ƘANWAR MAZA 15

889 40 4
                                    

                ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.


P 15

Gaba ɗaya aka juyo ana kallon ruma, mutanen wurin suka hau dariya.
Shi kansa Jamil da yake ango, da sauri ya ƙara rufe fuksarsa da rawani yana murmushi, dan saura ƙiris dariya ta ƙwace masa.
Adam kuwa sake tsare gida yayi, kasancewar dama can ba mai yawan fara'a bane ba, jin muryar ruman yake a wani abu daban, anya mutum ce?. Kamar zai juya domin ganin fuskarta, sai kuma ya fasa ya sake rufe fuskarsa da rawaninsa, yayi gaba.

Ƙawar Hauwwaliya kuwa ɗan zaro ido ta yi ta ce "Ke kin san waye wannan kuwa?"

Ruma ta ce "Ba shine sarki ba?"

"Ba sarki bane ba ai, ɗan gidan marigayi Galadima ne da ya rasu, sunan sarki ne da shi, Takawa ake ce masa, wallahi ki ka bari ya kamo ki, sai kin gayawa mutanen garinku, ba ki san yadda muke jin tsoronsa ko a family ba, hmmm su Ummanmu sun girme shi amma tsoronsa suke ji, ba ya wasa da mutane"

Bayan gama jin jawabin da aka yi mat, ta taɓe baki ta ce "Taɓ, na gama yaya umar, ni gani nake kamar na taɓa ganinsa ma, ko a ina oho mini dai na manta, so nake na ga fuskar sa"

Dariya yarinyar ta yi ta ce "Ki zo wataran mu je gidansa, ko gidansu sai ki ga fuskar sa amma daga baya zan laɓe ke ki shiga" ruma ta kwashe da dariya ta ce "Ke da wasa nake miki, amma dai zan zo wataran a ɗanani a doki"

Yarinyar ta dubi Hauwwaliya ta ce "To yaushe zaku kuma zuwa?"

"Ke, ita fa ruma ba a nan unguwar take ba, zuwa ta yi yau zata koma gida, a ɗorayi take fa"

"Haba, idan mun zo hawan salla wataran, sai na zo gidanku"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo ki, amma baki gaya mini sunanki ba"

"Sunana Jannah, ke kuma ruma ko?" Ruma ta jinjina mata kai alamar eh.

Ta miƙowa ruma ledar viba ta ce "Ga saƙonki" ruma ta karɓi ledar ta yiwa Jannah godiya, suka tafi gida.

Allah ya taimaketa, Abdallah bai dawo ba sai bayan salla magariba, sannan ya ɗauketa suka tafi gida.

Tun a hanya yake tambayarta meye a ledar hannunta, amma tayi mursisi ta rungume ledarta taƙi nuna masa, har suka je gida.

Mama sai da tayi mita "Abdallah ka ɗaukar mini 'ya ka tafi da ita, tun ɗazu nake zuba ido in ga ta ina zaku dawo, ka san da wuri take bacci, kun je kun yi dare".

Abdallah ya ce "Mama wai dama kina son yarinyar nan?"

Mama ta buɗe baki, tare da yin murmushi ta ce "Dan ƙaniyarka in haifi 'yar a cikina ka ce dama ina son ta, ni duk cikinku waye bana so, ai banda hali irin na ruma son da nake yi mata daban ne, kasancewar ta mace ɗaya tilo a cikinku, amma sanin halinta ya sa wasu lokutan nake kamar bana son ta, idan ba haka taɓarar da zata yi sai Allah"

Ruma ta ce "Kai ban taɓa jin kin ce kina sona ba, ashe idan na mutu zaki yi kuka"

Mama ta ce "Ke rabani da shiririta, tashi ki yi sallar isha'i ki zo ki ci Abincin dare ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta".

Ruma ta tashi ta ce "Ai ni yau ba abincinki zan ci ba, na gidan sarauta zan ci" mama ba ta ɗau maganarta da muhimmanci ba, sai da ta idar da salla, ta janyo viva, tana firfito da Abinci.
Mama ta matsata da tambaya, ta bawa mama labarin abin da ya faru.

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now