ƘANWAR MAZA 17

780 39 1
                                    

         ƘANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.


P 17

Shiru ta yi ta kasa cigaba da maganar, ta zuba masa ido ta na jiran ta ji mai zai ce.
Ya tako a hankali ya zo gabanta ya tsuguna, ya na kallon idonta. Cikin sauri ta sunkuyar da kan ta ƙasa, tana jin yadda abincin da ta ci ya tsaya mata a ƙirji, ga wani irin ƙugi da cikinta yake yi mata saboda tsoro.

"Aure ko, shi ki ke so?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Ki je ki dawo daga makarantar, za mu yi magana in dai aure ne baki da matsala, za'a aurar da ke tun da shi ki ke so" da sauri ta ɗago, ta kalleshi za ta yi magana, amma ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce "Shhh, tashi ki wuce ki tafi makaranta"
Kamar wadda aka gayawa mummunan saƙo, jiki babu ƙwari ta bar gidan ta tafi makaranta, sai dai kamar ta faɗi a hanya, dan jefa ƙafarta kawai take yi, maganar mai sunan Baba ta tsaya mata da yawa.

***
Samha ce zaune a kan gado, hannunta riƙe da waya, ɗaya hannun kuma tana wasa da gashin kanta, amma hankalinta ba a kan wayar ba, zancen zuci take yi.
Ƙarar buɗe ɗakin ne ya dawo da ita hayyacinta.
Fauziyya ce ta shigo, ta ajiye jakarta ta zauna a kan gadon, ta dubi Samha ta ce "Ke jiya ki ka shanya ni ina jiranki, amma ki ka ƙi zuwa"
Samha ta ɗan lumshe ido, ta buɗe tare da ajiyar zuciya.

"Ke wai meye haka ne?"

"Ke bari kawai"

"Ban gane in bari ba, kin san ba ma 'yar haka da ke, explain kawai madam"

Samha ta dubi Fauziyya ta ce "Jiya na je mun haɗu da gayen nan fa"

Fauziyya ta waro ido wace ta ce "Ki na da hankali kuwa? Mutumin da baki sani ba ki ka je wurin sa?"

"Eh tare da security na je, sai dai ban bari ya sani ba, kin san waye ma tukuna?"

"A'a, sai kin faɗa"

"Khalifa Usman wakili"

"Meye haɗinki da shi? Ko ya na ciki ne?"

Samha ta yi tsaki ta ce "Ke ba wannan ba, wai yayi bincike a kaina, so yake na taimaka masa ya kai takawa ƙasa, saboda yana barazana ga feature ɗin sa, da mahaifinsa"

Fauziyya ta zaro ido ta ce "Yaya Adam dai?"

"Shi fa"
"To me ki ka ce masa?"

"Fauza, kin san ina son Adam, ba zan goyi bayan a cutar da shi ba, dan haka nace masa ba zan iya ba, kar kuma ya sake nemana"

"To meyasa?"

"Fauza yayanki ne fa, kuma kin san abin da yake zuciyata game da takawa"

Fauziyya ta jinjina kai ta ce "Na san yayana ne, amma ke yanzu haryanzu ki na nan a kan bakanki kina son sa, ana barin halak dan kunya fa"

"Ke ki ka san ta, ita halak ɗin, bari na shiga wanka" ta yi maganar tana miƙewa.

Ɗan shiru Fauziyya ta yi, ta fara zancen zuci 'wannan ai wata damar ce ga Mummy, tabbas Khalifa wakili zai yi wa mummy amfani' da hanzari Fauziyya ta tashi ta fice daga ɗakin.

***
Yau wunin ranar ruma ba a hayyacinta take ba, duk ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Allah ya taimaketa mai sunan Baba bai dawo ba sai dare, tun da ya dawo ta rasa sauran nutsuwarta, tana jiran mai zai ce mata.
Sai da ya gama abin da yake, har ta kwanta ta fara bacci, ta ji ana dukan gefen katifarta.
Gabanta ne ya faɗi da ta yi tozali da shi, ta tashi zaune tana rarraba ido.
Da hannu yayi mata nuni da ta fito ta biyo shi.
Haka ta fito ya na gaba tana baya, zuwa tsakar gida.
Ya ja kujera ya zauna, ita kuma ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai.

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now