BABI NA TAKWAS

89 10 9
                                    

SANADINKI NE!
©
MARIYA JIKA

BABI NA TAKWAS
 

Khairat

Na bude idona naga duhu. A take numfashina yafara tafiya da sauri  da kyar na samu na iya mikewa ba kowa ba komai a dakin sai duhu da yamamaye dakin ta kara jin wani tsoro domin ba abunda bana tunani a wannan lokacin.  Na daga hannuna cikin duhu na fara lallube ko zan ji handset ko kuma abun kunna wuta Allah da ikonsa kuma akwai fitilan wuta na gefen gado don haka na qunna wutan naga kaina a wani daki daban wanda  ban san shiba a take nakara jin sabon tsoro wadda har tasa jikina yana qarqarwa ba abunda nake

tunani kar dai an sace ni ne...........

Wannan kidnapping da nake ji a katafen yada labarai yazo kaina yau.

Don haka na tashi tseye  da sauri game da tuge pitilan da ke gefen gadon  gabaki dayanta domin in riketa a matsayin makami na. Na taba kofan naji ba a kulle takeba don  haka na budeta game da lekowa naga kofofin wasu dakuna har biyu sai kuma corridor.

Cikin sanda kamar sabuwar barauniya duk da tsoro ne ke cike da zuciyana pal amma nasan bazan zauna ina mai jiran miracle dole nasan abunda ke faruwa sannan in san matakin da zan dauka . Da wannan tunanin na samu karfin gwiwa nashire tsorona , nafara takowa har na kai karshen corridon.

Wata karamar parlour ce a gefe sai kuma matakalan bene,don haka nafara takata har na kusan sauka kasa. Sai ganin Ya Saif zaune a kujera a gaban sa computer ne da yeke dannawa da kuma cup na shayi ne ko coffee ne ban sani ba,sai a lokacin na tuna ashe mun bar main house zamu dawo gida ,gidanshi ne wannan. Kukulwata ta kara min nayi aure

Yanzu a

matsayin matansa nake kenan .

A lokacin ne kuma hankalina ya dawo jikina in dai zan iya tonawa ya daukoni daga main house , kaman bacci ya dauke ni a mota tunda bansan yanda muka iso gidan ba kar dai tun a mota nayi bacci ? .
Tambayan da nayiwa kaina kenan to tabbas dazo nayi bacci a mota, da muka iso waye ya  shigo dani ko kuma da kafata na tako nashigo gidan ne ko ya akayi ne oho?

kan na farga daga tunanin da nakeyi naji na taka wayan pitilan da nake rike da ita a hannuna na sulube zuwa kasa . Allah ya so ni saura taku daya ne in karasa saukan benen ba wata  nisa sosai ba.  

Fadowa yayi dai dai da lokacin da ya Saif ya daga cup dake hannunsa zai kai shayine ko coffee da yeke gabansa zai kai bakinsa,yana gani na shima ya taso da saurin sa . Kan ya karasa har na fadi kasa Tim kake ji.

Ko da ya karasa in
da nake bai ce mini komai ba hannun sa ne yasa ya duba kafana cikin ikon Allah ban buga kafan ba ko naji wani ciwo ba don haka ya taimaka min natashi seye.

Murmushi yayi wanda bai kai zuciya ba ya kai dubansa zuwa gareni "ki dinga maida hankali kina duban takonki don ba kullum zaki yi sa'a" . Wani kololon bakin ciki ne ya seya a makwogorona. Me yeke nufi ne? Ban iya tanka masa ba na kara gyara sayowata da kaina .

"Welcome home dear"

kalman da naji ya furta kenan cikin lallausan murya,bangama mamakin sa ba na kara jin yece

"zo kici abinci kada yayi sanyi" . Bai tseya wani bata lokaci jiran jin amsana ba yayi gaba abunsa ya barni .

Ni dai tsandarewa nayi wajen domin razane nake,  ban samman jin wannan kalmomi daga gareshi ba. Yau itace  ranana na farko a gidansa, daga 'kan da zan yi na gansa yana tseye da alama ni yeke jira don haka ban bata lokaci na'ba na bishi zuwa wajen cin abinci .

Kwanokan abinci ne na alfarma a jere akan dining table din, bayan da ya zauna yaja plates guda biyu. Ya bude kwanokan.  sinasir ga kuma pinkasau, da miyan alaiyahu sai pepper chicken da kuma potatoe casserole, sai kuma miyan tuwo da miyan kuka da nagani.

SANADINKI NE ! Where stories live. Discover now