8

415 36 1
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''



8️⃣


Hannunshi daya d'aga zai mareta tabi da kallo kana ta mayar da kallanta kanshi, hannun ya sauke tare da juya mata baya ya cusa hannunshi cikin sumar kanshi, duk ya burkice kammaninshi sun sauya idonshi yayi jajir, jijiyoyin kanshi sun fito sunyi rad'o-rad'o, lokaci d'aya taji mugun tsoronshi ya shigeta, " tafi! yace mata batare daya jiyo ya kalleta ba, ba musu tabar wajen a sukwane, d'an d'osanawa tayi ta zauna saman bed,
" mari...!?

"Ni Yaya Yuraam zai mara saboda ball?

"Anya yana cikin hankalinshi kuwa?

Ta dad'e tana tunane-tunane kafin bacci yayi awon gaba da ita.

Duk yadda Yuraam yaso ta bashi dama suyi magana tak'i sai binta yake yana san bata hak'uri amma ina ta k'uduri niyyar saiwa kanta mutunci, tana kwance tana bin karatun Sudais dake tashi a wauyarta taji an turo k'ofa a hankali ya shigo bakinshi d'auke da sallama, in banda amsa sallama ya zame mata dole a addininta da bazata amsa mishi sallamar ba.

"Magana nake san yi dake please, bata ko kalli inda yake ba, taci gaba da abinda takeyi.

Sosai ya marairaice kamar zayyi kuka yace " please ki saurare, dan girman Allah.

Jin ya had'ata da girman Allah yasata kashe karatun, batare data ce mishi komai ba, bata kuma juyo ta kalleshi ba.

Matsowa yayi ya zauna a k'asa kusa da k'afafuwanta ya rik'e k'afafuwan gam while tana kwance bata motsa ba, sosai ya k'ara marairaicewa ya kwantar dakai kamar me neman gafara yace.

"Na sani ban kyauta, na san na b'ata miki Maryama, amma dan girman Allah kiyi hak'uri, nasan ke me hak'uri da yafiya ce, please I'm so sorry.

Ya k'arasa maganar yana rik'e kannuwanshi, bata motsa ba balle ta bashi amma, " kiyi hak'uri ban k'arawa please.

Banza ta kuma yi dashi a karo na biyu, tsaye ya mik'e ya shiga yin up & down yana rik'e da kannuwanshi, while yana fad'in " kiyi hak'uri please kinji?

Cikin nutsuwa ta juyo tayi mishi kallan tsanaki kafin ta fitar da nannuyan numfashi tace" ka bawa ball fahimmancin dabe kamaceta ba,
mahimmancin daka bata yafi na kowa da komai Yuraam, " naji nidai kiyi hak'uri please ban k'arawa i promise.

"Dama ka daina wahalar da kanka ka fice, saboda abu d'aya na sani ni Maryama bazan tab'a yin auren duka ba,
bazan tab'a auren namijin dake yunk'oron dukana tun ina gidan iyayena ba, bazan auri namiji daya fifita shirmen banza akaina ba.

"Idan na sake na aure ka nayi ganganci Yuraam, saboda shi namijin zaman lafiya tun daga soyayya da neman aure ake gane shi, haka idan na aure ka duk abinda ya biyo baya ba k'addara bace ganganci ne.

Zayyi magana mahaifiyar Maryama ta shigo taji duk abinda suka tattauna akai, saurin mik'ewa Maryama tayi tana fad'in " Mama kin gama?

"Me ya faru a tsakaninku?

Mama ta fad'a tana kallansu, dukkaninsu shiru sukayi babu wanda yayi magana, " nace meke faruwa a tsakaninku?

"Bana san rashin zaman lafiya, na lura tun yanzu kuna neman haifar mana da matsala, tunda muke aurarwa bamu tab'a cizon yatsa ba.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now