ƘANWAR MAZA1

2K 90 9
                                    

       ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.

*Ina fatan yadda na fara lafiya, Allah ya sanya na gama lafiya. Ƙirƙirarren labari ne, idan akwai abin da ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne*

Page1

Bismillahirahmanirrahim

Daji Ajiyar Allah! La'asar sakaliya, a lokacin da hasken rana ya fara disashewa, ta doshi yamma za ta faɗi, duhun magariba na ƙoƙarin shigowa ya maye ragowar hasken da ranar ta bari kan ta ƙarasa faɗuwa.
Gamayyar bishiyoyi ne, dogaye da da madaidaita, haɗe da ciyayi da ga mabanbantan tushe, suka haɗu suka yiwa dajin ƙawanya. Zai iya kasancewa abin sha'awa ga wanda ya zo yawon buɗe ido, idan har bai san mai dajin ya ƙunsa ba.
Ga wanda ya san abin da ya ƙunsa kuwa, zai kasance wuri mafi razani, firgici da kuma tashin hankali.
Gudu take yi a tsakanin rayuwa da mutuwa, tana rungume da wani zani a ƙirjinta, babu yadda za ayi daga nesa ka gane me ta rungumo haka take wannan uban gudun.
Ƙafafuwanta babu takalmi, jikinta babu mayafi, duk da yanayin garin babu zafi, amma laɓɓanta sun bushe tamkar dutsen da ya shekara ruwa bai zuba a kansa ba, babu alamar tana gane in da take jefa ƙafarta. Duk da wannan mawuyacin hali da take ciki, ta bawa abin da take rungume da shi muhimmanci sosai da sosai.
Cikin rashin sani, tayi karo da wani abu da ita kanta ba ta kai ga tantance ko meye ba, sai dai ƙarfi da nauyin abun ya sanya ta faɗi ƙasa, take ta saki wani marayan kuka, a lokacin da jini ya fara zuba daga ƙeyarta.
Sai a lokacin abin da take rungume da shi ya tsala kuka, saboda firgitar da ya yi shima.
Jariri ne ɗanyen goyo, cibinsa ko faɗuwa bai yi ba, jikinsa duk busashshen ƙazantar haihuwa da alama yaron ya kwan biyu, amma ko ruwa bai taɓa gani ba balle a wanke wannan ƙazantar!.

**************

Cikin garin Kano, unguwar ɗorayi tinga, misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar Alhamis, wani matsakaicin gida ne, cikin rukunin gidajen dake ɗan ƙaramin layin,  kallo ɗaya zaka yi wa gidajen, ka san na masu ƙaramin ƙarfi ne, duba da yanayin kwatoci da kuma kasancewar gidajen awon igiya, ba magudanan ruwa, babu layuka masu kyau, kowa da in da fuskar gidansa ta kalla, haka zalika kowa in da ya ga dama yake sako kwatar gidansa, wasu da gyara wasu babu, ga gidajen 'yan ƙanana tamkar wani zai hau kan wani.

"Wai ba zaki fito ki je mini aiken ba, har sai gawayin ya ƙare tukuna?" Cewar wata matashiyar dattijuwa, da take zaune a gaban kurfoti, hannunta riƙe da mafici tana firfitawa, gefe ga farantin silba ɗauke da garin tuwon masara a kai.

Wata  yarinya ce ta fito daga wani ɗakin da yake bayan matar, hannunta ɗaya riƙe da hijjabinta, ɗaya kuma sai matsar hawaye take yi.

Matar ta kalleta ta ce "Kukan me  ki ke yi?"

Aikuwa kamar mai jiran ƙiris, cikin sangarta yarinyar ta ce "Ba Huzaifa bane ba ya....

"Ni yi mini shiru, haka dai kuka iya faɗa kamar kuna ganin hanjin junanku, idan na hana ki zuwa in da yake ai ba zaki hanu ba, maza ki ɗau kuɗin nan ki je mini gidan Laure, ta baki kuka ta sittin, daddawa ta arba'in sai manja na naira ɗari ki kawo mini canjin, na yi maza in kaɗa miyar nan kan magariba".

Kwaɓe fuska yarinyar ta yi ta ce "Wai yau ma miyar kuka za ayi Innalillahi wa innalillahi raji'un"

Baki buɗe ta bi Yarinyar da kallo, cikin hasala ta ce "Idan na kaɗa kukar kar ki sha, zaki ɗau kuɗin ki fita ko sai na yi fatali da kanki a wurin?"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now