39

391 31 0
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

3️⃣9️⃣

Kafin awanni 24 da Barrister Shatima ya ambata labarin Maryama ya cika Media kaf, yadda kasan guguwa haka labarin yabi iska ya shiga duniya,
ta kowanne b'angare na duniya maganar da akeyi kenan, har tashoshin CNN, BBC da ALJAZIRA sun haska labarin, sosai labarin ya tab'a zuciyar mutane, aka rink'a fitowa ana yin video ana wallafawa a kafafan sada zumunta,
turawa da 'yan Nigeria suka fara zanga-zangar lumana suna yawo da allunan rubutun JUSTICE FOR MARYAMA, wasu suka rubuta FREE MARYAMA SHE'S INNOCENT,
kafin kace me manyan celebrities na duniya sun fara magana akai...

Maiduguri...

Abba na zaune a falonshi saman sallaya Yuraam ya shigo da wani irin gudu babu ko sallama, duk da yaga Abban na lazumi bai tsaya ba,
ya d'auki remote ya kunna channel d'in BBC k'aton hoton Maryama ne ya bayyana hannunta da k'afarta d'aure da ankwa,
jikin Abba na rawa ya warce remote d'in ya k'ara volume,
da gudu Yuraam ya fita tsakiyar Estate d'in ya tsaya ya d'aga murya yana fad'in kowa ya fito ga labarin Maryama,
jiki na rawa suka rink'a fitowa daga sashensu, duk wanda yazo sayya nuna mishi falon Abba, gaba d'aya gidan aka hallara a falon Abba ana jin labarin Maryama,
har Yuraam ya shigo zai zauna yaga babu Umma, yasan dama ba lalle tazo ba dan duk wannan tsayin shekarun basu shirya da Abba ba, anyi-anyi da ita har an gaji,
tana dai zaune kawai a gidan amma ba wata ma'amula ta auratayya dake shiga tsakaninsu da Abba a tsayin shekaru takwas da Maryama tabar gida,
sake fita yayi ya nufi part d'inta tana zaune a falo tana kallan film d'in Wata Shari'ar a YouTube Channel d'in Al Ajabi Tv, da yayi sallama ko motsi batayi ba,
balle ta d'aga kai ta kalleshi.

"Umma ga labarin Maryama, saurin kallanshi tayi had'i da cewa " a ina?

"Kizo part d'in Abba, duk muna can, d'an jimm tayi tana kallanshi dan tunda abun ya faru bata sake shiga part d'inshi ba har yau,
" idan kayi min k'arya ranka sayya b'aci ka sani ko?

"Waya isa yayi miki k'arya akan abinda ya shafi Maryama Umma?

Ya fad'a cikin girmamawa, dan kowa a gidan shayinta yakeyi yanzu, dan babu ruwanta zata zageka tass, jin abinda yace yasata wuceshi ta barshi nan tsaye,
kanta tsaye ta shiga d'akin tana bin ko'ina da kallo komai ya canja a falon dan ba kayan d'akin data sani bane, shekaru takwas kenan rabanta da part d'in,
ganin hotan Maryama yasata isa gaban TVn tana shafa fuskar Maryama hawaye nabin kuncinta.

"Shekaru takwas kenan raban dana ganki Maryama.

Ta fad'a tana jin wani abu na taso mata.

Tun daga farkon labarin sukaji har k'arshe, tun fitarta daga gida har kawowa ranar data bada labarin, sosai familyn Bugaje suka girgiza dajin labarin Maryama,
da irin wahalhalun data sha, da gwagwarmayar datayi, kaf d'insu babu wanda bai zubar da hawaye ba, harda masu rusa kuka kamar anyi mutuwa,
Abba kanshi sai da yayi hawaye, Umma kam ba'a magana yadda kasan ance mata iyayenta sun mutu.

"Dan girman Allah Alhaji ka nema mana Visan Landon mu tafi, muje muga Maryama, mu tsaya mata, Mama ta fad'a cikin sautin kuka,
ranar kam haka aka yini kamar Abban ne ya mutu, a ranar ya bugawa agent d'insu me yi musu visa waya, ya sanar mishi yayiwa Bugaje's gaba d'aya Visan Landon, ya amsa da " to zan zo na amshi passport d'inku, Abba bayyi magana ba ya kashe wayar.

DUK NISAN DARE....حيث تعيش القصص. اكتشف الآن