ƘANWAR MAZA 7

1.1K 38 8
                                    

                 ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.

P7

Dafe goshi Yasir ya yi yana murzawa a hankali, ruma 'yar bala'i ce, ba zata tashi yi maka hansfree ba a cikin jama'a sai kowa ya hallara kamar mai sanar da wani abu mai muhimmanci, in da ya gode wa Allah da ya kasance, a makaranta ta ji ana koya musu, da bai san da wasu kalaman zai amfani wurin kare kansa ba.
Ita kuwa ta zaƙalƙale tana ta jawabi, babu wanda ya tanka mata, karo da idanun Umar ne ya sanya mata aya a jawaban da take kwarowa babu ƙaƙƙautawa.
"Zo nan" yayi maganar cikin bada umarni.

Kamar mara gaskiya haka ta tashi ta je gabansa ta durƙusa.
"Je ki ɗauko mini jakarki ta makarantar boko da ta islamiyya"

"Dummm ta ji gabanta ya faɗi, har gara jakar islamiyyar ta ma, tun da ba a daɗe da sakata ba litattafan da mutuncinsu, amma ta makarantar boko dai kam sai dai Allah ya kyauta.
Jiki babu ƙwari ta je ta kwaso jakunkunan, ta zo gabansa ta ajiye su.
Ya kalli jakarta ta makarantar boko, duk ta ci ubanta da jagwalgwalon biro, har da zanen 'yan aljanu a jiki da su ABCD a jikin jakar, sunan 'yan gidan nan kuwa babu wanda ba ta rubuta a jiki bs. Tun daga nan ya san cikin jakar ma ba za ayi abin arziki ba.
"Oyaa zazzage litattafan na gani"

Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, litattafan nan sun ga duniya, tamkar ɓera ya ci rage mata. Kaf litattafan babu bango a jikinsu, sun yi kaca-kaca, wasu ma nannaɗe su tayi, wasu ta ninka su biyu, a taƙaice kai ka ce bolar wani office ɗin ce. Sai uban fensura sun kai biyar a cikin jakar, ga su ulu da farar ƙasa da sauran goriba duk a ciki.
Umar ya kalli ruma, ya kalli bolar dake gabansa, dan ba zai ce litattafai ba.
"Yanzu wannan sharar ce litattafan karatun naki?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Ya sanya hannu ya ɗau littafi ɗaya yana dubawa, ba uwar da take yi a ciki, littafi ɗaya sai ta yi duk subject ɗin da ta ga dama a ciki.
A hankali ya cigaba da duba litattafan nata, ga class work da tarin assignment, wasu tayi ta ci zero wasu makin da take ci ma gwanin ban haushi, subject ɗaya ya ga ta mayar da hankali tana yi yadda yakamata, kuma ba ta faɗuwa shine maths.

Yayi ajiyar zuciya ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Ashe asarar kuɗin tara kawai ake a banza ko? A biya miki kuɗin makaranta idan zaki tafi sai an baki abin tafiya makaranta, amma ki je kina wannan jakancin, kalli wai wannan ne litattafan ki na karatu, kalli wannan wai 4\20 ki ka ci, ba zaki iya kawo abin da baki iya ba gida a koya miki, wasa da surutun banza faɗi ba a tambaye ki ba shi ki ka saka a gaba ko?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Ƙarya na yi miki kenan? To bari ki ji na gaya miki, ina nan zan zuba ido a kan result ɗin da zaki kawo wannan karon, wallahi idan bai yi mini ba sai an miki repeating "
Ras! Gaban ruma ya faɗi "Na shiga uku, dan Allah ka yi haƙuri, zan daina surutun in dinga karatu".

"Kar ma ki yi, wallahi primary 1 zan saka a mayar da ke, ki cigaba da daƙiƙanci, kuma ina samun information a kan abin da ki ke a islamiyya, ke kin zama jan wuya zaman ajinku ma ba kya yi, ke kin sakawa kan ki ba zaki iya karatu ba ko? Oya buɗe Alqur'ani nuna mini a surar da ku ke"
Ai nan ma badan-badan tayi ta yi, domin kuwa ba ta san a ina suke ɗin ba.
Carbi ya bata, ya biya mata aya biyu, ya ce tayi ta maimaitawa sai tayi ƙafa dubu.
Da haka yaya umar ya ƙwaci yasir, ta zauna ta dinga nanata karatu har barci ya fara ɗaukar ta, da ta fara bacci yake zuba mata carbi a ƙafa, ta tashi a gigice ta cigaba da karatun, da haka sai da ta haddace rabin shafi, bai ƙyaleta ta kwanta ba sai wurin ƙarfe ɗaya na dare, da kuka haka ta kai karatun nan, ya sa ta kwashe bolar litattafan ta ya sallame ta.

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now