11

542 37 10
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


1️⃣1️⃣


Tun tana gyangyad'i daga zaunen harta zube saman gadon batare data sani ba, baccin take yi cike da wahala ga yunwa ga gajiya kwata-kwata bata jin dad'in baccin,
irin baccin nanne daya zamewa mutum dole badan yaso ba ya d'auke shi, k'arfe biyu da rabi na dare matsananciyar yunwa ta farkar da ita,
a hankali ta bud'e idonta tana kallan saman P.O.P ta d'an dad'e a hakan bata motsa ba kafin  ta d'an motsa kad'an,
cikin sanyi ta zuro k'afafuwanta k'asa ta mik'e ta isa gaban wardrobe ta d'auko riga marar nauyi wacce iyakacinta gwiwa,
ta cire kayan jikinta dan bak'aramin damunta sukayi ba ga nauyi ne dasu.

Harta nufi haryar kitchen ta tuna da ko sallar magriba batayi ba, kanta ta dafe tana juyawa ta nufi toilet ta d'auko alwala,
harga Allah bazata iyayin sallar bata ci komai ba, dan bak'aramar yunwa take ji ba, idan tace zatayi sallar a halin da take ciki bazatasan abinda take fad'a ba.

Kitchen ta nufa tayi tsaye tana bin ko'ina da kallo cikin ranta tana jin wani abu daban, a fili ta sauke ajiyar zuciya, ta nufi store,
babu abinda babu aciki, " Allah sarki Abba, Ubangiji ya biyaka Allah ya saka maka da mafificin alkhairi,
ta fad'a tana nufar katan d'in indomie, ta bud'e ta d'ebo biyu, ta d'auko albasa da attaruhu da bushashshen kifi ta dawo cikin kitchen ta aje saman durowar kitchen,
ta shiga dudduba ko'ina tana neman inda aka aje tukwane, tayi sa'a taba sha wahala ba ta gansu,
ta d'auki 'yar k'arama ta d'auraye ta kunna gas ta d'ora ta zuba mai kad'an kana ta yanka albasa da attaru ta zuba,
ta bud'e bushashshen kifin ta zuba a roba ta wanke shi sosai kana ta zuba ta tsaida ruwa, tana tsaye harya tafasa ta zuba indomien, bata bar kitchen d'in ba saida indomien ta daho ta zuba a plate kana ta fito falo.

Ajewa tayi ta koma ta bud'e fridge ta d'auko ruwa mai sanyi, ta dawo ta zauna bata ma nufi dinning table ba, ta zauna k'asan carpet tayi wanwar,
tana soma ci ya shigo bakinshi d'auke da sallama, bata amsa sallamar ba, sai d'aga kai da tayi ta kalli makeken agogon bangon dake manne da bangon falon.

K'arfe uku da kwata, batayi mishi magana ba ta cigaba da cin abincinta, ya zauna kusa da ita yana binta da kallo, fuskarta d'aure murtuk babu alamun wasa,
" amarya kinsha k'anshi, ba magana?

"Ba sannu da zuwa kina ganin angonki ya dawo?

Sai lokacin ta kalleshi, kallan da bai wuce na second 2 ba ta kawar da kanta gefe, " ba tayi?

Still batayi magana ba balle ta kalli inda yake, " yunwa nake ji sosai, banza ta kuma yi dashi, a hankali ya zauna kusa da ita yana murmushi while yana k'ok'arin neman su had'a ido,
a shagwab'e yace " please ki bani naci da gaske fa nake jin yunwa, ya k'arasa maganar yana sanya hannu cikin plate d'in, tsam ta tsame hannunta tare da mik'ewa tabarshi nan zaune.

Bata shiga d'akin da aka fara kaita ba, dan alamu sun nuna mata nan ne d'akinshi dan haka ta shiga d'akin da take zaton nanne nata, shiko bayanta yabi da kallo yana murmushi,
bai wani damu da tashin datayi tabarshi anan ba, ya jawo plate d'in gabanshi ya cigaba dacin indomien.

Daya gama bai nufi d'akinta ba, ya shige nashi d'akin ya watsa ruwa, ya zira jallabiya, yayi kwanciyarshi  saman bed, bai dad'e da kwanciya ba aka kira sallar asuba, ya mik'e ya shiga toilet ya d'auro alwala, d'akinta ya biya da niyyar tashinta,
yana shiga ya isketa saman sallaya da alama tunda ta shigo bata kwanta ba, bayyi mata magana ya juya ya fice ya nufi masallaci.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now