5

551 42 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*

INA KUKE MAKARANTA??

INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B

INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.

1- *KAUNA CE*
      NA UMM ASGHAR

2- *RUKUQI*
   NA FEEDHOM

3- *WANI SO*
      NA ZEE YABOUR

4- *SO DA ALAKA*
       NA UMMI  AISHA

5- *MUGUN GANI*
    NA SADIYA NASIR DAN

6- *ABDUL_HAMEED*
      NA NANA DISO

7- *MUKULLIN ZUCIYA*
        NA MAMAN KHADY

DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA

(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS

*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*
+447894142004

IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki


5️⃣


*LABARIN MARYAMA...*

Gidanmu babban gida ne dan a k'alla part yakai 30 a ciki, akwai 'ya'ya da jikoki a ciki, duk wanda yayi aure anan ake bashi part ya zauna,
da wuya kaga familyn Bukar Bugaje a waje ba a cikin Estate d'inmu ba,  kakana Bugaje Zanna yana da matan aure uku da 'ya'ya ashirin, matarsa ta farko tana da yara goma wacce itace kakata data haifi mahaifina Bukar Bugaje, mahaifina shine babba a gaba d'ayan gidansu,
sai matarshi ta biyu tana da yara shida saita uku tana da yara hudu kunga su ishirin kenan cif kakana ya haifa, jikoki kam ba'a magana dan bazamu lissafu ba, kuma gaba d'ayan 'ya'yan kaka babu wanda yayi karatun boko saina allo,
mahaifina Allah yayiwa arziki sosai dan babu inda sunanshi bai kai a Nigeria da wasu k'asashen k'etaren ba,
babban d'an kasuwa ne da Allah yasa mishi albarka cikin kasuwancinshi, mahaifina yana da matan aure biyu Mama itace uwar gida sai Umma mumu goma sha uku ya haifa maza sha biyu sai ni mace d'aya,
Mama itace mahaifiyata ainahin sunanta Falmata, mu takwas ne a d'akinmu, Madu shine babba sai Abuwar, Baana, Bakura, Rawaana, Ari, Tujja, sai ni Auta Maryama,
a d'akin Umma, wacce ainahin sunanta Fandi, yaranta biyar, Massa shine babba, sai Zanna, Aduu, sai Aliyu da Adaa.

Mahaifina yadad'e yana san 'ya mace yana kuma addu'ar samunta, amma bai samu ba sai daga k'arshe, Allah ya bashi ni, yayi murna sosai da farin cikin haihuwata ya saka min sunan Kakarshi data rik'eshi ta jiya mishi dad'i sosai Maryama.

Na taso cikin so da k'auna da kulawar 'yan uwana dan san da ake yi min daban yake, kowa ni duk inda na juya ni, kamar ni kad'aice 'ya mace a gaba d'ayar zuri'armu, k'annan mahaifina 19 kowa yana da 'ya'ya mata daga mai biyu sai mai uku har da wad'anda mata kawai suka haifa ba maza, amma a danginmu 'ya'ya maza sunfi yawa.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now