Chapter Eleven

9 2 0
                                    

Da sassafe Junaid ya shirya dan komawa wajen aikin sa kasancewar ranar ta kama Monday. Bayan ya kammala shirye shiryen da zaiyi ya wuce direct kitchen ya hadawa kansa coffee sannan ya dawo dining ya zauna. Mamaki ne ya kamashi ganin an jera abinci a saman table din. Tabbas ya tsorata dan shaf ya manta da wanzuwar wata halitta a cikin gidan, duk a tunanin sa shi kadai ne. Budewa yayi domin yaga menene a ciki sai kawai yaga hadaddiyar sakwarar da tayi jiya.
"Hmmmm" ya faɗa hadi da lumshe ido bayan ƙamshin miyar daya bude ta bugi hancinsa.
"Ga dai abinci yayi kyau amma nasan babu dadi" A fili yayi maganar yana mayar da murfin ya rufe. Bai dauki wani lokaci ba yana shan coffeen ya mike yayi hanyar waje.
Cikin nishadi yake tukin sa dan ya gama kaguwa ya isa wurin aikin shi saboda Princess ta sanar mishi tana can tana jiranshi a office dinshi. Cikin rough driving dinshi ya isa sannan kai tsaye ya wuce top floor inda nan ne office din nashi yake.
Kamshin turaren sa na Maison Francis Kurkdjian Paris ne ya sanar da ita zuwanshi. Da sauri ta taso daga zaunen da take a kan kujerar sa ta tunkaro shi gadan gadan da niyyar rungumar sa. Sanin halin ta ne ya sashi dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.
"Haba sweerie lemme just hug you this once. Kasan fa na dade ban ganka ba." Ta faɗa tana raurau da idanu. Kasancewarta girman kasar turawa yasa wasu abubuwan sam bata dauke su a bakin komai ba kama daga runguma zuwa musabaha da kuma abota da namiji. Ta dauka duk a cikin rayuwa ne sannan iyayen ta ma basu taba sanar da ita rashin dacewar hakan ba. Ga kuma bata zuwa islamiyya dan rabonta da islamiyya tun batafi shekaru goma a duniya ba.

"No Princess kinsan hakan baya cikin tsari na. Komai na da lokacin sa."
"This is what you're always telling me. For God's sake nifa girlfriend dinka ce ba wata ba. Idan ban hugging dinka ba who will I hug?"
"Time. Patience."
Iyaka abinda yace kenan ya wuce ya zauna. Itama zama tayi ganin ya zauna sannan suka fara hirar su na masoya. Allah ya gani tana matukar sonshi ko kadan bata son ganin ɓacin ransa shiyasa ko ya rejecting actions dinta take hakuri duk da a ranta ta i alwashin sai ta canza wannan banzan halayen shin na rashin wayewa a cewar ta. Sosai sukayi hira har lokaci ya ja sannan ya rako ta har bakin motar ta kamar karsu rabu.

_______
Sosai tayi bacci har ta makara dan bata farka ba sai bakwai da mintuna biyu. Cikin sauri ta gabatar da Sallah kasancewar bakon nata ya tafi sannan ta nemi gafarar Allah bisa rashin yin Sallah da wuri. Bayan ta idar ta wuce kitchen ya nemi abinda za taci. Nan ne ta ga Junaid bai ko taba abincin da yasa ta girka masa. Abinda bata sani ba shine Junaid baya cin abinci mai nauyi idan dare yayi. Kawai ya sata aiki ne dan ya wahal da ita. Wayar ta dake gefe ne ya dauki ruri. Da zama ta dauka ganin Hibba ce ke kira sannan suka gaisa inda Hibba ta tambaye ta address din gidan.
"Naje inda akayi jeren kayanki babu kowa a gidan sai mai gadi kuma yace babu kowa a gidan sannan ba'a kawo kowa ba."
"Hibba nidai ban san me mutumin nan yake nufi dani ba. Wani gida ya kawoni daban." Ta fada da alamun kuka a muryar ta.
"Okay yanzu ki bani address din wannan gidan sai nazo."
"Ban san a wacce anguwa muke ba amma idan ya dawo zan tambaye shi. Please kizo kiga inda nake..." Kasa ƙarasa maganar tayi saboda kuka da yaci karfin ta.
Sosai Hibba ta shiga tashin hankali da jin aminiyar ta na kuka. Take itama hawaye ya fara sintiri a fuskar ta. Hakuri ta baiwa kanta sannan ta yiwa kawar ta addu'ar samun sassauci daga wurin mahalicci.
Ita kuwa Noor gaba daya abincin ma kasa ci tayi don zuciyarta zafi take mata ga wani kullutu da ya tsaya a makoshin ta yaki wucewa. Fashewa tayi da kuka sannan ta wuce dakinta da gudu ya faɗa kan gado. Haka ta cigaba da kuka har sai da hawayen ya daina fita sannan ta hakura ta mike zuwa parlour ta fara gyarawa. A hankali take komai har ta kammala sannan ta haura saman shi ta gyara ta fito. Haka ta cigaba da gyara ko'ina hatta harabar gidan dan bata manta abunda ya faɗa ba. Kafin ta karasa ta galabaita ga uwar yunwar da takeji. Zuwa karfe sha daya ta gama sannan ta wuce tayi wanka ta shirya cikin wasu rantsatsun English wears Dan dama tafi jin dadin mu'amala da su. Kitchen ta koma inda ta fara tunanin abunda zata girka amma ta rasa gudun kar Junaid yaki ci kuma yace tayi wani girkin daban. Karshe dai ta fara shirin dafa Lasagna Bolognese (Italian dish ne) ganin ya zauna na tsawon shekaru a Italy tasan bazai ki wannan delicious abinci ba. Kachokam ta maida hankali wurin aikin ta tana yin komai just like the expert she is. Cikin 2 hours ta gama ta jera komai a dining table din sa ta gani a kitchen mai kujeru biyu sannan ta debi nata ta wuce akurkin ta, sabon sunan da ta sawa dakin kenan, sannan ba tare da ta tsaya cin abincin ba ta wuce toilet ta dauro alwala ta gabatar da zuhur prayer sannan taci abincin ta sosai dan har bashin na safe da bataci ba sai da ta biya.
Wuraren uku ya dawo gidan. Tana jin karar motar shi amma tayi biris ta cigaba da zaman ta a sittingroom ɗin dan tana buƙatar address din inda suke. Tana kallo ya shigo ya haura sama baima lura da ita ba. After like twenty minutes ya sauko cikin simple short sleeve da three quarter wando sai kamshi yake zubawa. Still bai kula da ita ba ya wuce kitchen dan ba karamin yunwa yakeji ba. Yana shiga ya bude drawer da yasan garin coffeen na ciki amma sai yaga wayam babu komai. Duddubawa yayi a kitchen din amma bai ga komai ba. Har cikin fridge sai da ya duba nan ma babu. Mamaki ya cika shi dan koda safe da ya haɗa coffee akwai dayawa sannan akwai cakes da sauran snacks amma bai ga ko daya ba. Gashi yunwa na damun shi sosai dan tun coffeen da yasha da safe bai sake cin wani abu ba gashi baya wasa da abinci daman. Juyawa yayi da niyyar fita dan ya sameta ayi duk uwar da za'ayi sannan ta faɗa mishi dalilinta na kwashe stuffs din da ta kwasa. Karaf idon shi ya sauka akan madaidaicin dining table din kitchen din sa kulolin da suke kai. Takawa yayi a sanyaye dan da kyar yake daga ƙafafuwan sa yaje a tsaya gaban table din yana tabe baki hadi da yamutsa fuska ya bude. Ai bai san sanda ya jawo kujera ba ya zauna dan ba kadan ba ƙamshin ya tafi dashi. Gashi kuma best food dinshi ta dafa. Baiyi ƙasa a gwiwa ba ya dishing Lasagna Bolognese din a plate yayi soro dashi dan gani yake kamar zai iya cinye kaff abincin gidan idan ya samu dama. First spoon da yayi was heavenly har bai san sanda ya lumshe ido ba. Kafin ya gama na bakin shi har ya kai second spoon. Kafin kace me har ya kusa half. Sai a sannan ya sarara ya kai duban sa ga jug din dake wurin. Jawo shi yayi ya zuba content din ciki ya kai baki. Tun kan ya kai ga sha yasan zaiyi dadi da ƙamshin flavour yaji mai shegen kamshi ga hucin sanyi da yake dakan fuskarsa. Bai dropping cup dinba sai da ya shanye tass sannan ya numfasa. Sai yanzu yaji ya koma daidai. Cigaba da cin abincin yayi amma bai wani ƙara dayawa ba yaji ya koshi. Tuttula drink din ya sakeyi yasha almost half kafin ya ajiye yana sakin murmushi tare da Siriya gyatsa sannan ya tashi da niyyar barin kitchen din daidai lokacin da Noor da ta gaji da jiranshi har ta gaji ta biyo bayansa kitchen din ta shigo. Isowar ya kenan taga yanda yake kwasar ganima. Tabbas yaji dadi a ranta ganin yaci abincin dan babu macen da zataso ta dafa abinci aki ci. Kunya ce ta kama shi da kuma bakin cikin ganin shi da tayi. Ai sai ta raina shi dan dama yasan ta gama raina shi. Haɗe fuska yayi sannan yayi kicinkicin wai gudun raini. Ita kam Noor ba wannan ne a gaban ta ba. A hankali tace
"Junaid dama address nake so ka bani an tambaye ni ban san address din ba."
Sai da ya kalle ta sannan ya wuce ta ba tareda yace komai ba ya bar kitchen din sannan yace

"Kada na sake ganin mummunar fuskar ki a waje idan ina nan."

Tsaye tayi a wurin batare da sanin me zatayi ba. Wannan wani irin rayuwa ce? Ji tayi gaba-daya ranta ya ɓaci. Sai kace wacce batada gata? Take wani bangare na zuciyarta tace ai gata ya kare tunda aka cusa masa ke yanzu kin koma karkashin sa sai yanda yayi dake. Hawaye ne ya nemi gangarowa amma tayi maza ta mayar dashi dan ta gaji da asarar hawayen ta hakanan.
Kwashe komai da yayi amfani tayi ta wanke na wankewa ta sake gyara kitchen din. Tana cikin gyaran ne kamar daga sama taji ana faɗin:
"No 9  Allen avenue."
Juyowar ta keda wuya taga har ya bar wurin yayi hanyar fita daga gidan.
Allen avenue ta fada a zuciyarta. Ganin biyar na yamma ya kusa yasa kawai tana fita ta dau wayarta ta turawa Hibba address din.

Fateedau♥️

Not edited😱

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now