ƘANWAR MAZA 2

2.8K 31 1
                                    

                   ƘANWAR MAZA

      BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724

P2

Kasa ɗauke idanunta tayi daga kallonsa, saboda azabar firgici da razanar da ta yi.
Ya janyo kujera ya zauna a gabanta, ya ɗan ƙura mata ido, sannan cikin kaushin murya ya ce "Gidan uban wa kika tafi da ta aikeki, tun la'asar ba ki dawo ba sai magariba?" Yayi Maganar yana tsareta da ido.
Kasancewar akwai wutar lantarki, ya sanya fes take kallon fuskarsa da idonsa.

"Ba magana nake yi miki ba, ki ka tsare ni da ido?" Ya daka mata tsawa.

Zabura tayi ta yinƙura za ta yi magana,amma ya sake cewa "Kuma wallahi kika yi mini ƙarya sai na ci ubanki a daren nan"

Jiki na rawa ta fara zayyane masa yadda aka yi tun bayan fitarta.

Huzaifa tun da  yaga Yaya Umar ya shiga ɗakin Mama ya jiyo kukan Rumaisa, ya sha jinin jikinsa, dan ya san yau sai yadda Allah ya yi.
Mama kuwa girgiza kai kawai ta yi, jin Yadda Ruma take faɗar gaskiya saɓanin ɗazu da ta yi mata ƙarya.

Umar ya ce "Namiji ce ke da zaki tafi aron taya?" Ta sunkuyar da kai tayi shiru.

"Kuma me nace miki a kan dambe a hanya, karya ce ke?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

Ya ɗora da cewa "Wato ke duk wani abu da za'a gaya miki sai dai ya shiga ta kunnenki na dama, ya fita ta hagu ko?"

Ita dai tayi shiru tana rarraba ido.

"Kyaci ubanki, tashi ki kama kunnenki tun da ba zaki yi hankali ba".

Maraicewa tayi zata fara yi masa magiya, amma da yayi mata wani mugun kallo, ba shiri ta miƙe ta durƙusa ta hau kamun kunne.

Gaba ɗaya Huzaifa ji yayi bai ji daɗi ba, maimakon a hukuntata tun a lokacin amma sai da aka bari ta fara bacci, za a sakata kamun kunne, ya tsaya ta ƙofa yana leƙen tsakar gidan ya san yanzu zata galabaita, gashi babu wanda ya isa ya hana Yaya Umar abin da yayi niyya sai Hassan ɗin sa wato Abubakar Sadik, shi kuma baya nan.

Umar ya nutsu yana duba litattafansa, Rumaisa kuwa sai tangaɗi take tana neman ta faɗi, amma yayi banza da ita, dan ta san idan ta faɗi ko ta tashi ba zata iya ɗaukar wani hukuncin ba.
Tun tana kuka ƙasa-ƙasa har ta fara yi da ƙarfi, saboda azabar gajiyar da ta yi.
"Tashi" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Ta ɗago duk ta haɗa uban gumi, ga hawaye da majina duk a fuskarta.

"Kukan uban me kike yi?"

Cikin kuka ta ce 'Yaya na gaji ne, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba, na tuba"

"Da alama haryanzu baki yi laushi ba, yi zaman babur tun da kin gaji da kamun kunne"

Babu kalar izayar da Yaya Umar bai yi mata ba a daren, har Sai da Mama ta ji babu daɗi a ranta, amma tuna cewar yarinyar ba 'yar goyo bace ba, ya sanya tayi banza ta cigaba da laziminta.

Aliyu ne ya fito daga ɗakinsu, cikin damuwa ya ce "Dan Allah Yaya kayi haƙuri ka ƙyaleta haka ta je ta kwanta dare yayi, wallahi ta horu, kuma ga gobe in Allah ya kaimu da makaranta".

A fusace Umar ya kalleshi ya ce "Ka ɓace mini daga gabana ko sai na haɗa da kai?" Ran Aliyu ba ƙaramin ɓaci yayi ba, kawai ya girgiza kai ya shiga banɗaki.

Sai da ya tabbatar da ta galabaita sannan ya ce ta zauna ta huta, shi kuma ya tashi ya fita.

Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, saboda jin cinyoyinta take kamar babu nama a cikinsu sai rodi, saboda azabar sagewa da suka yi, ƙashin bayanta ma ban da azabar ciwo babu abin da yake yi mata.

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now