Chapter Seven

11 3 0
                                    

Cikin kiɗima ta shinfidar da ita a kasan dakin dan bazata iya daukar ta ba zuwa kan gado cause ko'ina na jikinta ya sake. Da hanzari ta nufi kofa ta fita zuwa kitchen neman ruwan sanyi inda cikin hukuncin Allah ta samu ba tare da ta wahala ba ta koma dakin daidai lokacin da wasu mata ke neman ina amaryar take. Saurin shigewa dakin tayi ta rufo kofar tare da sanya key ta rufe shi gam gudun kada mutane su fara tunanin wani abu idan sunga halin da Noor din ke ciki.
Da sauri ta isa ta durkusa a gaban ta ganin har lokacin babu alamun numfashi a tare da ita. Ruwan ta bude ta zuba a hannun ta sannan ta shafa a fuskar Noor din amma ko gezau batayi ba. Sake zuba ruwan tayi ta sake shafawa amma still babu wani change. Hankalin tane ya fara tashi inda ta fara kiran sunan ta tana danna ƙirjin ta amma still babu wani improvement.
Zuwa yanzu hankalin ta yayi kololuwar tashi inda babu zato ko tsammani ta fashe da kuka tana girgiza Noor din dake kwance kamar gawa. Ruwan sanyin dai still ta sake dauka sai dai wannan karon ba a hannun ta ta zuba shi ba direct a fuskar Noor din ta zuba kaff dinshi. Aikuwa cikin ikon Allah sai gashi taja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuciya mai tafe da raunataccen kuka.
Rungume ta Hibba tayi itama hawaye na zuba daga nata idanun tama kasa rarrashin Noor din. Tabbas itama ta sani Noor din tana bukatar yin kukan ko dan radadin da zuciyarta ke mata.
Ita kanta tasan an tauye hakkin Noor din dayawa. Amma babu yanda suka iya domin kuwa su ɗin iyayen ta ne.
"Shikenan ni kuma Hibba nasan daga yau rayuwar farin ciki ya kare mun. Zan fara sabon rayuwar da ban taba tsammani ba a inda ban taba mafarki ba, kuma duk ta dalilin hukuncin mahaifi na. Sai dai duk da haka banji haushin shi ba. Kin san meyasa?" Share hawayen da suke zuba masu zafi tayi tana kallon Hibban kafin tayi murmushi tace
"Saboda su ɗin iyaye na ne. Su suka kawoni duniyar kinga suna da iko a kaina mai tarin yawa. Ni kuma as a good girl biyayya shine kadai abinda zan musu."
Ta gama fada wasu hawayen suna gangarowa. Ko bata faɗa ba kallo daya da Hibba ta mata ta gane ba karamin namijin kokari Noor din tayi ba dan alamu sun nuna cewa ta danne radadin da take ji ne tayi wannan furucin nata dan kawai ta kwantar wa da Hibban hankali. Allah sarki Noor mai iya shiga damuwa dan wani yayi farin ciki. Kuma hasashen Hibban yayi daidai dan ganin irin kukan da Hibban keyi ne ya sanya Noor din aro jarumta dan ta rarrashe ta. Lokaci mai tsayi suka dauka suna karfafawa juna zuciya most especially Hibba da take ta kokarin ganin hankalin Noor din ya kwanta.
Knocking din kofar aka sake for the umpteenth time. Bude kofar Hibba tayi. Ashe wasu cousins din Noor dinne suka dawo daga reception wai baiyi dadi ba dan babu amarya a wurin shiyasa suka baro wurin duk da dai ana nan ana cashewa. Bayan nan Ammiey ta shigo dan dama dazu tazo ta samu kofar a rufe sai ta koma. Yanzun ma tazo ganin how her daughter is doing ne. Ita ma dai karfafa mata gwuiwa tayi sannan ta haɗa mata da nasiha mai ratsa zuciya sannan ta koma wurin bakin ta.

_____

Karfe shida na yamma Ammiey ta kawo wani dankareren bridal dinner gown da tayi order daga Switzerland purposely dan dinner da za'ayi bayan isha. Duk wani shiri nasu kuma sun kammala shi dan daga wurin dinner din me kuma za'a wuce da amarya gidan mijinta.
Ita kam amarya tana kwance a bakin gado ta tsunduma kogin tunani. Wai yau itace da igiyar aure a kanta? Marar tane taji ya karta amman sai bata ba hakan muhimmanci ba dan tasan ba period dinta bane. Hasali ma Two weeks ago ta gama period din so ba inda za'ayi ace shine. Tana kwance a wurin har aka kira magrib sannan ta tashi ta dauro alwala ta gabatar da sallar ta. Sauran 'yan matan dake dakin ma kowa tayi bata sannan aka fara shirin dinner. Lokacin da suka kammala shiryawan har anyi isha sai kowa ta gabatar kafin kuma kowa ya dunguma zuwa wajen taron banda Hibba da amarya da taci makeup din da ya kara wa fuskar ta kyau ga kuma dress dinta dark peace da ya kara fito da kyan fatar ta inda ta rike Black shiny purse ƙirar Calvin Klein sai black high heels ma haka wanda ke dauke da siraran igiyoyi a saman shi. Kanta kuwa nannade yake da black silky head sai wani mayafi da aka yafa mata shi stylishly shima baki. Kana ganinta kaga young bride da sai mai rabo ka samu.

_____

Taro ake gabatarwa na manya cike da kasaita inda manyan mutane suka samu halarta. An ci an sha sannan anyi barin kudi. Couple din suna zaune a kujera mai cin mutum biyu inda suka haska wurin sai dai daga amaryar har angon babu alamun fara'a a fuskokin su. Hibba dai na gefen Noor kamar yadda Saif, babban abokin ango ke gefen shi. Lokacin da Mc ya bukaci couple din su shigo fili suyi tasu rawar nan ne kallo ya koma kansu inda kowa ke jiran mikewar su amma ko gezau basu yi ba. Sake kiransu yayi nan ma shiru har saida aminan nasu suka dago su kafin suka fara takawa a hankali zuwa tsakiyar filin. Ko da aka bukaci suyi rawa babu wanda ya motsa a cikin su. Ganin bata lokaci kawai yake a tsaye yada ya zura hannu a aljihu ya ciro bundle din American dollars ya fara barin shi a kanta. Ihu mutanen hall din suka soma hadi da tafi ganin irin barnan kudin da yake. Sai da ya barar da bundle uku sannan suka koma suka zauna.
Bayan nan ne aka bukaci abokin ango da kawar amarya su bada takaitaccen tarihin couple din inda Saif da Hibba suka fito fili cikin harshen Ingilishi kaff suka bayar. Aikuwa sun matuƙar burge mutanen wurin har har hakan ya jawo wasu suka musu likin kudi suma.
An kammala taron daidai lokacin da aka dauka kuma aka rufe da addu'a. Nan dai aka fara daukar mutane ana maidawa gida har ya rage saura masu kai amarya gidan mijinta ne a wurin suna jira a kawo musu motocin ɗaukar amarya amma babu alamun su.
Wata dattijuwa ce wacce ta kasance yayar mahaifiyar Noor din ta tunkari abokan angon da maganar. Kafin su bata amsa Junaid ya karaso ya shaida musu daga shi sai matar shi zasu tafi ba sai anyi rakiya ba. Mamaki ne ya kama wannan dattijuwa har ta kasa boye al'ajabin ta.
"Yaro me kake cewa ne haka? Rakiyar da ta kasance al'ada kake cewa ba sai anyi ba?"
"Eh" ya amsa a takaice.
"Anya kana cikin nutsuwar ka kuwa ɗan nan?"
Bai saurare ta ba ya juya ga friend dinsa yace
"I think we should call it a day."
Kafin Saif yace wani abu har ya juya zuwa cikin hall din maybe to get the bride. Shrugging shoulders kawai Saif yayi dan he's so used to Junaid's behavior. Shima wucewa yayi ya samu sauran abokan ya sanar dasu meke faruwa.
Junaid na shiga hall din bai bi ta kan komai ba ya finciko hannun Noor yayi hanyar waje da ita ba tare da la'akari da mood dinta ba a wannan lokacin. Motar sa ya nufa da ita yana jan ta da karfi ba tare da damuwa da irin takalmin da ta saka a kafafun ta ba.
Kasancewar babu mutane a wajen sai 'yan tsirarun da suka tsaya kai amarya ne kuma su ɗin ma suna ta gaban hall dinne yasa babu wanda ya ganshi dan motar tasa ta baya ya ajiye ta.
Suna kaiwa bakin motar ya bude front sit ya wurgata ciki har hakan ya janyo buguwar kanta a jikin motar. Bai kuma bi ta kanta ba ko bugewar da tayi ya wuce fuu ya bude driver sit ya zauna sannan ya tada motar ya figeta a 180 ya bar harabar har ya kusa take gatekeeper din badan ya matsa ba.
Bayan tafiyar su ne Saif ya koma wajen dangin amaryar ya sanar dasu ango already ya tafi da amaryar shi suyi hakuri a mayar dasu gida. Nan dai kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa inda wasu suke ta mamaki hadi da Allah wadai da rashin kunyar ya'yan zamani.
Gudu kawai yake shararawa hankalin sa gabadaya na kan titin ita kuwa sai zubarda hawaye masu zafi take dan wannan abun da yayi ba karamin tayarda hankalin ta yayi ba. Ta ya zai dauko ta haka kawai ya taho da ita kamar wata mara daraja? Koda shike zata iya danganta kanta da marar darajar duba da irin auren da aka mata sannan ta sani Junaid bazai taba ganin mutuncin ta ba.
Wasu hawayen ne suka sake zubowa wanda sukafi na da dumi hakan yasa ta sanya gefen mayafin ta ta share a hankali amma basu dena fitowa ba kuma babu alamun tsagaitawar su. Babban damuwar ta shine she didn't even say a proper goodbye to her Ammiey dan ita Noor a tunanin ta daga dinner din gida zasu wuce. Yanzu shikenan tayi bankwana da rayuwar ta mai cikeda dimbin farin ciki da soyayyar mutane daban daban kenan? Tayi bankwana da kwanciyar hankali ta dalilin mahaifinta da ta kasa gane dalilin sa na mata wannan auren a kananun shekarun ta? Shin me ke jiran ta a wannan wuri da Junaid zai kaita yanzu? Menene makomar rayuwar ta? Wani irin kalubale zata fuskanta a gidan? Tunani kala kala babu wanda batayi ba. A hankali ta saki kuka mara sauti jin murdawar da marar ta yake sai karuwa yake dan tun a hall din yake mata tana daurewa ne kawai amma yanzu kam ya fara yawa. Dama ita irin mutanen nan ne da idan ciwo na damun su sai suyi ta kuka😭ga kuma inda ta buge kanta sai zugi yake mata.
Wani wawan burki da Junaid din ya ja ne yasa a firgice ta dawo hayyacin ta taga har sun iso.

"OUT!!!"

Ya daka mata tsawa har sai da ta wuntsila. Da sauri ta kama handle din tana kokarin budewa amma ta kasa tsabar karkarwar da hannun ta keyi. Da kyar dai ta samu ta bude aikuwa cikin sauri ta sauka idon shi a kanta. Aikuwa karaf idon shi ya sauka a kan Peach coloured gown dinta.

"What? Blood in my car? WTF!"

_____
Not edited.

Fateedau!

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now