BABI NA BAKWAI

139 11 4
                                    

SANADINKI NE!
©
MARIYA JIKA

BABI NA BAKWAI

Karfe hudu dai-dai yan tawwagar amarya suka  dauku amarya zuwa budan kan amarya da za'a yi a gidan Baban mijinta wanda yazama kaman shine family house na zuriyan Galadima a anguwan Maitama da ke Abuja. Katon gida ne wanda yeke dauke da itatuwa da furanni daban - daban. Tun daga kofan gidan ma kasan naira ta sha kuka anan.

*******

Motar da ke dauke da amarya shine a tsakiya  zaune take a tsakiyan kakanta da yar babanta . Sai wata cousin nata da suke sa'ani ta zauna a gaba. Duk da na'oran sanyaya daki dake cikin motan yana hora iska mai sanyi hade da kamshin air fresher da ke tasowa a motan fun da haka bai hanata yin zufa ba sai . Lullube ta ke da zani super wax sai kuka ta ke tayi tun kakanta na tsokanan ta har ta dinga bata hakuri duk da haka bai sa ta dai na kukan da ta ke yi ba . A hankali motan ta zagaye wani fountain da aka yi a tsakiyan gidan mai alaman roundabout yana fito da ruwa mai kaloli daban- daban na ban sha'awa idan dare yayi  . Sannan motan ya gangaru ya sauko har inda aka sanya kujeru domin yin budan kan Amarya.

A hankali Khairat ta fito daga motan aka sata a tsakiya sannan suka jeru domin zuwa wajen da aka tana da domin budan kai amarya wanda ya kasance daya daga cikin al 'adan fulani idan an kawo amarya za a kaita gaban uwar miji da yan uwan sai ayi budan kai da kudi.

Maroka ma a Lokacin ne suke cin kasuwan su , khairat na fara takowa kuma maroka ne suka fara nasu bambadawan suna ma amarya da zuriyanta kirari mai sanya ya rai da kuma nuna mata ita din wata ce , kuma daga gidan mutunci ta fito. Kalmaomin  da suke rerawa mata da angonta har sun bata dariya a zuciyanta tace duk rashin sanin me ake ciki ne ke damunsu.

  Ana rike da hannunta har zuwa taburman da aka shimfida ma Amarya da kuma zanin da aka a shimfida a matsayin red carpet,  tawagganta na biye da ita. Zamanta ke da wuya yan kanan yara suka taso suka dinga mata spray da nairori a matsayin sannu da zuwa. Sannan aka fara bude taro da addu'a ana gamawa sai kyautan Uwar miji a matsayinta na uwa tana mata sannu da zuwa da turmin Super wax da lace da sallaya da hijabi da kuma naira miliyon daya a matsayin nata tarban kenan, kan kace me dangin baban ango suma sun bada nasu dubbai haka yan uwan maman ango, kawaye da abokan arziki suma sun yita mika nasu kasun, kafin agama budan kai dai har amarya ta tasan ma naira na dukan naira har miliyan biyu da dubu dari shida da hamsin. Sunan da suka rada mata dai nata inkinya suka mai da mata wato" Khairat" . A lokacin ne aka bude kanta wanda ke  a  lullube, an rufe duka jikinta tun ta sauka a mota kamun a shigo da ita cikin gidan. Duk da ita yar gida ce an saba da ita bai sa ana rige -rigen kallonta ba ita ma sai sauka da kai takeyi domin wani irin kunya ta dinga ji. Bayan haka aka ja khairat zuwa gaban mahaifiyar angonta domin a kara yi mata natsiha a matsayin ta na sabuwar mahaifiyarta da kuma a bata amanar sabowar yarta wadda aka dauko ta daga nasu gidan zuwa ga sabon rayuwa wato gidan danta . Dattijai da ke wajen sun yi musu  nasiha da kuma tunatarwa mai kashe jiki . Kamun a gama dai har Maghriba ta kawo kai don haka aka shiga dasu cikin gida domin suci abinci suyi sallah.  Daki na musamman aka sauke su, akwai walima da aka tanadar bayan sallan Isha'i . A wajensu ba sabon abu bane tun kakansu Alhaji Galadima nada rai haka al'adan family din take, baya yadda ayi irin su dinner a biki , shi yasa ana budan kai daren walima ake yi. 

Khairat dai ganin komai banbarakwai take yi gidan da ta saba zuwa tayi har hutu ko week end ma ganinshi take yi kaman bakon wajene ta zo.

******

A hankali Shukrah ta mike domin zuwa bayi tun shigowanta jirgi ta katsa motsin kirki a gajiye ta'ke sosai ga kuma maranta dake cike da pitsari  sosai , amma  kuma ko motsin kirki ta gagara yi saboda tsoron Habib da take ji yanzu ba kadan ba.  Tasan abu daya shine rayuwanta ya riga da ya  chanza.  In ba dai ranan da Allah ya fita da ita daga hanun devil nan ba . Wanda tun haduwan su yabi ya chanza mata rayuwa sosai .  Shima da kansa yazame mata wani mutum ne daban wanda  bata taba sani ba,  kaman wanda basu taba yin wani rayuwa ba. Idonta ta rintse tunawa da tayi da wata rayuwa na daban wanda ko da wasa bata son tunawa . yana daga cikin abinda Habib yayi amfani dashi ya samu rinjaye akanta da kuma cikan burinsa har ta bijirewa iyayyenta. Domin photonan da yeke dashi duk da tayi kokarin  deleting photona  da kuma goge ko wani irin evidence da zai yi linking nata da rayuwanta  na baya ,  duk da hakan bai hana shi dawowa yana mai barazana da rayuwanta ba. Tsoron halin da  iyayyenta da yan uwanta zasu shiga muddin suka  san wace ce ita ? wani irin rayuwa tayi ? Me ta dauko wa kanta a bayan tarbiyan da suka bata yasa ta biye mishi har suka yi aure suna kuma kan hanyan su na zuwa Canada inda dama a shan suka hadu .  Habib dai bazai taba barinta taci gaba da rayuwanta freely ba he's obsessed with her kuma irin obsession mai ban tsoron nan ne.

Dada sukabe ce 👌

SANADINKI NE ! Where stories live. Discover now