BABI NA BIYAR

103 10 0
                                    

   SANADINKI NE!
©
MARIYA JIKA.

BABI NA BIYAR

Tsit dakin yayi ba abunda ke tashi sai karan AC dake aiki kowa da abunda yeke tunani a ransa. Sunyi kusan minti Goma ba wanda yecewa ɗan'uwansa ko kala. Wayan Uncle Usman ne yai ringing ya katse tunanin da sukeyi "Assalamu Alaikum, lafiya khaleel. ok ka sameni a Nizamiye Hospital din yanzu kuma kazo da Saif ɗin ."

"yanzu haka zamu ce an fatsa auren ?  " cewar  Anty Nana, Ammie ce ta iya amsa mata tambayan " Toh yaya zamu yi , dole mu faɗi ma mutane gaskiya akan an fatsa auren, domin ko da munce an ɗaga ranan dole ne sai an fara neman ƙarin bayani wanda bamu da amsa akanta."

Mummy  ce takara pashewa da sabon kukan da take kokarin danne shi tun ɗazun " Ya Illah Shukran dai taja mini disgraced."
Daddy ne ya fara  magana " ki daina cewa taja mana, tayiwa kanta Allah ne shaidanmu akan irin tarbiyan da muka basu, kuma Insha Allah bazamu tozarta ba"
 

A take naji iyayena sun bani tausayi. Ni menene amfanina ne da bazan share musu hawayen su ba, kawai ayi auren dani yafi , wata zuciyan tace kaɗa ki yadda ki kawo wannan shawaran har kin mance waye Saif mutumin da yafi tsanarki a duk duniya , kila in kika  aureshi kashe ki zai yi.  Tunda nake dashi ko gaisuwa bai taba hadamu ba idan na gaishe shi baya amsawa don haka na hutar da kaina. A take na watsar da tunatarwa da zuciyata ke min bazan juri ganin iyayena kukan iyayena ba gwamma inyi kuka sau dubu akan suyi don haka bansaya wani tunani ba na fara magana " Dady in bazaku damu ba adaura auren dani amadadin Shukran in Ya Saif zai yadda."

Mummy dake zaune bata san lokacin ta tashi tseye ba "What! kinsan me kike cewa kuwa Khairat ?" kowa adakin ni yeke kallo atake naji bugun zuciyana ya sauya , duk da haka banyi kasa a gwiwa ba " Mummy na amince adaura dani I'm ready ina son inyi replacing na  sister na."

" ready for what ? Khairat kin san aure kuwa ko kin dauka kaman cartoon da kike kallo ne na wasan yara, domin nasan ke ba Romantic novels ko movies kike kallo ba balle ince sune ke yawo a kwokwolwanki." Mummyn na magana tana mini wani murmushin da bai kai rantaba. Ido kawai na zubawa Mummy sannan na fara magana domin in nuna musu da gaske nakeyi." Mummy ai ni nace zan auri Ya Saif din ba wanda yasani dole,  in ya amince shikenan adaura amma bazan yadda kuji kunya ba . Kaɗa ki damu ki bimu da addu'a kawai Insha Allah i will try my possible best inga munyi zaman lafiya." hawaye dake makale a idanuna suka gangaro. " Daddy da Uncle kun amince ?." Daddy dai kallon Khairat yeke yi tare da mamakinta shi da yasanta da rawan kai da surutun tsiya shi yasa yeke mata kallon yar Baby ashe ta girma . Wani farin ciki mara misaltuwa ne ya mamaye shi bai san sadda ya rungometa yana sanya mata albarka ba . " Khairat Allah ya miki albarka " Cikin jin daɗi takara shigewa cikin jikin Daddy ɗin . " Khairat Allah yakara miki albarka kai-kai kin share mana hawaye " cewan Anty Nana dake tseye kusa da ita .

" Nifa ban yadda da wannan shawaran ba Khairat, ba ki gani kinyi kankanta gaskiyan Aisha da sa'ke"  cewan Uncle Usman

Ammie dake kallonsu tun dazun batace komai ba,  dama ita tun fil azal tana son ma saif din khairat domin yarinya ce da ba ruwanta da harkan kowace.   Koma tana mata so  tun asali . Anty Nana ce ta tabota "baki ce komai ba Ammie " murmushi tayi "me zance Nana duk abunda kuka zartar ni yayi mini Allah yazaba mana abunda yafi alkhairi." Uncle Usman ya kalli Ammie " nifa ban yanda ba Salamatu kin san halin ɗanki sarai , yarinyan nan tayi kankanta bazata iya juran zama dashi ko kadan ba he will destroy her! ".

Ammie dai kallonsa take yi meyeke son tace , ita har ta isa tasa baki a al'amarin bare kuma abunda ya shafi saif , ko yamanta shi yeke taking decisions ne bata da say akan lamarin yaron ita dai nata addu'a ne ako da yaushe.

"Khairat buɗe kunnuwanki kiji ni da kyau, gwamma muji kunya a idon jama'a akan in aura dake yanzu, kan kanuwa dake kinsan me ake cewa aure ko sha tara baki cika ba da kila zan iya cewa shekarun ki yakai , koni da nake mahaifiyarki banyi aure a shekarunkin nan ba a zamanin da ake rikon amana bare yanzu da yawancin auren zamanin  yazama sai Allah ya  karawa kowa hakuri." Dady dai da yaga matarsa zata iya loosing control,ya mata wani kallo da ita kadai tasan ma'anarsa, sannan tayi shiru.

Uncle Usman ne sukayi signal da Dady alamun su hadu awaje.

****
"Mukhtar ina ga dai tunda haka yafaru gwamma mu hakura kawai, tunda waccan da take babba ta gudu ina karaman zata iya," murmushi yayi yana kallon amininsa " Usman kamanta Aisha ne , bawai bata so kawai ra'ayi ne irin nata na activist ne she's always against early marriage "  kanshi ne  ya girgiza "kada kamanta Mukhtar, Aisha kanwata ce nasan halin ta tun tana karama tunda tariga tafara haka baza ta amince ba" . Kada ka damu Usman  na baka kalmomina Aisha zata amince da batun she's in shock ne , nasan zata sauka kuma zatayi alfahari da auren nan zuwa gaba da yardan Allah .
" Na amince indai ba wata matsala Mukhtar "  cewan Alh Usman . Murmushi sukayi dukkansu biyu sannan suka kara musabaha , cike da farin ciki suka koma zuwa dakin da aka kwantar da khairat.

  Shigan su kenan khaleel ma ya iso tare da Saif. Suka gaida iyayensu sannan Khaleel ya iso gadon da Khairat take '' Little monkey me ya faru?  '' sunan da yasa mata kenan tun tana karama saboda yawan hawe hawen da karambani da tayi tana karama. murmushi tayi ''Hamma khaleel ba  komai'' Saif dake tseye a gefe ko kallo ma bata ishe shi ba balle magana da kyar tasamu tadaga kai ta kai kallonta inda yeke tseye kusa da bakin kofa sannan ta bud'e baki '' ina kwana Hamma saif '' yayi kaman bai ji taba. Nana ce tamasa saif khairat na gaisheka sannan ya amsa da tambayanta ya jikinta.

   Ganin haka jikin iyayen yafara sanyi balle Mummy dake ji da khairat natal. Dady bai yi sanya ba yafara jawabin abunda ake ciki don haka haka saifu shi yasa muka kiraka domin muji idan ka amince da chanjin da za'a maka ka amince zaka auri Suwaiba ? yana kai nan yayi shiru da bakin sa domin yabashi mintuna kadan domin yayi nazari da kwakwal wansa.

Bayan minti goma Saif yayi magana ''ba komai idan har ta amince zata aure ni din''. A ganin sa duk daya ne ko Shukhran ma bai fi sau biyu ya ganta da nufin aure ba kuma duka daga gaisuwa dukkansu basu cewa komai na farkon kama khaleel ne yayi ta surutun tunda dama shan kawar matansa cewa kuma shi yafi sabawa da kowa a dangi da abokanaye fiye da shi ko abokan ma don kullum suna tare ne shi yas abokansu daya.

A hankali na juwe kaina zuwa ga Saif na zuba masa ido shima dai dai lokacin ya kai dubansa gareni wani kallo ne ya watsa min mai cike da kiyayya da kyashi . Ban san lokacin  da na sauka da idona ba. Su Dady ne suka fara mikewa Alhamdulillah. Muje mushirya gashi har karfe goma ta kusa kada muyi letti. Dr ne suka kira yakara dubani yece ba komai, ba abunda ke damuna sannan yabamu sallama duk da yaso rikeni na ko da awa sha biyu ne amma don bayanin da aka masa ya sallameni. Wani irin kallon da bazan iya fassara ba saif ya watsa min kafun su tafi. Jikina a mace muka iso gida Mummy dai bata ce min komai ba. Amma nasan akwai abunda ke cinta Dady dai sai murna yeke yi. Securities ne daga kan estate har gidan mu. 

Dada Sukabe ce!👌🏻

SANADINKI NE ! Where stories live. Discover now