SANADINKI NE!
BABI NA UKU
Saifullah Usman Galadima wanda aka fi sani da Saif ko kuma ( S.U.G ) . Mutum ne wanda baya son hayaniya ko kad'an . Tseye yeke yana kallon tagan d'akinsa ba abunda ya tsana kaman kukan tsuntsaye da sharan zakara. Wasu kaji ne da tanta'baru suka addabeshi, Tun tarewansa a gidan sati biyu da suka wuce. Duk da ginin gidan , gini ne na bene kuma dakinsa a sama yeke . kajin nan haka zasu fire zuwa sama don naci da jaraba, bai san kuma me zaiyi musu su tafi ba, kaman suna da masaniya duk d'akin da yaje ya kwana sai sunje ta tagan sun ta damunshi da kukansu , bai ma san daga ina suke zuwa ba , gabaki daya yama rasa yanda zaiyi dasu. Ba ranan da garin Allah zai waye basu zuba shi kuma ba ranan da ba ya koransu amma washegari haka zasu sake dawowa. Abun mamaki kuma ya kasa sabawa da kukan su, wani lokacin har kofa zai bude yaje ya koresu, wani lokacin kuma ya dinga bude window yana rufewa ko zasu gudu, amma ko a jikinsu . Shi da gidanshi sun hanashi baccin tsafiya. Gashi kuma shi mutum ne mai son baccin tsafiya . kaman yayi kuka ba yanda ya iya hakan ya hakura. Yaso yin bacci ko da kad'an ne domin kusan kwanakin nan duka baya iya baccin kirki . Ganin yana 'batawa kansa lokaci gashi har karfe shida tawuca yasa ya shirya zuwa mini Gym . kasancewansa mutum ne mai son motsa jiki . Har wajen motsa jiki ya gyara a gidansa.
******Khaleel ne yashigo cikin gym d'in . “ Ango kasha qamshi gwomma ka kara himma wajen shaping na jikinka kada amarya tafara complaint kasan mata dason maza masu exercise, ” harara ya watsa masa ,“ meya kawoka ba tun jiya na sallameka ba. ” murmushi yayi “ kad'a kadamu mutumina in na kawo ma amaryarka zanyi gaba .” Hannu khaleel ya miqa masa alaman su gaisa “ Assalamu Alaikum. ” kamar wanda bayason amsa sallaman ya mika masa hannu. Murmushi khaleel yayi tunawa da yanda suka rabu da mutumin nasa jiya. Gashi har yanzu yana wani cin magani don kad'a ya tada maganan jiya, dole ne su masa magana ya rage yawan fushi da yawan hada fuska. Saboda in yayi aure matar tasake jiki dashi .
“ Yakamata Saif zuwa yanzu ka girma ka daina yawan fushi. mufa nasiha ne kawai muke maka a matsayin mu na elders wanda muke da aure, kasan abun sai anhada da tips ” Saif dai bai ce masa komai ba sanin halin khaleel da son girma don haka Towel kawai yaja ya fara goge zufan dake saukowa daga jikinsa. Khaleel na binshi har suka isa kitchen , yaso watsa ruwa a jikinsa , amma yunwa yakeji don haka Coffee kawai ya hada ma kansa , ya cewa khaleel , “suit yourself ,” murmushi kawai yayi “madam ta cikamin ciki da masa da kunun gyada , kada kadamu mutumina.”
*****Yana gama shan coffeensa wayansa ya fitar yafara game . khaleel na ganin haka yafara magana “ na dauka wanka zakayi mushirya zuwa main house kasan ana jiranmu ashan , gashi ka hana mutane zuwa gidan nan ban san daga ina ka kawo wa'anan securities ba nima sai da nayi tsiya da su ba kadan kamun inshiga gidan nan yau, wai kabada order kada kowa yashi go ” ganin saif bai ce masa komai ba .
“ Saif wai ni kam bada kai nake magana, tun dazu ina ta ma bayani ko ka d'aga ido kagan ni,” kanshi kawai ya daga batare da yace komai ba ya zubawa d'an uwan nasa 'kyawawan idanunsa da ke rikita mutane dayawa. Hannu ya masa alaman me ka ke cewa ne. “ Kasan Allah bana son rainin hankali kana ganin karfe takwas har tayi. Kuma kana sane daurin auren nan sha d'aya ne . ” Hararan da saif ya zuba masa ne ya bashi dariya “ kaga Malam ni dai taya ka shiri kawai nake yi , kasan assignment aka bani, zanyi kokarin ganin nayi aikina yanda aka bani umarni. ” Kai kawai Saif ya girgiza masa da motsin da yayi da bakinsa . Yasa ya gane meyeke nufi waton cewa shi ba inda zai je . Daga hakan ya maida hankalinsa zuwa wajen game da yeke yi da wayansa . khaleel na ganin haka yasan Saif bai da niyyan shiri. Bai kara ce masa komai ba ya fito daga parlour. Yana tafiya yana tunani mutum d'aya kawai zai iya da Saif kuma tana busy yanzu . Allah ma yasani, shi yana tausayawa matan da Saif zai aura , shi yasa ma bai so wannan auren da za'a ma dan uwan nashi din. Sanin halin abokinshi dan uwanshi, kuma surqinsa tun tasowansu shi wani irin mutum ne da gane halinshi sai a hankali . Haka ya sake koma parlourn babu yanda ya iya dole ne yayi hakuri don rana d'ayan nan ko da lallashi ne in ya kama yayi zai yi in dai bukatan iyayensu zai biya Zai yi don ya samu kan Saif din. In ba haka ba Nana zata iya fushi dashi tunda ta bashi wannan aikin .
********Ko da khaleel ya dawo bangaren Saif bai tarar dashi a parlor ba. don haka ya haura zuwa sama , yayi sallama yaji shiru , sai ya bud'e dakin Saif ya duba dakin , shima bai tarar dashi ba har zai juya ya fita yaji kaman motsin ruwa a bayi murmushi yayi yasan Saif na wankane. Don haka ya sauko zuwa a dai_dai lokacin kuma wayansa yayi ringing. Abba ne ke kiransa.
Saif dai ba abunda yeke yi a toilet sai tsaki , Allah ma ya tsani shi baya yadda da kowa more especially mata. Yasha yadda da mutane amma a karshe cutar dashi suke yi . Shi yasanya baya son soyyaya a rayuwansa domin ba abinda ke cikinta sai wahala da yaudara. Ba yanda ya iya ya zama dole yayi biyyaya wannan karon, ya auri zabin Iyayensa ba don yaso yin haka ba.
Dada Sukabe ce!👌🏻
![](https://img.wattpad.com/cover/137300709-288-k295629.jpg)
ESTÁS LEYENDO
SANADINKI NE !
RomanceTun kan in karasa karanta wasikan wata zufa take yankowa daga kowace kofar gashi na jikina. Da guduwa na shigo dakin Anty shukran ko sallama babu. Ba in da ban buďe ba daga Bathroom zuwa closet kai hatta karkashin gado na leka babu ita ba alamanta...