6

516 40 2
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*

INA KUKE MAKARANTA??

INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B

INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.

1- *KAUNA CE*
      NA UMM ASGHAR

2- *RUKUQI*
   NA FEEDHOM

3- *WANI SO*
      NA ZEE YABOUR

4- *SO DA ALAKA*
       NA UMMI  AISHA

5- *MUGUN GANI*
    NA SADIYA NASIR DAN

6- *ABDUL_HAMEED*
      NA NANA DISO

7- *MUKULLIN ZUCIYA*
        NA MAMAN KHADY

DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA

(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS

*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*
+447894142004

IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki



6️⃣


Yau muke kammala karatun secondary da kuma saukar Al-Qur'ani abisa k'aidar ahalinmu yau ya kamata a d'auramin aure, dan duk wacce ta kammala secondary school da sauka tare akeyin walimar data bikinta,
kasancewar manemana nada yawa a zuri'armu yasa Abba bayyi hakan ba, dan gudun kada hakan ya haifar da matsala a family,
tunda a ranshi ya riga yayi min miji sai dai idan d'aya daga cikinmu baida ra'ayi ko zai zama cutarwa ga d'ayanmu, anyi walima cikin wadata anci an sha, dan ma yamu yamu ne ba bare, dayake bamu da k'awaye ko abokanai a waje, komai zamuyi mu kad'ai mukeyi, tunda muma bataliya ne.

A gajiye lik'is na shigo main gida ina tafiya ina had'a hanya, ji nayi anyi cali-cali dani an d'aga ni sama, danasan ma bazan iya rigimar ba shiru nayi,
aka kaini har d'aki, a shagwab'e nace " kai Yaya Zanna harda kai?

"Eh mana, auta fa guda, dakyar nace " sai da safe zan rama kansu Yakaka, " tunda zaki rama kan yarana bari najaki a k'asa, " dan Allah ka bari mana, ta fad'a a kasalance, " to kwanta, ya fad'a yana ja mata hargo kana ya fita.

Bata tashi ba sai wajen k'arfe tara na safe, da sauri ta mik'e ta shiga toilet ta d'auro alwala dan yau ko sallar asuba bata fita masallaci ba, dayake suna da babban masallaci da suke yin sallah har sallar juma'a da idi nan sukeyi cikin estate,
a gurguje tayi sallar asuba ta d'ora da walaha, Maryama nada ibada sosai dan azumin litinin da alhamin baya wuce ta, haka sallalolin nafila masu girma,  bakinta kam koyaushe cikin ambaton Allah yake dayin istigfari da azkar,
saida ta karanta izu d'aya da rabi kana ta aje, ta gyara d'akinta tsaf, indai tsafta da gayu ne wajen Maryama ba'a magana,
sai da ta gaida Mama kana ta d'ora da " Mama akwai abinda zanyi miki?

"A'a babu an gama komai, ga abinci can jeki d'iba kici, sai da tad'an yatsina fuska saboda ba wani sosai abinci ya dameta ba, tafi gane abu light marar nauyi, indai ba tuwo ba " me aka dafa?

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now