Chapter Eight

18 2 0
                                    

"What? Blood in my car? WTF!"
Ya faɗa cikin karaji sanda ya maida kallon shi ga sit din da ta tashi a kai. Da ya ga alamun bata ma san me ya fada ba ran shi ya sake ɓaci. Babu bata lokaci ya ɓalle kofar side dinshi ya fito da sauri.
"Bitch gidan uban wa zakije?"
Dakatawa tayi da tafiyar da take jin abun da ya fada. Idan ba gizo kunnuwan ta ke mata ba bitch taji yace. A hankali ta nanata kalmar BITCH da ya kira ta. Bata taɓa zaton zai kira da hakan ba ido da ido duk da kalmar ba sabon abu bane a wurin ta domin duk lokacin da zai tura mata sako wannan kalmar dole ta kasance a ciki. Slowly ta juyo tana kallon shi. Ganin irin kallon da take mishi ne mai nuni da bata san abinda ta aikata ba yasa ya iso inda take babu zato babu tsammani ya sauke mata lafiyayyar mari a fuska wanda har sai da jin ta da ganin ta suka dauke na wuccin gadi. Kafin ta gama dawowa hayyacin ta ya kamo gefen rigar ta ya finciko ta har gaban motar sannan ya sake ta.
"Look over there!"
Ya daka mata tsawa pointing at the direction.
Karaf idon ta ya sauka akan bloodstain din da ya mannu perfectly akan white leather sit din motar. Take zuciyarta ya bada wani sauti na musamman wanda ba don hankalin Junaid baya wurin ba da babu abinda zai hana shi jiyowa. Cigaba yayi da fadin:
"Ko ance miki motar diban prostitutes ne da zaki bata min mota?"
Ita dai bata ce komai ba kawai dai ta sunkuyar da kai ne.
"I don't want to see that when I come." Silently yayi maganar ta yanda duk wanda yaji yasan babu wasa a tattare da shi sannan ya wuce cikin gidan yayi banging din kofar da karfi har sai da ta razana.

Toh jinin menene wannan? Ni dai nasan ba period ɗina bane dan I have almost 5 days left. Toh how comes of all times zai zo yanzu? Ko dai bani da lafiya ne?
Sune tambayoyin da ta jero wa kanta.
Lafiyar ki kalau. Tashin hankali ne ya janyo hakan.
Wani sashi na zuciyarta ya fada. And yes, tashin hankali na janyo hakan sabida she can remember rannan a jirgi za suje Cairo wajen kanin babanta sun hadu da wata wacce ranar ne first day na hawa jirgin ta. Kuma ta daga hankalin ta taki kwantar da shi. Da jirgin zai take off kuwa was a sight to behold cause she did the unexpected. Noor cema ta taimake ta ta rirrike ta. And then later on they realised that she had stained her sit. And she said ba period dinta bane. A doctor sitting close by ne ya musu bayani cewa firgitan da tayi ne ya causing hakan.
A hankali Noor ta zare hannun ta daga kuncin ta da Junaid ya mara dan dama all these while yana kai. She could not even remember when last aka mari Jawad that is far more younger than her ballantana ita. Amma gashi wai yau da ya kasance first day dinta a gidan miji ne ta samu tarba na mari daga mijin nata.
Tunani ta fara na yanda zata wanke mishi wurin. Har bayan minti biyar bata sami mafita ba sai ta yanke shawarar dubawa ko zata samu pampo a harabar gidan. Nan ta tafi tana neman pampo amma bata samu ba. Cikin sanyi ta dawo tana tunanin what to do next. Maybe gogewa kawai zatayi. Amma idan gogewar zatayi dame zata goge? Nan ta fara neman abunda zatayi amfani shima kuma babu. Purse din hannun ta ta bude cikin ikon Allah ta hango handkerchiefs dinta guda biyu masu matukar laushi da tsada. Zaro ɗaya tayi ta koma cikin motar amma me? Jinin ya bushe ta inda sai ta zuba ruwa a jiki kafin ya fita. Babu bata lokaci ta fara neman ruwa a cikin motar dan tasan bazata rasa ba. Bata wani bata lokaci ba ta samo goran ruwa daga gefen kujeran driver. Dauka tayi ta bude sannan ta tittila  kadan a wurin. Cikin ikon Allah kuwa sai gashi ya fita cikin sauki kasancewar leather ne kujeran. Gudun kar cikin motar tayi ƙarni ta dauko turaren ta da dad ya bata mai sanyin kamshi ta shafa a daidai shatin wurin. Take motar ta dau kamshi mai daɗin gaske. Satisfied with the result ta ja dogon numfashi ta sauke.
Wayar ta dake cikin purse din ta dauko tana duba time. Karfe sha biyu saura mintuna hudu ta gani. Tsoron da ya kama ta ne yasa ta nufi entrance din gidan da sauri sai dai tana zuwa taji shi a kulle. Murda handle din ta sake yi nan ma shiru. Kenan Junaid ya kulle ta a waje? Yana nufin ta kwana a waje kenan? Sharrr hawaye suka fara kwaranyowa daga idon ta. Wannan wacce irin rayuwa mahaifinta ya zabar mata? Rayuwar tozarci ko me. Gashi kuma tana tsoron tayi knocking ya zama wani abu daban.
A hankali ta zame ta zauna a verandan dake wurin ta takure dan ba karamin sanyi ake busawa ba. Nan ta zauna tana kuka hadi da tuna mahaifiyar ta da karamin kanin ta da kuma aminiyar ta wato Hibba. Allah sarki ya zasu ji idan suka ga bata nan Junaid ya tafi da ita ba kamar kowacce amarya ba? Tunani kala daban daban ta rinka yi tanayi tana duba time. Gashi bacci barawo yau yaki zuwa ya sace ta. To ma taya za'ayi yazo bayan irin sauron da suka addabe ta da cizo da komai? Ga kuma insects daban daban da suke ta kai kawo a wurin.
Tana zaune har akayi kiran sallar farko a kunnen ta. Gaba daya tausayin kanta yakeji da kanta. Ta rasa meke mata dadi a duniyar baki dayan ta. Tasan shikenan tayi bankwana da farin ciki a rayuwar ta. Kuma har a lokacin hawaye take fitarwa. Tunani kala kala babu wanda batayi ba. Can taji ana kiran sallah a wani masallaci amma babu halin tashi tayi sallah dan babu ruwa a wurin sannan gari bai fara haske ba. Tunawa da tayi da sauran ruwan Junaid dake cikin mota yasa ta mikewa dan ta dauko sai dai ta kasa tafiyar dan kafar ta ta kumbura sosai ga kuma zugi da take mata sakamakon gurdewar da tayi jiya. Da kyar ta lallaba tana dingishi har ta isa motar ta dauko ruwan. Fitsari take so tayi amma bata san inda zataje tayi ba. Can dai ta daure ta nufi wurin flowers ta tsugunna tayi. Nan ne ta tuna da jinin da yazo mata jiya. Normally saura kwana biyar yazo amma yayi sammakon zuwa. Komawa tayi ta jingina da bango ta zauna ta kwantar da kanta. Nan da nan bacci yayi gaba da ita.
Kasancewar bata samu bacci da wuri ba kuwa har gari ya waye bata farka ba hakan yasa koda Junaid ya fito da shirin sa na fita ya ganta tana faman bacci. Ran sa ne ya ɓaci ganin kamar tana enjoying baccin da take duk da a zaune take. Kalle kalle ya soma yi can ya hango hose ai kuwa cikin sauri ya nufi wurin ya bi bayan flowers ya kunna tap din wurin. Dawowa inda take zaunen yayi ya saita mata hose din a take ruwan ya jikata jagab. A firgice ta tashi jin ruwan sanyi a jikin ta kamar daga sama. Sosai ta tsorata ganin shi staye a gaban ta cikin yanayi na rashin walwala. Baya ta soma ja tana kokarin gaishe shi amma ya katse ta da fadin:
"Shut up. Har kin samu bacci wato ga gidan ubanki ko?"
Sunkuyar da kanta tayi sabida bazata iya kallon shi ba tsoro yake bata. Gashi sanyi sai shigar ta yake.
"Get in and clean everywhere sannan ki fito compound dinnan ki make sure everything is in order. Stupid bitch."
Yana gama faɗin hakan yayi gaba. Baiyi taki yakai biyar ba ya juyo smiling evilly yace:
"Welcome to my world Jannaah" sannan ya tafi. Zama Noor tayi a kasan wurin wani kukan bakin ciki na taso mata tun daga kasar zuciyarta. Taya zata rayu a haka? Kallon kafar ta tayi da yayi jaa dalilin kumburin da yayi wanda hakan ya sake haifar mata da wani kukan. Gaba daya kafar zafi take mata gashi Junaid ya sa ta aiki mai wahalar gaske. Duban ta takai bakin kofar shiga sai taga bai rufe ba. Tashi tayi da kyar tana dingisawa har ta shiga ciki.
Tabbas gidan na bukatar gyara don kura ne ta ko'ina. Ta yaya gida zaiyi irin wannan ƙurar? Wani sashe daga zuriyarta ta tambaya. From all indications kuma ba'a taba amfani da gidan ba dan kujerun a lullube suke. Ta ina zata fara?
A hankali ta bude kofar wani daki dake parlon sai taga restroom ne. Shiga ciki tayi luckily kuma akwai heater a ciki. Da sauri ta kunna ta tari ruwan zafi sannan ta zauna ta gasa kafar ta sosai. Tabbas taji daɗin ruwan zafin dan a take kafar ta rage zugin da take.
Mikewa tayi ta mayar sannan tayi wasu uzurinta sannan ta ciro inners dinta ta watsa a washing machine ya wanke haɗe da drying a lokaci daya. Tissue paper da ta gani ta dauko ta sarrafa shi yanda zai taimaka mata kafin daga baya ta dauko kayan shara tabi ko'ina ta share starting from the sitting room sannan ta shiga kitchen. Nan ma yayi kura sosai sai dai bata wani sha wahala ba shima ta kammala. Bayan nan ne ta koma bedrooms din dake parlon suma ta gyara su dan babu datti dayawa a wurin. Bayan ta gama da downstairs ne ta wuce sama ta fara gyarawa. Parlor ne madaidaici sai kofa guda daya da zai leading dinka zuwa four bedrooms din dake upstairs din sai kuma library. Saman bai kai kasan datti ba so in no time ta gama da wurin sannan tabi ko'ina da different varieties of air fresheners da ta samu sannan ta dawo kasa nan ma ta sa room freshener. Tun shigowar ta ta lura da wani glass door dake can far end na parlon amma bata bi ta kanshi ba sai yanzu. A hankali tayi hanyar wurin ta bude. Dining area ne na alfarma da aka ƙawata sosai. Wow ta faɗa a hankali sannan ta shiga. Babu kura a wurin ko kadan probably saboda window din a rufe yake but still sai da ta gyara shi tsaf ta sa room freshener sannan ta fito wanda fitowar nata yayi daidai da fara ganin dishi dishi a idanun ta dalilin yunwar da ya fara kwakular hanjin ta tun tana upstairs. If she can remember rabon ta da abinci tun jiya da rana da Hibba ta forcing dinta. A haka ta daure ta fito harabar gidan ta fara sharewa. Da kyar take sharar dan yunwa ya galabaitar da ita ba kaɗan ba. A ranta kuwa addu'a take Allah yasa Junaid ya taho sa abinci duk da tasan ba lallai ya kawo ba. Ta dauki tsawon lokaci a compound din sannan ta gama cause ganyen flowers sun zube sosai.

Sorry for the late update.
Fateedau.

NOORUL JANNAWhere stories live. Discover now