35

422 39 2
                                    

'''DUK NISAN DARE...!'''

*(Unlimited love, Countless love, limitless love, unconditional love, deep love, True love is a strong and lasting affection between spouses or lovers who are in a happy, passionate and fulfilling relationship, It's hard to wait around for something that you know might never happen. But it's even harder to give up when you know it's everything you want.)*

*HAUWA A USMAN*
     ~JIDDARH~

'''Wattpad:- HauwaAUsmanjiddarh'''

3️⃣5️⃣

Murmushi yayi yana kallan d'an k'aramin bakinta dake ta zuba kamar ba dagashi maganar ke fitowa ba.

"Dan Allah fad'a min abinda ya faru dakai.

"Please karki tambayeni labari dan yana da tsayi wata rana inda rabo zakiji, zatayi magana yayi saurin taran numfashinta yace " ya sunanki..?

"Maryama Bukar Bugaje..!

"Ke 'yar Bukar Bugaje ce?

"Eh tace tana d'an gyara zamanta, "Bukar Bugaje fa?

"Eh! Shi dai na Barno, ni 'yarshi ce ta cikinshi, ajiyar zuciya ya sauke had'i da cewa " ikon Allah! to amma meya raboki da gida ya kawoki cikin wannan masifar?

"Karka tambayeni labari na please dan yana da tsayi wata rana idan da rabo zakaji, ta mayar mishi da irin amsar daya bata, dariya yayi sosai kana yace " Hassada, Bak'in ciki, ganin kyashi, munafurci babu abinda zaki tsinta cikin labarina idan ba wad'anan ba.

"Maryama makusanta na sune suka jefa ni cikin wannan bala'in, su suka shirya komai saboda dukiya, su suka rabani da farin cikina, arziki da duk wata ni'ima da Allah yayi min, *MUTUM MUGUN ICCE...* ne Maryama, daga nan ya kwashe labarinshi tass ya fad'a mata,
hmmmm Maryama ta karanta littattafai da bazasu irgu ba masu d'auke da labaran makirci, hassada cin amana, da bak'in butulci ta kalli finafinai amma bata ga ko taji makamancin labarin Mukhtar ba, ko littafin Gadar Zare Na Hauwa A Usman Jiddarh data saurara a YouTube channel d'in Al Ajabi Tv bai kai labarin Mukhatar Taheer ba,
ita wasu abubuwan ma gani take kamar bazasu iya faruwa a gaske ba...

*Duk mai san jin labarin Mukhtar Taheer ya tara a cikin littafin NISAN KWANA... na Bintu Mamman Toga, labarin Mukhtar da Bintu littafi d'aya ne*

Ajiyar zuciya ta sauke a fili had'i da goge hawayenta tace.

" Lalle kaga rayuwa kaima ganin idonka, sannu kaji, murmushi yayi sosai yace " meya raboki da gida Maryama..?

D'an jimmm tayi kana tayi gyaran murya ta kwashe labarinta tun daga farko har k'arshe ta fad'a mishi, kanshi kawai yake iya jinjinawa batare daya iya furta koda kalma d'aya ba,
sai ido daya zuba mata yana kallanta deep down yana jinjina girman wautarta da gangancin da tayi, ya dad'e cikin yanayin kana yace " dogon buri yana mayar da mutum mahako,
ta yadda bazai iya ganin ni'imomin da Allah yayi mishi ba, meyasa bakiyi amfani da hankalin da Allah yayi miki ba?

"Meyasa bakiyi zurfaffan tunani kafin ki yanke hukunci ba?

"An tambayi Manzon Allah (SAW) menene hankali?

"Sai yace " juriya akan bak'in ciki, da yin raha ga mak'iya, da barin mummunan zato, da cire girman kai dan samun farin jinin mutane, da karb'ar uzuri a wurin da ka san ba gaskiya da hak'uri a inda kake da k'arfin ramawa.

"Abu na farko shine juriya akan bak'in ciki, meyasa ke kika kasa jure bak'in cikinki akan farin cikin iyayenki?

"Sosai take kuka wiwi harda majina tace " wallahi nayi nadama, nayi danasani, nayi kuka harna gaji, bana san na mutu ban nemi yafiyarsu ba, ina san na sake ganinsu kodan na durk'usa a gabansu na rok'esu yafiya...

DUK NISAN DARE....Där berättelser lever. Upptäck nu