BABI NA D'AYA

642 42 19
                                    

SANADINKI NE!

GODIYA.
Da sunan Allah mai Rahama mai jin 'kai, ina godiya ga Allah da yaba ni ikon ɗaukar alkalami bisa karambani na son isar da sakon da ya daɗe a 'kar'kashin raina. Allah ya bani ikon kamallawa yasa darusan dake ciki ya zama mai amfani ne.

BABI NA 'DAYA.
A firgice na farka daga baccin daya ɗaukeni mai kama da baccin tafiya numfashinta na har abada. Cike da karsashi da rashin nutsuwa na furta,
"Alhamdulillahil lathee ahyana ba'da ma amatana wa-ilaiheen-nushoor ."
Na yi furucin a hankali tamkar mai raɗa jikina ko ina zufa yake. A hankali na karasa buɗe idanunaa cike da tsantseni kamar wadda na warke daga makanta. Wani irin nauyi na ji sunyi man wanda har yanzu ke mani nuni akwai ragowar bacci tare da ni. Ko da wasa ban yi mamakin hakan ba saboda gajiyar da ke tattare da ni kuma da ita na kwanta.
Cikin kunnuwana na soma jin hayaniyar da ta katse mani duk wata gajiyar data haifar mani da wani irin karfin kuzari mai tattare da ruɗani. Har yanzu ina jin kamar faɗa-faɗa da tashin muryar da na tabbatar na majiɓanta lamurana ne. Mikewa na yi a saurance da nufin bin hanyar da hayaniya da maganganun suke fitowa, wanda suka kasance sama-sama cike da ci da zuci. Kunnuwana suka cigaba da saurara tare da haɓaka bugun kirjina.
Cike da rashin nutsuwa na ɗan yi mi'ka tare da kaiwa agogon ɗakin bahagon kallo wanda ke kan gefen drawer (night stand) mamakina ya tsananta ganin karfe biyu da kwata na dare wato ( 2:15 am). Hakan bai hanani gane karfe nawa ba duk da akwai kasantuwar wutar (dim light) wadda ba haske sossai. Jin har yanzu hayaniya bai tsagaita ba kamar faďan (Daddy) da kukan (Mommy) yasa ni saukowa daga kan gadon na kai dubana zuwa ga kannena (twins) 'yan tagwaye sunata baccin su cikin kwanciyan hankali . Mamaki ya kamani jin gidan tsit, kasancewar muna taron bikin yayata wanda kowa yasan gidan biki ba a rabashi da hayaniya komai dare. Cikin hanzari na bude kofata cike da sanda gudun yin kyakkyawan motsin da zai fargar da na kusa da dakina su hankaltu da abinda ke faruwa.

A hankali na ke taka 'kasa kamar mai tambayar tile ďin izini, duk da na yi sallama kafin na shiga zuwa ga fallon amma da alamar ba wanda ya ji ko kuma ya maida hankali da shigar tawa . Mommy ce na fara hangowa fuskarta duk hawaye ga wani na bin wani wajen tururuwar fitowa. Cikin sassarfa na karasa har ina kokarin faduwa sakammakon ganin ta har wani bugu zuciyata ta kara. A hankali na ďauke idona daga kallonta na kai dubana zuwa ga Dady. Wani wawwan birki numfashina ya yi domin hasko wani bahagon tashin hankali daya bayyana 'karara akan fuskarshi. Tun tasowata da ahalina ban taba ganin irin wannan tashin hankalin tare da su ba. Da sauri na kara so inda suke zaune.
"(Mommy! Daddy!)"
Na kirasu da alamun tsoro kuma lokaci ďaya suka ďaga kan su suna kallona. idanun da suka zuba min yasa jikina ya fara kyarma. Ban san lokacin da na kai kujerar da Mommy take zaune ba. Kawai sai na rungumeta, a take ta kara fashewa da sabon kuka ba abinda na ke furtawa sai,
"Innalillahi wa'Inna ilaihi raji'un."
Mommy ce da kuka yau? Na yi maganar a zuciyata kodai kakanmu ne ya rasu? shi din ne kawai ya fado raina kasancewar ba shi da lafiya. Da kyar na iya aro juroya na azawa zuciyata na kokarta tambaya saboda ďacin da na ke ji a makogwarona.
" Mommy me ke faruwa? "
Tambayar da nayi mata yakara sa mata wani sabon kukan. Jin tayi shiru bata ce komai ba sai shasshekar kuka yasa na tattara hankalina zuwa wajen Daddy wanda ye ke jinmu bai ce mana ko ci kanku ba.
"Daddy menene ya ke faruwa ne? Me yasa me ka ne kai da Mommy?"
Na idar da tambayar da muryar kuka ina kara zurfafa tunani na akan menene ummul aba'isin tashin hankalin su? Ko dai Daddy ne ya cewa Mummy zai ma ta kishiya? Na saje tambayar kaina duk da nasan shirme na ke bani da amsar hakan amma na kasa tankwara zuciyata wajan hanata aikata haka. Abin mamaki kuma a take na ji zuciyata ta qaryata ni.
Tabbas wannan abu kuma da mamaki, kasancewar nasan yadda Daddy ke son Mummy kuma, suna nan kullum kaman saurayi da budurwa gaskiya da wuya duk da na san cewa shi mijin mace hudu ne. Kwata kwata mahaifinmu ba shi da sha awar kara aure. Da sauri wata zuciyar ta tunasar da ni alkamin kaddara zai iya sauya komai. Na yi saurin gurgiza kaina yadda na tuna ita kanta mahaifiyarmu kullum cewa ta ke bata yadda da wannan magana ba sai randa dai dayansu ya mutu za'a cire tsamani.
Na dawo daga wasikar jakin da na ke yi shi ma dai bai ce mini komai ba . Hasalima idanu ne ya zuba mini wanda suka rikide suka yi jazur. Kallo ďaya zaka masa kasan yana cikin mummunan tashin hankali. Handset na Mommy da ke gaban center table ya dauka ya mika mini, ban ce masa komai na karbi wayar daga hannun sa sanan na buďe screen na wayar, nasa ma wayar (password) makulin sirri na Mommy, wanda ta sanya sunan yan autan ta wato (twins). Ina budewa gabana ya yi mummunar faduwa sakammakon abinda idanuna suka gani...

Cikin alamun kamar ana bani umarni na cigaba da zagaya idanuna kan abinda su maganan nawa suka nuna min, kwalwata kuma ta karantin amma na kasa gasgatawa bale nasa ran hadace su. Ba komai na gani ba face ina buďewa na yi karo da numbar yayata amma ba bangaran kira ba sai bangaran (whataspp chat). Idona ya sauka kan (Dp) nata ina kare masa kallo sakammakon hoton da ta dora me alamun hotan zuciya wadda ta rabu gida biyu. Na yi saurin janye idanuna saboda ina saurin san sanin dalilin kukan mahaifiyata bayan muna cikin murnar auran yayata wadda a gobe ake shirin daurin aurenta in Allah ya kaimu.
Sai a lokacin ne ma na tuna da yayar tawa , rabona da ita tun dazu domin ta rigamu shiga bacci tun dawowar mu daga "Bridal Eve " mun rabu da ita akan a barta ta yi bacci tana jin ciwon kai har magani Anty Dr. Ta rubuta mata . Saurin kauda wannan tunanin a raina nayi, domin tunuwan da nayi da abunda ke faruwa yanzun. Na tattarar duka hankali na zuwa ga wayar Mommy, sakon da nagani na karshe na fara karantawa domin nasan kila ita ce ke tattare da duka amsoshin tambayoyina . Zuciyan na dukan uku-uku . Na sauke idanuna kan rubutu dake rubuce ina karantawa cike da tararrabi.

Assalamu alaikum warahmuttalah wabarkatuhu, Mommy da Daddy ina neman gafarar ku da duk wanda zan bata wa rai musamman sis ďita, Mommy kuyi hakuri bazan iya bin zabinku ba domin ina da wanda na ke so, kuma yeke sona. Bazan iya auren zabin Daddy ba, bazan iya rayuwa da wanda bana so ba, domin in na yadda na aure Saif zan kuntatawa kaina ne, tunda baya sona nima ba son sa nake ba sannan kuma haďin auren ma daga duka bangarorin biyu akwai son zuciya a ciki ga kuma neman suna da kwadayin abun duniya daga gareka da kai har Uncle.
A da kam da farko naso in danne zuciya ta inyi biyyaya gareka, hiranku da na ji ta sanya duk karfin halin da so in yi in kyautatta maka matsayinka na mahaifi ya gagareni, duk da nayi-nayi in danna zuciya ta in maka biyyaya na kasa Daddy. Wannan ya sa ba yanke shawarar bin abinda zuciya ta ke so da muraďi. Ku tayani da addu'a kusa mini albarka. Kuma ina rokon ku kaďa ku wahala wajen nemana, domin an riga da an daura mini aure a massallacin Yoruba , za ku iya zuwa headquarters domin kain bayani.
Yanzu da na ke tura muku wannan sakon ma ina cikin jirgi domin barin kasar , zuwa ga inda zamu shimfaďa rayuwan mu cikin so da kwanciyan hankali . Balaraben da na kawo lokacin da na dawo daga karatu kuka ki amincewa dai shi ne na aura. Kusa mini albarka Mummy ke uwace kin san yanda nake ji. Ki bawa siblings nawa hakuri bama kaman yar uwata , na leko don na mata sallama na ga tana bacci , nasan yau zan yi missing naku duka."
'Diyarku,
Shukrah.

Tun kan in karasa wata zufa take yankowa daga kowace kofar gashi ta jikina, kaina ya yi wabi mugun nauyi kamar ba tare aka hallita shi da gangar jikina ba. Harshena ya yi nauyi na kasa furta komai sossai zuciyata ke bugu wai abin da nake karantawa a littafi ko na gani a film an gudu SABODA AURAN DOLE wai yau shi ne ya ke faruwa a gidanmu kuma akan yayata? Wani daci naji a makoshina kamar wanda ya fashe na mike da sassarfa kamar wadda akaiwa umarni da gudu na nufi ďakin da Anty Shukran kamar wata mai tabin kai.

Ba in da ban buďe ba daga Bathroom zuwa closet kai hatta karkashin gado na leka babu ita ba alamanta , ina ta dialling no da wayan Mummy da ke hannuna wai switch off. Kan gadon ne , na fadaina fara kuka it can't be true wannan mafarki ne nake yi. Hannuna nasa na dauki Teddy bear da ta ke bala'in so wanda nagani ta bari a kan gadon da kuma bracelet da muka taba sa aka mana an rubuta "Sisters 'forever " na rungumi teddy ďin wani karamin paper ne ya faďo daga jikin " love you my sister, I will surely miss you and promise that i'll never forget forget about you."

Da sauri na fito daga ďakin zuwa inda bar iyayyena na rungumi Mommy wanda har yanzu tana ta kuka ,Daddy ma na nan zaune a inda na bar'shi. Duhu ne ya mamaye idanuna na daina gane komai cikin duniyata.

Dada Sukabe ce!👌🏻

SANADINKI NE ! Donde viven las historias. Descúbrelo ahora