page 6 to 10

864 37 0
                                    

💖 *INA ZAN GANSHI?*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

xarahbukar.wordpress.com

               6 - 10

Tafiyar kusan minti goma  tayi kan babban titin Kawo dake cikin garin Kaduna. Hankalinta gabad'aya na bisa titin da babu alamun abun hawa na haya banda mayan motaci dake walk'yawa. Ajiyar zuciyar mai dauke da wahala ta sauk'e, rashin abu hawa a unguwar tasu ba k'aramin ci mata ruwa a k'warya yake ba, ina ma ace tana da motar kanta saidai kawai yan polytechnic su ganta da ride dinta koda ma ace comot make i enter (One door).
    Jakarta irin wace ake sak'alewa a hammata ta bude ta ciro dubu biyu da Baba ya bata na siyan handout, kallon su tayi tana jinjina rashin k'yaun da dattin kud'in dayasha satalif, mai shesu tayi cikin jakar akayi rashin sa'a iska yayi sama dayan canjunan.
    Da azama ta mike tahau tsintarsu, saidai kash, ashirin uku sun haura saman titi, tsabar rud'u bata ankara da SUV dake dannowa aguje ba tahau bin ashirin dinta dake tsilla tsilla a titin.
    Kiiii!!!! Kakeji, yaja mugun burki da ita kanta saida ta razana, jiki na rawa take kalan motar da tunda uwarta ta haihefa bata taba gamo da irin taba, ko inuwar mutum bata hange ciki kansancewar tinted glass dinta, kallan motar kawai take tana imaging kanta aciki. Kallo daya yakai mata ya dauke kai yaja motarsa yabi gefenta ya wuce, RMD data gani cikin plate number yasata wage idanu, tanajin labarin family din a fulanin talla, yau gashi tayi gamo da motar, inama ace taga mai tuka motar yau da tayi kwanan farin cikin haduwa da mai kudi, duban kayan jikinta tayi ta buga tsaki, ta tabbata ya fola mata, ba mamaki kodaddiyar arabian gown dun jikinta ya kwafsa mata, last week kadai ta siyeta a gwanjan kasuwar bacci ganin sabuwar ita yan makaranta ke yayi.
Cike da tausayin kanta ta ida tsince kudin sannan ta nufi k'aramar kasuwar dake gurin, tafi awa daya tana zagaye kasuwar kanan tasamu jakar swagger da ake yayi, cikin dubo biyun ta fidda duba daya ta siyeta, acewarta ta gaji da rike mak'ale mata.
    Bayan ta ida dakyar  tasamu achaba ya karasa da ita inda yan Marwa (keke Napep) ke tsayawa, aranta sai mita take tayi latti zuwa makaranta (sai kace wani ya aiketa kasuwan).
   "Ke tafiya ne" Ogan gurin ke tambayar te, amsa mai tayi da eh, yahau k'walla kiran Mamuda dake zaune can gafe yana gabtar rake.
"Kaida kake layi maiya kaika da zama can" acewar ogan cikin muryar sa nayan tasha.
"gani zuwa" Mamuda ya fadi hade da mik'ewa kyakyabe jikin sa, wata tsohowar yadi mai araha ke sanye jikinsa da wata jar hula bisa kansa, jikinsa dukun dukun da bakin mai tamkar wani mechanic, fari ne dago dasai mai ido ne zai gane akwai farin, kacakaca da yake yasa na kasa tantance kamannisa.
   Tamkar wani shashasha haka yake magana, cikin maganar sa ta e'ena yace "shi shi gaaa muje"
Tsulum Batula ta fad'a cikin marwan, ta k'agara tabar gurin.
Suna tafe tahau gyaran rolling din veil dinta dake nema warwaro, bayan ta gama kudin da suka zube tahau dirgawa dari uku da saba'in tagani, babu naira ashiri cikin, Allah ya isa taja, tana maganganu kasa kasa, yasata asara ya tafi yabarta.
    Duk abunda take yana kallonta ta circle side mirror,  daure fuska yayi tamau had'e da dauke kai ganin ta dauko jar hoda tana shafawa, suna hawa booms hodar ta subuce hannuta, tas kake ji dankarariyar jar hoda ta fashe mai hade da madubi, baima lura ba, lailayo ashar da tayi yasa shi tsayar da Marwan.
"Kan uban can, dan Marwa kamin babban asara"
Kallonta yayi sannan ya kalli inda idon ta yake, yace "ayi hakuri abisa rashin sani ne, banda ke wake shafe shafe a titi"
Harara ta kaima, "dayake titin na ubanka ne, ai dole kace haka, ina ruwanka kaine ke siyamin kayan shafan komi"
"Allah ya wuce zuciyar ki, cikin kudin da zaki biya ki cire murtala uku da goma ki siya sabuwa"
Wani k'askantaciyar kallo ta aika mai, "bura ubar murtala uku da goma, nayi maka kama da talaka mai shafa hodar hamsi, banxa matsiyaci, talaka kun dauka kowa irin kune" tsaki ta buga tana cigaba da banka mai harara.
Kallonta kawai yake yana maimaita abunda tace, shidai baiga banbanci sa da ita ba da take kirasa talaka harda zagin dan tsohonsa dabai san hawa ba balle sauka.
Shareta yayi ya kunna Marwan yaja, tsine tsine tahau yi bai tanka ba.
"Kad poly xaka ajiye ni" yaji ta fadi cike da karaji.
Suna isa ta sauka ta fiddo tsofin goma da ashiri, naira saba'in tabasa, bata jira cewar saba tayi gaba abunta.
Mamaki da tsoron Allah ne ya turnuk'esa, yahau juya saba'in din, akalla daga Kawo zuwa gurin daya ijiyeta Jaka biyar ce, danta raina masa wayo ta basa saba'in tsabar tsiya, mai take nufi kenan, kudin hodar ta cira komi. Kai ya girgiza ya karasa gaba inda yaga passenger.
    B'angaran Batul kuwa dama saba'in tayi niyya basa koda ace hoda bata fashe ba, tana isa hall har angana 8 to 10 lec, ta tsaya jira na 12 to 2. Jikin motar Minal yar ajin su ta jingine jikinta, duk wanda yaxo wucewa saiya tsamma nin motar tace, daga gefen motan taji murya Minal da kawarta Billy suna hira da dariya sam batasan sun kunno kai ba da alamu suma basu lura da ita ba, hirar wata magazine dake rike hannun Minal sukeyi.
"Amma fah RMD dinnan ya burgeni, duba fa kiga CEO ne a Mobile oil Nigeria(MON), one of the major petroleum product marketing companies amma ji yadda yake keeping low profile, ko picx dinsa baa gani, koda yake ance ma hardly 20 letter word ke fita daga bakin sa" acewar Billy
Murmushi Minal ta saki wanda babu tantama ta fola mai dukda sunansa kadai yaya appearing a magazin din, "Ina zan Ganshi, na jima ina neman sa, ni wlh ganinsa kadai ya wadatar ni."
Dan duka billy takai mata tana dariya, "ance komai nasa customised yake da sunansa, kila idan da rabo zakiga motocin sa ko wani abu nasa wataran.
Tsur Batul tayi tana sauraran su, tana tuna motar RMD data gani dazu, dabarace ta fado mata ta saki murmushi, yawaci yaran masu kudi nan basu fiya sanyi kawace da talaka ba saidai iri iri su, balle ma Minal da take daukar kanta diyar shugaba, maganin su kadai zatayi ta hanyar raina masu wayo, tun shigowar ta poly bata samu kawaye ba yawanci yan kuci ku bamu ke manne mata, ita kuwa ta wuce ajin su.
Wayar ta chaina kirar S7 da screen yagama tsagewa ta fiddo ta dasa a kunnuwanta, da ganin wayyar sai ki rantse original dince.
"Hello RMd nayi fushi tun d'azo kace zaka xo"
"Toh ba komai, ka gaishe min dasu mama sai naxo gida gaidata" katse wayan tayi tana kallon su ta gefe ido, sarai sun jita, imani ya hanasu magana banda saki baki da sukayi suna kallon ta.
Taku daya biyu tayi da niyan barin gurin, sukayi azama tarota, Minal tace "Fatima kin san shine ?
A yatseni ta dubeta, aranta tana fadin shegia ashe tasan suna na, a fili tace "wa kenan ?
"Rmd mana, naji kin kira sunansa ne"
"Ayyo wai cousin dina Rmd, kina neman sane ?
Kafin Minal tayi magana Billy ta janye ta gefe,
Tana magana kasa kasa, alamun bata gamsu da Batul ba, kayan jikinta ma ya isa ya nuna class din data fito.
Gyara murya Batul tayi tace "nasan bazaku yadda dani ba, amma kusani ni abun duniya bai dameni ba shiyasa nafison zama simple, dan kun ganni haka dat doesnt mean am poor" k'arashe maganar tayi dakai masu harara sannan tayi gaba.
Da azama Minal tayi saurin taro ta tanai bata hakuri, harga Allah ta gamsu da kalamanta tunda shi kanshi Rmd din ance kudi bai dame saba same goes to his cousin kenan. Dakyar jidda ta hakura bayan billy tasa baki, sai wani ja masu aji Batul take wai ita mai cousin, Minal dai sai kokarin chilling dinta up take, a lecture ma kuna da ita suka zauna bayan an gama suka wuce African dish cin abunci, nan ma sai yatseni take ko dogon surutu tak'iyi karsu k'ureta da tambaya, gabanta sai dauks uku uku yake karsu barta da biyan kudin abinci dan plate dinsu akwai tsada gashi ta cire kunya taci tayi nak, sa'ar ta Minal ta biya duka bill din sannan suka firo tafiya gida, ba yadda basuyi da ita su ijiyeta gida ba taki yadda acewar ta  library xata shiga karatu, sai da taga sunja sun tafi da mintuna talatin sannan ta hau Marwa ta wuce gida murna fal zuciyan ta tasamu b'agas, sai dai tunanin ta daya "Ina Zan Ganshi?"

   Nima xarah nace Ina xan Ganshi, kuma Readers ina zaku ganshi ?

   Ku biyoni muje Neman sa😂😂

INA ZAN GANSHI ?Kde žijí příběhy. Začni objevovat