Chapter Six

13 4 0
                                    

Bayan gama wayar ta da Junaid samun kanta tayi a yanayi mai wuyar misaltuwa hakan yasa ta zame tare da kwanciya a wurin ta saki kukan da ya tsaya a makoshin ta. Bazata iya ƙayyade sa'o'i nawa ta kwashe a wurin ba dan baccin wahala ne yayi gaba da ita.

Bangaren Junaid kuwa a matukar hasale yayi wurgi da wayar yana huci kamar zai ci babu. Taya za'ayi ta amince da auren bayan duk barazanar da yayi mata? Amma babu komai. Zai shayar da ita mamaki dan babu wanda ya taba masa kutse a rayuwarsa kamar ita. Zai tabbatar ya azabtar da ita ta inda ko numfashin sa taji sai ta razana. Wannan alkawari ne ya ɗaukar wa kansa.

*****
Ammiey na zaune a dakin mahaifiyar ta tana mata fadan ya zata amince a wa 'yar ta auren dole ba tare da neman shawarar kowa ba. Ita dai Ammiey sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba dan sai yanzu take nadamar rashin sanar da iyayen ta da batayi ba.
"Magana fa nake miki kin sani a gaba kinyi shiru sai sunkuyar da kai kike kamar kina gaban surukin ki." Hajja ta faɗa a zafafe.
"Hajja kiyi hakuri rashin sanar muku da banyi ba nayi tunanin zan iya handling case din ne ni kadai."
"Eh lallai gashi kam kin handling har ma kin win. Wannan irin shashanci har ina? Sai kace wa'yanda suka rasa mafaɗa? Amma sam banji dadin hakan ba kuma duk laifin ki ne. Sai kace baki san zafin haihuwar ba kawai kika amince masa? Zamani fa ya canza an dena auren dole yanzu."
"Hajja option ya bani. Kinsan nace maki har mun kwanta a asibiti. To bayan mun dawo ne na kira shi a waya nake masa magana sai cemin yayi idan na sake magana akan hakan a bakin aure na. Zai sawwake mun sannan ya aura wa 'yar sa wanda yayi niyya. Ni kuma ganin da gaske yake shine kawai sai na amince dan gwara ayi komai a kan idanu na sannan zan rinƙa yi mata addu'a inshaallah.''
Hawayen da suka cika mata ido ne suka samu nasarar gangarowa. A hankali tasa handkerchief ta goge sannan ta mayar cikin jakar ta. Tausayin tane ya kama Hajja dan duk wanda ya ganta zai fahimci damuwar da take ciki. Dan har wata uwar rama ta haɗa. Maimakon faɗa da Hajja ta fara sai ta koma kwantar mata da hankali tana bata wasu shawarwari matsayin ta na mahaifiya har lokaci ya tafi.

Abu kamar wasa sai gashi an fara shirin biki kai kace wani auren soyayya za'a kulla. Ta kowanne bangare shiri akeyi na kece raini.
Ammiey ma ba'a barta a baya ba cewar ta dan za'ayi wa 'yar ta auren dole bashi zai hana ta yin abun da ya dace ba saboda haka ta zage sosai wajen ganin komai ya tafi daidai at the same time kuma tana shirya 'yar ta ciki da waje.
Ita dai bangaren Noor Babu abunda take shiryawa hakama angon. Sai dai tun da aka tsayar da bikin duk bayan kwana biyu sai Hibba tazo gidan kuma zuwan nata ba karamin ɗebe wa Noor kewa yake ba dan dama ta dena zuwa makaranta tunda ko taje dinma ba fahimta take ba sannan dad na tunanin zasu iya hada baki da Ammiey ta tafi wani wurin da sunan ta gudu.
Ta bangaren Junaid kuwa babu abinda ya ragu na kiyayyar da yake wa Noor din sai ma abinda ya karu. Alwashi kala kala kam ya sha su a kanta sannan ya gama tsara duk yanda zai tafiyar da ita duk sanda ta shigo gidan shi ta inda sai ta nemi ya sake ta dan kanta a lokacin kuma babu wanda ya isa ya raba shi da ita dan sai tayi danasanin zuwan ta duniyar ma baki daya!

*****
Kwanci tashi baya hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba. Yau ya kama saura sati daya daurin aure baƙi na nesa wasu har sun iso kowa na jiran lefen da za'a kawo zuwa anjima.
Noor da dama ta kasance ba mai jiki ba ta ƙara ƙanjale wa ta rame sai haske da ta kara sakamakon gyaran da ake mata na amare. Ga texts din Junaid kala kala da yake turo mata masu ban tsoro da sa firgici a kullum wanda ya haddasa mata wani irin tsoro da har hakan yake affecting dinta mentally dan ba sosai take iya bacci ba. Ta wani bangaren kuma ga wani ciwo da ƙirjin ta ya fara mata a duk lokacin da taci karo da daya daga cikin sakonnin shi na kullum. Amma bata taɓa nunawa kowa ba hatta Hibba da ta kasance aminiya a gare ta. Sannan duk irin tambayar da zasu mata akan abin da ke damun ta bata taɓa basu gamsashiyar amsa. Sai dai kawai tace "she's fine" wanda hakan yake tabbatar musu cewar tana da matsala amma taki basu damar sanin takamaiman damuwar nata.

Cikin yardar Allah kuwa karfe hudu na yamma bayan sallar la'asar aka kawo lefe na alfarma inda akwatuna suka kasance guda goma sha biyu kowanne shake da kaya masu matukar tsada. Sannan bakin sun samu tarba ta aminci daga ɓangaren dangin amaryar. Cikin mutunci akayi komai aka watse kowa sai san barka take.

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now