BABI NA BIYU

257 29 10
                                    

SANADINKI NE!

BABI NA BIYU
Nasan dai a ra'ye nake, na riga da na tabbatar da hakan, domin ina jin motsi a kusa dani . Duk dai da na ƙasa buɗe idanuna naga komai , amma kuma bai hanani jin hayaniyan mutane sama-sama a kaina ba. Ba inda baya mini ciwo a jikina ,bazan iya taɓa waje ɗaya ince ga inda yeke mini ciwo a jikina ba.
" ta dawo hayyacinta, ta farfaɗo" . Naji an faɗa a kusa da ni ,ban gane mai muryan ma ba , anya nasan wannan muryan ma , tabbas ban san wannan muryan ba. Nayi kokarin ganin na bude idanuna ,hakan ya gagareni, nayi kokarin juyar da kaina na gagara kasancewar nauyin da naji kaina ɗin ƙeyi . Sai da na bari na ɗan huta kaɗan sannan na sake godawa wannan karon cikin ikon Allah , ya bani ikon buɗe idanuna , duk da dai ina jin ɗayan idon na mini nauyi.

Mutanen da nagani seye a kaina da farin kaya ya bani tabbatacin lallai likitoci ne, duba da nayi da yana yin gadon da kuna maida hankali na da nayi da kallo zuwa dakin yasa nagane a asibiti nake. Tou me ya kawoni asibitin , oho , nayi kokarin matsawa kwokwolwata amma hakan ya gagare ni, ganin na kasa tuna komai yasa na maida hankalin wajen ganin na motsa kafafuwana da hannuwa na da suka kasa motsi . Likitan ne ya katse mini kokarina na ganin meya hana gabbobin jikina motsi . Ya Allah ka tsare ni badai wannan ciwon shanyewan ɓarin jiki da nake jin labari bane ya sameni ni ƴasu ! Tambayan da na yiwa kaina kenan.

" Khairat kina jina"

ɗaya daga cikin likitocin ya min magana , girgiza kaina nayi . Alaman eh kuma a take nayi mamakin yanda kaina din ya juwe. Ɗaya daga cikin likitonci yece " kaman fa tana jinmu, gashi ta amsa ? "
naji wani yece "kaman bugun zuciyanta ya karo" ya rike hannu na, ko ba a fadi ba nasan agogonsa yake dubawa, ya sunkuya kusa da kunnenna . " kaɗa ki ji komai ,insha Allah komai zai zama normal. For now zaki dinga jin nauyi a jikin ki amma kada ki damu ba komai bane, hakan na faruwa don katsewan da kwokwolwanki yayi na lokaci kadan. Nanda zuwa mintuna ko awanni kadan komai na jikinki zai koma aiki normal ." tun ya fara magana ina kallonsa Jinshi kawai naƙe yi , bana ma gane me yeke cewa sosai .
" zan fadawa yanuwanki kin farfad'o so that hankalinsu ya kwanta ."

Kiran sunan yan uwana da yayi ne , yasanya ni tunowa da abunda yafaru , dalillin shigana wannan halin. A take zufa ya fara kwarorowa daga jikina duk da sanyin na'urar sanyaya ɗaki dake aiki. Mommy ce tafara shigowa dakin , Dady na biye da ita. Ido biyu mukayi da Mommy da tayi wani irin fari ta fige a dare daya, na kara jin tausayin ta sanin yanda suke fi shakuwa sosai da Adda Shukran . A cikin hanzari ta iso dab da gadon na ke kwance hannuna ta rike.

" Khairat ya jiki ? Sannu pls ki gafarta mini kinji pls stay kada ki tafi ki barni kema ". Murmushi nayi tare da ajiyan zuciya. Na kara godewa Allah da ya farfado da ni daga karamin mutuwa da nayi , da kila daga hakan sai mutuwa .

" sannu khairat "

Naji muryan Dadyna shi ya katse mini tunanin da nake yi . kai kawai na iya girgiza mishi har yanzu muryan taki fitowa. ina kallonsa , shima ɗin ni yeke kallo. Tausayi ya bani ganin damuwa da tashin hankali kwance a saman fuskansa. Bayan dakikai da basu fi biyar ba na cire idanuna da ke kallonsa.

Likitan dazun ne yesake lekowa " can i come in "
" Bismillah Dr. Ka shigo mana kai da aikinka kuma sai ka tseya wani tambayan izini " .

Yana shigowa wajen da nake yazu direct , kin tuna da ni ni ne Dr Moh'd da fatan bazaki damu ba zan kara dubaki. kaina a girgiza masa ya fara wasu aune-aune. Bayan da yagama aune-aunen sai da yayi rubuce-rubuce a cikin folder na , ya kara mini wasu tambayoyi ko akwai wani abun da ke mini ciwo , na girgiza kaina alaman ba komai, sai dai maganan da banayi , na nuna masa da hannu, murmushi yayi ba komai shima zuwa anjima zaki fara yi da yardan Allah. Dady dake a tseye kusa da Dr ne yafara tambayansa. " Ina fatan dai babu wata matsala da ke damunta " ya karasa maganan yana mai kallon likitan. " Ba komai your Excellency, so far dai ba komai a iyakacin binceken da muka mata ba bu abunda ke damunta komai yana normal. yanzu dai tana bukatan hutu akwai wani allurar da aka mata dazu wanda zai kara bawa kokolwanta daman hutawa, zata dinga bacci tana farkawa. zuwa anjuma in ta tashi sai muga me ake ciki . Zamu riketa awowi kaɗan under close observation . Zamu sallameta zuwa nan da sha daya in munga ba wata matsalan ." sai da yagama bayani ya sannan ya dan dakata kadan don yaga yanayin yanda suka dauki bayanin " ba komai Dr. Duk abunda kaga yakamata kuyi, kuyi ɗin ,i'll give you 100 % support , Allah dai ya bata lafiya shine burinmu mukam " Ameen .

Ya mikawa dr din dake kokarin fita hannu suka dada handshake . kafin likitan ya fito daga dakin ya fada mana a kan nurses da drs zasu dinga shigowa don daukan Bp da pulse nawa.

Mummy ce da ke zaune a kujeran dake dan nesa dani tun shigowan dr din ta dawo kujerar dake kusa dani . "khairat sannu hai. Ina fatan dai babu inda ke miki ciwo" a hankaki na furta " eh " Alhamdulilah jin muryana ya dawo . yatsuna na sanya Ina goge hawayen da ke saukowa har yanzu daga idonta. " I'm ok Mum stop crying. I'm feeling better now "

Daddy dake tseye yana kallon su ji yeke kaman yeje ya rungumi matarsa da yarsa ya lallasheta , amma hakan bamai yiwuwa bane a gaban yarsa. Don haka ya tako zuwa wajen da suke , yayi abunda yasan zai iya yi a yanzu. Yasanya hannayensa a kan kafadanta
" ki kwantar da hankalinki fateema . addu'a itace maganin ko wani matsifa da bala'i ." hannunta da ke rike da na khairat ta saki , sannan tasanya akan na maigidanta . " ba komai Habibi na. Everything
shall be well insha Allah. "

kallon su nake , ina kara sha'awan yanda suke lallashin junan su a ko wani lokaci in abu ya bullo musu. Har bacci yayi awon gaba dani.

Dada Sukabe ce!👌🏻

SANADINKI NE ! Where stories live. Discover now