ƘANWAR MAZA 16

810 28 5
                                    

                    *ƘANWAR MAZA*

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro

Page 16

Kallon-kallo suka shiga yi wa juna, aka rasa wanda zai bawa wani hanya, Mahmud ne ya fara janye nasa idon ya wuce yana wani irin taku cike da rainin hankali, ya bawa Adam hanya.
Cikin hanzari Adam ya bar falon, yana jin wani abu yana tsikarar zuciyarsa.

Adam na fita, Mummy ta taso ta na faɗin "Mahmud ya haka, meyasa ba zaka tsaya ku gaisa ba, kamar ba ɗan uwanka ba?"

Mahmud ya ce "Mummy, ni baki ga abin da ya yi mini ba? Lokacin da ya sauke girman kai ya duƙa mini, wataƙila na fara saurarasa"

"Haba Mahmud, shi ne fa gaba da kai, ya zaka ce haka? ni fa bana son ace ina ziga ka, kuma ko ba komai ya ci sunan mai martaba, ya cancanci ka girmama shi, kuma idan Allah ya sanya sarautarmu ta dawo gidan nan, ka san shi ne magajin babanku, shi zai zama galadima tun da shi ne babba"

Ya dubi Mummy ya ce "Ni wata sarauta ko wani abu makamancin haka bai dameni ba, a naɗashi sarki ma gaba ɗaya, wannan shi ta shafa, look Mummy, a bar wannan zancen ni bani da lokacinsa, bari na je na karya"  yana gama maganar ya wuceta, ya na bada baya, Mummy ta yi murmushi ta ce "Haryanzu ina wasana yadda nake so, Mahmud dole na ɗarsa maka zaƙin mulki da ƙaunar sarauta, sannan kuma azo a rasa sarautar gaba ɗaya mu je zuwa".

****
Aliyu suna tafe a hanya, yana ta yiwa ruma faɗa.

"Dan ubanki kuɗin makaranta na, na registration na fara tarawa, yanzu kin saka na kwashe na bayar a banza, ban ci ba ban sha ba, dan ma Allah ya sanya DPO ya biya mafi yawa daga kuɗin. Saboda ba ki da mutunci ina kareki ki na ƙaryata ni, ni dama na ƙyaleta ta yi miki shegen duka".

Ta waro ido ta ce "Kaii, idan ta sumar da ni fa?"

"Ai gara ta sumar da ke ɗin, tun da ke dai har abada ba kya hankali, wai ki ka karya 'yar mutane saboda tsabar kanki ba daɗi"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now