ƘANWAR MAZA 13

875 34 0
                                    

                ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.


P13

Kwanci tashi asarar mai rai, ruma ta kammala primary school za ta shiga sakandare, sai murna take yi, sai dai babu abin da ya sauya a halayenta na rashin ji, ta hanasu sakat,a gidan, da an jima sai ta buga tsalle ta ce "Wooo ni zan shiga sakanni in dire"

Yasir ya ce "Ji banza, me aka yi da maza meye wata sakandare, ai yanzu aka fara"

"A'a bar ni na yi tsalle, na samu cigaba a rayuwa ta, Sakandire fa, zan shiga jss1 ai girma ya zo, yanzu ni ma zan yi tsayi tun da zan shiga Sakandire"

Usman ne ya miƙo mata kuɗi ya ce "Yi sauri ki je wurin mai shayi, ki karɓo mini madara zan karya"

Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce "Mama fa ta hana ni zuwa wurin mai shayi, da mai kifi da mai nama"

"Za ki wuce ki je ko sai na zo kan ki?"

Ba dan ta na son aiken ba, ta karɓa ta saka hijjabi ta fita, tama tafe tana shan farar ƙasa, bakinta yayi fari tas, kai ka ce akuya ce ta dumbuji dusa.
Ko da ta isa rumfar, dandzon matasa ne a ciki, sun cika kuma galibi abokan yayyenta ne, ba wanda ta kula a cikinsu ta miƙa kuɗi a bata madara.

"Rumaisa, ina Dambele?" Cewar wani matashi da yake ƙoƙarin kai lomar indomie.
Ta kalleshi ta ce "waye kuma dambele?"

"Ussy mana, na gidanku"

"Sai ka ce mini wani dambele kuma, kamar sunan rago, yana gida ya aka yi?"

"A'a ba komai, kawai na tambayeki ne, kin san Usman dambele wani ɗan ball ne, shi ma haka ake ce masa a filin ball".

"Ni zaka gayawa dambele ɗan ball me, ai sai dai na baka labari"

Kan kace me, aka ɓarke da hirar ball a teburin mai shayi tare da ruma, yadda take bayanin ball ya isa ka gane ƙanwar maza ce, gaba ɗaya ta manta da aike da aka yi mata, ta tsaya ana sharhi da ita.

A ƙalla ta kai mintuna arba'in a wurin, ta manta da aiken gaba ɗaya, ga wurin shayin a ƙofar gidan su yaje, ya ci ace ta je ta dawo, amma babu ruma babu dalilinta.

Ba shiri Usman ya sanya riga, ya fito nemanta, 'yar muryarta kawai yake jiyowa, tana bayani, har da dukan teburin mai shayi tana mayar da yadda aka yi.

"Ke! Meye haka?" Firgigit ta waiwaya, ta ga Usman a tsaye a bayanta.

"Aiken da na yi miki kenan?"

Kame-kame ta tsaya yi, dan har ga Allah ta manta da wani aike, musun ball na ɗibarta a rumfar mai shayi.

"Dambele yanzu nake tambayar ruma kai, ashe kana gidan ma, yarinyar nan ta burgeni, ta san ta kan ball abin mamaki, gaskiya na yarda ƙanwar maza ce"

A ƙule ya ce "Kai dilla ware, wannan ai hauka ne, kawai kun saka yarinya a gaba, kuna wani surutu, meye alaƙarku da ita?"

"Haba Usman, Ruma ai ƙanwarmu ce"

"Ba wani ƙanwarku, baku haɗa alaƙar komai da ita ba, ke kuma wuce kan na saka ƙafata, na kifa ki a wurin" sumi-sumi ta bar rumfar mai shayin ta nufi gida.

Ya bita gidan, ya dinga yi mata masifa, kamar zai cinye ta ɗanya.

*****

"Hutawarki lafiya uwar ɗakina ta kai na, jirgin sama maƙurar tafiya komai nisan ta"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now