page 31 to 35

628 29 0
                                    

💖 *INA ZAN GANSHI*💖
            Rubutawa
                  Xarah Bukar

®NWA

xarahbukar.wordpress.com


              31 - 35

Shuru Batul tayi tana sosa gashin k'eyarta cike da kunya, ji take tamkar ta mike ta fad'a rijiyar dake fuskantar ta, kayan jikinta ma ya isa susan karya take ba gidan kitso tazo ba.
Murmushin dabai kai zuci ba Hajjo ta sakar masu sannan tace "yammata mungode da ziyara, saidai bamu dafa komai ba balle mu baku gashi yaune daurin auran kawar taku"
Cike da mamaki su ukun suka zaro idanu suna kallon Hajjo, hardai Batul da firgici ya bayyana fuskarta, atare Minal da Billy sukace "Auran gaske ?
Kallon baku da hankali Hajjo takai masu, ina aka tab'ayin auran karya koda yake sunan Batul na biyu karya dole su watso mata tambayar, bata amsa suba ta juya ta shige daki.
    kallon tir da hali Billy ta watsa mata, "amma dai kinji kunya fatima, haihuwar irinki asara ce, banza, makaryaciya".
Haushi ne ya turnuk'e Batul, cikin borin kunya ta mike suka hau cece kuce, kasa cewa Uffan Minal tayi banda mamakin hali irin na batul da take, sau da dama ana bada labarin masu halinta bata taba yadda ba yau sai gashi ya faru akanta. Dakyar Minal taja Billy suka fice daga gidan, Hajjo dake jinsu bata lek'o ba, saidai asarar haihuwa da Billy ta fadi yay mugun mata ciwo, ita haihuwa k'yautar Allah ce komin ya yaro yake bai kamata ka dangan tashi da asara ko tsiya ba saidai ka bishi da fatan shiriya idan ya kauce hanya, tanaji da Batula har ranta halinta kadai yasa batason tsakan mata fuska.
Saida Batul ta tabbatar sunja mota sanna ta fad'a dakin hajjo, ba tambayar duniya daba tai mata akan gaskiar auren, banxa kadai Hajjo tai da ita tana mai cigaba da hajun gabanta.

Farar yadi wace ake kira da mamar ya sanya da hula buluwa, fuskar sa fayyus daka ganshi kasan baya cikin farin ciki, daure wa kawai yake, nan suka hadu da Baba a bakin massallaci, gaidasa yayi alabadce, Baba ya amsa, ganin yanayin sa baba yace "Mamuda karka damu, idan baka da kudin sadakin nizan biya maka"
Yaken dole ya saki yace "Baba ba matsla, akwai kudin".
"Madalla, Allah yayi ma Albarka"
Amin",ya amsa suka karasa ciki, bayan sun gabatar da Sallah aka dauran auran AbdulRasheed Muhammad Deeni da Fatima Muhammad Yero akan sadaki duba goma kacal.  
Bayan sun fito wani mugun sanyi jikin sa yayi, wani abun mamaki shine yadda Baba bai tambaye sa akasari suna daya bambamta ba, sai mai cema dayayi "Mamuda aure zaman hakuri ne, dan Allah banda niba kayi hakuri da yarinyan nan"
"Insha Allah" kadai ya iya furta mai, Babu wanda yace uffan cikinsu har suka karasa gida, ta bangaran Baba bai kawo komai aransa ba game da sunan, aganinsa Mamuda da ake kiransa dashi lakabine na gidansu.
Tsaye yayi waje Baba ya shigo gidan, turus yayi ganin Batula tsaye bakin kofar dakin hajjo da kodadan kayan jikinta, atunanin sa batayi wanka ba.
"dauko kayanki muje" Baba ya fadi.
Turo baki tayi "babu inda zani.." bata rufe baki ba taji saukar wayan rediyon bayanta, "wuce dan ubanki ki dauko kayanki" Hajjo tace tana shirin kara lafta mata.
Kaman zatayi kuka tace "banyi wanki ba, duk sunyi datti"
"Haka kuwa zaki kwashe su, idan kinje can kya wanke abunki"
K'in motsawa Batul tayi, saida taga Hajjo dagaske take sannan ta ruga daki tana kuka, kayanta dake cikin  tsohuwar ghana must go  ta daukA ta fito, hannu Baba yasa ya karbe suka fice waje Hajjo na mata fatan zaman lafiya.
     Kuka sosai Batul take bata gama girgiza ba saida taga Baba ya jefa ganar cikin Napep ga kuma Mamuda agaba yana shirin ja, harara ta watsa ma cike da tsana, cikin muryar kuka tace "Baba babu mota ne ?
"Kedai shiga muje" baba ya fadi.
Rai bace ta shiga, sannan ya shiga ya zauna kusa da d
Ita.  Kuka take ba k'agauta, ba auran miji ne ke b'ata mata rai ba sai cikin keke da za'a kaita, wato ma mijin matsiyaci ne, uwa uba yadda tayi planing ma kanta big wedding shine Baba da Hajjo suka k'askantar da ita, irin su Dinner, mother's eve, fulani day event dayawa datasa buri sun wuce ta, honeymoon da ake fita waje duk bazata samu ba, Allah ya isa kawai take ma dan iskan daya amshi Sadaqan ta kuma tadau alwashin ko waye sai yayi dana sanin amsarta.

INA ZAN GANSHI ?Where stories live. Discover now