. Bayan kamar mintuna talatin suka kammala komai Noor ta wanke duk abubuwan da suka ɓata sannan ta tafi dakin Ammiey.
Zaune ta samu Ammiey a dakin tana waya Jawad kuma ya kwanta a sofa din dake dakin har ya fara bacci.
Sai da Ammiey ta gama wayar kamin ta dawo gefen 'yar ta ta zauna. Tabbas zatabi shawarar mahaifiyarta. Zata amince ayi auren. Kamo hannun Noor tayi ta fara mata magana cikin hikima da son fahimtar da ita abunda take faɗa.
"Noorie ki saurare ni da kyau kiji abinda zan faɗa miki. Regarding decision ɗin da mahaifin ku ya yanke a kanki, ina so kiyi masa biyayya don na tabbatar baze taba zaba miki abunda Zai cutar dake ba. Duk wanda yayiwa iyayensa biyayya tabbas baya taba ganin ba daidai ba a rayuwarsa. Saboda haka Please ki dena daga hankalin ki da yawan tunani inshaallah Allah na tare da ke."
Haka dai Ammiey ta rinƙa faɗa mata maganganu masu ratsa jiki har ta shawo kanta ta amince.
"To Ammiey na. Inshaallah zaki sameni mai biyayya a gare ku." Noor din ta faɗa cikin karayar zuciya. Ta yadda da auren ne kawai for the happiness of her parents. Amma deep down Allah ya sani tana jin tsoron abin da zai je ya dawo. Amma ba komai, bazata taba bijirewa iyayenta ba tunda abinda suke so kenan zatayi. Kuma zata jure koma menene dan ganin farin cikin su. Da haka dai Ammiey ta cigaba da bata baki har suka dibi lokaci mai tsawo a tare.

*****
A can bangaren dad kuwa aikinsa yake tukuru ba tare da damuwar komai ba. Duk da ya so komawa asibitin amma yasan muddin ya je toh ba makawa Ammiey zata sake bijiro mishi da zancen auren. Shi kuma har ga Allah bazai taba janyewa ba.
Knocking kofar akayi aka shigo. Sai da ya kai aya a aikin da yake sannan ya dago ya kalli wanda ya shigo ɗin. Alhaji Arabi Katagum ne tsaye sanye da farar shadda ƙal wacce tasha ɗinkin babban riga. Zama yayi suka gaisa sannan suka tattauna harkar business dinsu inda daga karshe Alhaji Arabi ya nemi da su fixing date din auren yaran cikin lokaci kankani. Babu wata damuwa dad ya amince da batun inda ya nemi family ɗin Alhaji Arabi dasu zo ranan Sunday for proper engagement.

Kamar yadda suka tsara hakan ce ta faru dan yau ta kama Sunday kuma magabatan Junaid sun zo inda uncles din Noor suka tsaida bikin zuwa sati uku masu zuwa.
Lokacin da Noor taji zancen numfashin ta ne ya katse ta samu dai ta laluba da kyar ta koma daki tayi kuka har saida taji nauyin da ƙirjin ta yayi ya ragu. Tashi tayi ta dauro alwala ta kabbarta sallah tana rokon Allah ya saukaka mata al'amuran nan. Ta jima tana addu'o'i kamin ta tashi tana naɗe prayer mat daidai nan kuma wayar ta ta soma ƙara...

Koda Junaid samu labarin an tsaida ranar bikin ranshi ne yayi kololuwar tashi. Murmushin karfin hali yayi yace
"Abba na gode Allah ya kara girma."

"Amin son. Sai ka kira ta kaji ko akwai abin da take buƙata."

"Abba ai bani da number ta." Ya fada dan dama yana bukatar number ta din quite alright. How could she? Upon all his warnings ta amince ayi auren? Me ta dauke shi ne wai? Me zaiyi da karamar yarinya haka 'yar under 18? Me zai aura a wurin? Amma gaskiya yarinyar nan ta raina shi da yawa. Amma shikenan shi zai gyara mata zama dan wallahi sai tayi danasanin amincewa wannan auren yayiwa kanshi wannan alkawarin!
Abba ne ya katse mishi tunanin da ya fada ta hanyar faɗin
"Are you with me son?"
"Eh Abba inaji."
"Zan kira Alhaji Mu'az sai ya turo min da number."
"Ok." Kawai yace a takaice.
Yana nan zaune har Abba ya gama magana da dad aka turo number sannan ya tafi dakin shi bayan ya dau lambar a watan shi.
Yana shiga bai wani bata lokaci ba ya danna wa Noor kira. Ga dai wayar tana ta faman ringing amma ba'a daga ba abin da ya sake tunzura zuciyarsa kenan.

Ita kuma Noor ganin sabon number ne yake kiranta yasa ta tsaya kallon number trying hard to remember ko ta san me number amma ganin number so special yasa kawai ta dauka daidai lokacin da yake kokarin yankewa ta kai kunne. Runste idanun ta tayi jin abinda ake faɗa daga dayan side din.

"You bitch how dare you? Wato ke ga 'yar iska ko? Shine har zan kira ki tsaya kina wasting min time? Nasan kina nan kina farin ciki zakiyi aure. Let me sound this to you. Getting married to me will be your worst mistake in life dan wallahil azeem sai kin gwammaci mutuwa akan zaman gidana. Mark my words!"
Yana gama fada ya kashe wayar sa ya wurgar a kan gado.
Tun da taji muryarsa ƙirjin ta ya fara bugawa kafafun ta suka kasa daukan ta hakan yasa ta durkushe a wurin tana kokawa da numfashin ta dake barazanar daukewa. Har ya gama magana tana riƙe da wayar ta kasa aikata komai. Wannan wacce irin kaddara ce haka? Zuciyarta zafi take mata gashi ko hawaye ta kasa. Ta ya zata fara rayuwa da wannan mutumin da maganganun sa are nothing but threats? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

Fateedau.

Not edited.

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now