38

429 46 4
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


3️⃣8️⃣

Tsakiyar birnin London igiyar ruwa tajawota ta b'ullo da ita ta wani babban gidan wasan ruwa, ta dad'e saman ruwa a same ga turawa nan birjik kowa na sabgar gabanshi, babu wanda ya kula da Maryama, kasan halin turawa babu wanda ya damu da rayuwar wani,
bata farka ba sai wajen k'arfe biyu na rana, idanuwanta ta fara bud'ewa taji ruwa ya cika mata ido, tayi saurin mayar da idonta ta rufe,
a hankali ta dafa bakin ruwan da aka gyara aka mayar dashi kamar swimming pool, mamakin ganinta tayi a wajen, ta shiga bin wajen da kallo,
an tsara wajen an gyara shi yadda kasan a aljanna, north sea suka jawo suka shigo dashi wajen dan haka igiyar ruwa ta jawota ta b'ullo da ita nan.

Babu wanda ya kula da ita balle suyi mata magana, jikinta a jik'e sharkaf haka ma gashin kanta a jik'e, ta nufi k'ofar dataga turawa suna bi a zatonta hanyar fita ce,
koda ta b'ulle k'ofar, wata sabuwar duniyar wasan ce, bata shiga ba tayo baya, ta rab'a ta tsaya tana nazartar wajen da mutanen wajen,
babu abinda ta iya fahimta illa iskanci da holewar da akeyi a wajen, ta runtse idanuwanta had'i da cewa " turr, Allah yafe mana.

Cikin harshen turanci ta tambayi wani matashin bature da " please where is the way out?

Kallan sama da k'asa yayi mata daga shi sai gajen wonda ya bata amsa da " ta ina kika shigo?

Don a zatonshi tambayar renin hankali tayi mishi, " please show me way out, ta fad'a tana marairace fuska kamar zatayi kuka, ganin yanayinta ya tambatar mishi da lalle bata san k'ofar ba,
a ranshi ya ayyana wata k'ila a buge take, hannunta ya kama yakaita har bakin k'ofar fita, ya nuna mata had'i da cewa " zaki iya gane gida?

Kanta ta d'aga mishi alamar eh, yayi mata murmushi tare da juyawa yabar wajen, itama ta fita, hanya tabi harta isa babban titi,
tun daga nesa ta soma ganin manyan fastocin Marshall a manyan allunan talla na bakin titi, harda videos nashi, ana tallan yau zai buga babban wasa anan birnin London a Emirates Stadium.

"Wayyo Allah na. tace tana yarfa hannu tamkar wacce take ciwon yatsa, bakinta yak'i rufuwa, ganinshi kad'ai datayi ya mantar da ita gaba d'aya wahala da gwagwarmayar datasha,
tun daga babban d'an yatsanta na k'afa taji wani yana tsarga mata har tsakiyar kanta,
so kenan, cikin k'ank'anin lokaci ta rud'e ta firgice ta fice daga hayyacinta, babu abinda jikinta keyi sai rawa da kerrrma, tama manta da wacece ita, ta manta komai da kowa,
jikinta na tsuma ta tsayar da Taxi tace " please take me to Emirates Stadium.

"Come in, yace had'i da bud'e mata k'ofa ta shiga ta d'osana ta zauna, gani take kamar baya tafiya sosai, ji take tamkar ta fita tayi tsuntsuwa ta isa wajen, tafiyar minti 30 sukayi suka isa wajen,
tun kafin motar ta gama tsayawa ta bud'e ta fito, ta zura a guje, " hey you where is my money, sai a lokacin ta tuna bata da ko sisi,
bata tsaya ba tana cigaba da gudun tace " sorry.

Cikin fushi yace " fuck you bitch.

Data isa bakin k'ofar shiga taga kowa sayya nuna get pass d'inshi (tickets) receipt d'in da sukayi payment d'in shiga, gefe ta koma ta tsaya had'i da runtse idanuwanta tana addu'a, saboda tsabar rud'ewa har cewa takeyiwa Allah dan Allah,

"Allah dan Allah ka taimakeni, kayi min wannan alfarmar, nayi alk'awarin bazan sake rok'onka komai akan Marshall ba, please ya Rabbi! ta fad'a idanuwanta a runtse, taita maimaita addu'ar,
tana tsaye taga wasu gungun mutane sun kai wajen su 20 zasu shiga, tayi wuf ta fad'a cikinsu ta maje yadda kasan tare suke, d'aya daga cikinsu ya mik'awa masu gadin wajen pass d'insu, ya amsa ya duba kana ya basu damar shiga,
tana shiga wajen ta sauke ajiyar zuciya a fili had'i da runtse idanuwanta hawaye na gangarowa saman kuncinta, "Alhamdulillah Alhamdulillah ya Rabbi ta fad'a a zahiri tana bin wajen da kallo,
mutane sunfi millions sun cewa a kintatasu sai tururuwa akeyi, kusan duka mutanen suna sanye da riga me hotanshi da sunanshi.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now