ƘANWAR MAZA 14

908 39 4
                                    

ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.





14

Buɗe baki Abdallah ya yi ya na kallon ruma, bil haƙƙi take maganar har cikin zuciyarta.

"Ke fa hankali bai wadaci ƙaramar ƙwaƙwalwarki ba, sai ki je allo ki zana babar wasu, idan aka zana taki zaki ji daɗi?"

"Ai ni na yi alƙawarin na daina dambe, ta zageni na kasa ramawa, saboda ashar take yi, ni kuma bana zagi, gaba ɗaya ta cuceni ta ɓata mini rai, ni kuwa ba ta san ba a taɓani a ci bulus ba, wallahi sai ta gane kurenta"

Abdallah ya girgiza kai ya ce "No, ki nemi wata hanyar dai, amma ban da iyaye, ba abin wasa bane"

"Iyaye ba abin wasa bane, ta ce mini mara tarbiyya babata tsohuwa, sai na ci buhun ubanta, ranar ma a sanyi ta sameni, da sai na tayar mata da aljanu na yi mata dukan tsiya, to bana som daga shigata makarantar a tsaneni ne, ayi mini mummunar shaida". Duk yadda Abdallah ya so nusar da ruma, ta yi biris ta ƙi fahimta ta yi alwashin ramuwar gayya a kan abin da aka yi mata.

*****
Nasihar da takawa yake yi mata, a hankali ta ji ta ratsata sosai da sosai, daga ita har shi suna fuskantar jarrabawa daban-daban, wanda hakan yake jefa Ammi cikin damuwa.

Nusaiba ta kalli Takawa da Iman ta ce "Iman 'yar gidan yaya, Ammi ta ki yayan ma naki"
Murmushi iman ta yi tana sake gyara zamanta.

Turo ƙofar falon aka yi, suka ɗaga kai gaba ɗayansu suka kalli ƙofar. Jabir ne ya shigo, da sallama a bakinsa. Suka amsa masa gaba ɗaya, hankalinsa ya na kan Iman ya na ƙare mata kallo. Hakan ya sanya ta haɗe rai tana ɗan kawar da kai gefe.

Yayi murmushi ya kalli Adam ya ce "Ni zaka yiwa haka, ka dawo amma sai dai na ji a gari ko ka neme ni"

Takawa yayi murmushin gefen baki ya ce "Ai idan ka san na dawo, zaka dameni ne ka sani yawo a gari, shi ya sa na yi shiru so nake sai na huta, shi ya sanya ma ban zauna a gidana ba, na yo nan"

Nusaiba ta ce "Uncle J, ina wuni?"

"Lafiya lau Nussy, Iman ba magana ne? 'yar rigima"

Ba dan ta so ba ta ce gaishe shi, gaba ɗaya kwanan nan ba ta son abubuwan da Jabir yake mata, wanda ta kasa gane kan su.

Suna tsaka da hirar sai ga sallamar su Fauziyya da Ruƙayya, tare da Samha suka shigo falon.
Gaban Iman ya faɗi da ta ga Samha, musamman wani irin kallo da take bin ta da shi, da Iman ɗin ta kasa gane wane irin kallo ne.
Jabir suka fara gaisarwa, sannan cikin girmamawa suka gaida Takawa. Cikin halinsa na ko in kula da kuma tsare gida ya amsa musu.

Fauziyya ce ta gyara zama ta ce "Yaya ashe ka dawo, bamu san ka dawo ba, sai ɗazu Mummy ta ce mana, ai ka dawo"

"Eh na dawo" ya faɗa a taƙaice.

"Masha Allah, ya ibada?"

Ya amsa da "Alhamdilillah"

"To Allah ya sa an yi karɓaɓiyya".

Samha ta gyara zama, ta na yiwa Adam wani irin shu'umin kallo, ta ɗan murmusa sannan ta ce "Takawa, ni fa kwance jaka na zo yi, daga zuwa wurin su Fauziyy, na ji suna cewa za su shigo yi maka sannu da zuwa, na ce bari na biyo su in yi sannu da zuwa, kuma a bani tawa tsarabar"
A hankali ya ɗago idonsa, ya kalli Samha, ya ɗan yi murmushi tare da girgiza kai amma bai ce komai ba.

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now