9

442 36 1
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''


9️⃣


Cikin kuka ta girgiza kanta tana fad'in " ban sani ba Abba, nima ban san hak'ik'anin gaskiyar abinda ke cikin zuciyata ba.

"Bana jin k'iyayyar Yaya Yuraam ko kad'an cikin raina, haka bana jinshi tsaye cikin raina.

Murmushi Abba yayi yana kallanta a tsanake yace " wannan baya nufin kina k'inshi, hakan mafarin gagarumar soyayyar da zata kafa tarihi a duniya ne, zanfi yarda da cewar banbancin ra'ayoyinku ne ya kawo hakan.

Kwatt Yuraam ya had'iye wani abu daya tokare mishi mak'oshi.

Kanta ta sake girgizawa tana fad'in " Abba ni dai...

Dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu yace " ya isa haka Maryama, kinfi kowa sanin bana san gardama,
bazan tauye miki hakk'inki akan aurenki ba, haka bazan tilasta ki ko inyi miki dole ba, kije na baki sati d'aya kiyi shawara, ki nutsu ki yanke hukuncin da zai amfaneki ya kuma yiwa kowa dad'i.

"Kada ki kuskura ki saurari kowa ko kibi shawarar wani, ki tsaida ranki kan zuciya da tunaninki, kiyiwa rayuwa da duniyarki ingantaccen zab'i, wanda zai haskaka hanyarki a gaba, kuma ki tabbatar bayan sati d'ayan kinzo min da mijin aure dan tare zan aurar dake da  'yan uwanki.

Baki Mama ta bud'e da nufin yin magana Abba ya dakatar da ita da fad'in " a'a Falmata ki barta ta yanke zab'i akan rayuwarta, dole tasa Mama yin shiru.

Abba ya kalli Yuraam dake d'osane idonshi kan Maryama yace " kayi hak'uri ba'a matsawa a auratayya saboda kada rabo yayi halinshi.

Cikin k'arfin hali Yuraam ya d'aga kai batare daya iya furta koda kalma d'aya ba.

Abba da kanshi ya rufe taro da addu'a ya sallami kowa, Baakura na gaf da fita Abba ya d'aga murya cikin tsokana yace " kabi a hankali wajen rarrashi kar a fasa maka kai, ayi biki ango a kicciye, kowa ya kwashe da dariya.

Da gudu-gudu tayi saurin shigewa d'akinta, ta mayar k'ofa ta rufe, dan kar Mama ko  Yuraam wani ya biyota ya hana mata tunani, kuma tana buk'atar zuzzurfan nazari saboda Abba magana yayi mata me harshen damo.

Lamo tayi saman bed ta rasa wanne irin tunani zatayi, dan haka ta tattara gaba d'aya lamarin ta mik'ashi ga Ubangijin komai da kowa, ta dage da Istikara gami da addu'ar neman zab'in alkhairi.

Tun daga ranar Mama ta shiga fishi da ita ko magana Maryama tayi mata bata amsawa, dakyar take iya amsa sallamarta ko gaisuwa suma ba koyaushe ba,
sosai hakan ya dame Maryama ta shiga damuwa, harta kai ga bata iya cin abinci, tad'an rame, damma Umma da sauran family's na rarrashinta.

Daga wani b'angaren kuma sosai Yuraam ya sata gaba ya hana mata sukuni dole tasa ta koma zaman d'akinta shima sai ta rufe dan idan bata rufe ba sayya shigo ya dameta da magiya.

Kusan gaba d'ayan Bugaje's sun had'u a falon Umma ana hira wasu nacin abinci yayinda wasu ke kallo, Yuraam ne kad'ai babu, Maryama ta shigo bakinta d'auke da sallama, Mama ta mik'e tana kallan Umma tace " bari naje.!

"Mama danna shigo zaki fita?

"Me nayi ne haka da zafi Mama?

Banza Mama tayi mata bata ko kalli inda Maryama take ba.

DUK NISAN DARE....Where stories live. Discover now