10

494 35 1
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


*ZAFAFA BIYAR....*
*ZAZZAFAR TAFIYA...*

*_KUFAN WUTA_*
_Safiyya Huguma_

*_BAQAR INUWA_*
_Billyn Abdul_

*_RAYUWAR MACE_*
_Hafsat Rano_

*_MASARAUTA_*
_Miss Xoxo_

*_NOOR ALBI_*
_Mamuhgee_

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*

09166221261


🔟


Idanuwanta ta lumshe hawaye na zubo mata wanda ita kanta bazata iya fassara hawayen meye ba, na farin ciki ne kona bak'in ciki,
tayi lamo jikin Umma sai sauke ajiyar zuciya take yi, cikin sanyi Umma ta d'agota tana binta da wani irin kallo da bamu san ma'anarshi ba.

"Maryama lafiyarki kike ta sauke ajiyar zuciya akai-akai kamar wacce taci uban kuka?

Batayi magana ba illa kallan Umman da take yi.

"Anya Maryama kina san auren nan kuwa?

"Kodai da wata matsala a tsakaninku ne?

Umma ta jera mata tamboyin a lokaci d'aya, had'i da dafa kafad'ar Maryama tana fad'in " ki fad'a min gaskiya, karki b'oye min abinda ke ranki dan Allah.

A sanyaye ta d'ago kanta ta kalli Umma tayi raurau da ido kamar zata fashe da kuka tace " ban sani ba nima.

"Babu abinda na sani, nima ban san gaskiyar komai a kaina ba.

Jimm Umma tayi tana binta da kallo can k'asan ranta taji tana tausayawa yarinyar kome yasa oho.

Hawayen dake zubowa saman fuskar Maryama tasa hannu ta share mata tana fad'in " kiyi addu'a Maryama, ki zama me zafin addu'a da k'arfin ibada,
ki rink'a mik'a komai ga mahaliccinki, idan kina addu'a duk abinda kika ji hankali da zuciyarki sunfi  karkarata akai kibi kawai Allah zai kawo maki mafita.

Fad'awa jikin Umma tayi had'i da fashewa da kuka mai cin rai, haka nan taji tana san yin kukan, 
Umma bata hanata kukan ba dan tasan hakan samun sauk'i ne,  ta shiga bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi,

Ya dad'e tsaye yana kallansu hannuwanshi hard'e a k'irjinshi, a hankali ya tako inda suke fuskarshi d'auke da yalwataccen murmushi.

"Alhamdulillah, finally you're Mrs Yuraam Abuwar Bugaje.

"K'ara shigewa jikin Umma tayi tana turo baki, cikin nutsuwa ya zauna kusa da ita, ya sanya hannu yajawo ta daga jikin Umma yana mayar da ita jikinshi yace " kun huta da shagwab'a, da aikin rarrashi yanzu aikin ya dawo kaina.

K'ok'arin zame jikinta ta shigayi, ya sanya hannuwanshi ya mayar da kanta saman k'irjinshi.

"Kwanta jikin mijinki ki samu nutsuwa kinji Baby na.

Duka Umma ta kai mishi tana fad'a " baka da kunya dama Yuraam?

"A gabana..?

"Idan baka fita ba saina sab'a maka.

DUK NISAN DARE....On viuen les histories. Descobreix ara