29

395 35 4
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


2️⃣9️⃣


Ruf! Maryama ta rufe idonta dan kar Tangaran ya tsokane mata ido, ashe duk kallan da take yi mishi yana ankare da ita, hannun ya sake yarfa mata har yana gogar hancinta yace..

"Zan dawo kanki bari na gama da babbar shegiyar kafin na dawo kan 'yar tatsitsiya sai kin fad'a min meye abin kallo a jiki na..

Ya murgina kanshi ya kalli Nini yace " a d'aga sama wai anyiwa wada kwace, ai a amshi kad'ai ne ba'aga mutuwa ba, kinci baya wallahi Nini ace wondon dana saka yayi datti na gaji dashi,
na d'auka nakai shara shi kika bi sharar kika d'auko, ina abin tunk'aho da samun saura..?

"Saura nane fa, duk na gama tsutseshi tas, abinda na gama dashi wallahi anci baya ace saurayin 'yar daudu aka kwace dan ci baya wance bata ramin kanta...

Nini ta tafa had'i dayin shewa tace " daga baya kenan sadaka da karuwa, aci a sha, a rage dan gobe, kuma aci yau aci gobe shine ci....

"Ya isa..

Mania ta fad'a cikin izzarta kana ta d'ora da " ki koma da yarinyar nan ki girka ta, ki bata cima me kyau taci tayi b'ulb'ul kafin ranar zab'e tazo, nan da wata tara ..

Nini ta amsa da "to, kana ta juya zata fice Maryama na biye da ita, " ki zab'a mata suna, Mania tayi maganar cikin rashin kulawa,
Nini ta juyo tad'an kalli Maryama kana ta mayar da kallanta ga Mania tace " *K'ARAMAR K'ASA* yayi?

D'an jimm Mania tayi tana nazari kana ta tab'a baki had'i da d'aga kanta alamar yayi...

Bayan Wata tara...

Watanni tara sun shud'e yayinda da Maryama keda  shekaru uku da watanni da barin gida..

Ta canja sosai ta samu kwanciyar hankali sai kewar gida da kewar iyayenta dake damunta, kamar yadda Mania tace a turka ta,
an turkata ta turku, tayi b'ul-b'ul da ita kamar ka tab'a ta jini ya fito, fatarta sai shek'i take tana d'aukar ido, kyanta da k'irar jikinta sun fito sosai,
maza kam sun yo caaa kamar zasu ci babu, harda masu tunk'ahun zasu biya ko nawa ne akanta, amma ina Mania tayi fur ta rufe idonta ta hana kowa koda ganin Maryama ne,
balle wani abu ya gifta, ta tarawa ranar zab'e, dan tasan anan ne zata samu kud'in gaske akan 'yar k'aramar k'asa..

Da farko Maryama bata fuskanci irin hannun data fad'a ba, duk abinnan dasu Tangaran keyi babu abinda ta fahimta, sai daga baya ta gane gidan karuwai da fataucin mata ta fad'a..

Da farko ba k'aramin d'aga hankalinta tayi ba dan gudun kada wani ya keta mata haddi, amma dataga kwata-kwata Mania ta hana a rab'eta saita kwantar da hankalinta,
ta dage da sallolin dare da azkar da addu'a ta tattara komai ta mik'awa Allah, danshi zayyi mata maganin komai..

A gidan Mania Maryama tayi k'awa koma ince aminiya, 'yar Niger itama bak'ar k'addara ta rabota da gida..

"Bintu dan Allah ki fad'a min meya rabo ki da gida please..?

Murmushi wacce aka kira da Bintu tayi ta kalli Maryama tace " waike meyasa kika damu da dole sai kinji labarina..!?

"Nasan akwai k'alubale da abubuwan mamaki a cikin labarinki, kalleki kyakkyawa dake san kowa k'in wanda yasa, doguwa fara, me gashi har gadon baya, va hanci kamar biro, da d'an k'aramin baki d'as da fararen hak'ura, ke kinyi fa...

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now