BABI NA TARA

147 23 12
                                    

SANADINKI NE!
©
MARIYA JIKA

BABI NA TARA
 

Khairat

Me yasa kika aureni ta nanata tambayan da yamata yakai sau goma a bakinta, bayan yasan dalili meyasa yeke tambayanta wannan tambayan mara ma'ana nan!

A hankali ta daga kanta ta watsa masa kyawawan idanunta wanda suke farare tas kaman madara . Shima dai idon ya zuba mata yana jiran me zata ce masa. Mikewa tayi batare da tace masa komai ba ta haura zuwa sama da guduwa bata tseya ko inaba sai dakin da taga kanta lokacin da ta tashi daga bacci.
Kuka ne take son tayi amma bata son ta nuna masa how weak she is. Don haka ya zaman mata dole ta hadiye kukan domin tasan rayuwanta da zaman gidan ba zai zame mata abu mai sauki  da kwanciyan hankali ba,  tasan Saif he will do whatever it takes to make her life miserable amma ta riga da ta shirya wannan duk abunda zatayi don taga mutuncin iyayenta bai zube ba a idon duniya zatayi, sannan zatayi kokari taga suna cikin farin ciki da kwanciyan hankali.

Adda Shukhrah ina kike ne meyasa kika tafi kika barni ba tare da kince min komai ba ,ina bukatan explanations daga gareki I thought we're friends Adda ta.

****

Ido kawai Saif ya bita dashi domin bai taba sammanin zata kasa bashi qaqqauran dalili ba a sanin da ya yiwa Khairat ba ta rasa ansa tou me ya hanata bashi amsan tambayansa?.

Rurin wayansa shi ya katse tunanin sa yana dagawa yaga P.A dinsa na yakira batare da bata lokaci ba yadaga call din , yana amsawa yasaka a kunnensa

" Master".

aka kira daga dayan layin

"ina sauraranka"

Bushashen nyawu Rayyan ya hadiye  sannan ya fara magana tsanin halin Ogan nasa zai iya yanka call din idan yakara wasu dakikai.

"Mr Wang da Mr Tom sun kara dawowa kuma wannan karon trouble da suke causing ba kadan ba"  Yana kai aya yayi shiru don yana jiran me Ogan zai ce masa.

Gefen bakin Saif din ne ya motsa  alaman murmushi " kasan dama mun san zasu dawo, ba bata lokaci this time around just deliver the package" yana fadan haka ya katse layin bai jira yaji ko me Rayyan din zai ce ba.

Bai tseya bata lokaci shima ba ya kashe fitilon parlourn ya haura sama domin he has alot to deal with yanzu a kansa.
Yana zuwa kofan dakinta yaga wutan dakin a kunne, yaji dai yakamata ya shigo yakara tambayanta amsan tambayan da ya tambayeta wadda  taki ta amsa masa dazun sannan kuma ya gindaya mata wasu sharudan zaman gidansa. Shi mutum ne mai ka'idoji. Idan tana son zama dashi cikin kwanciyan hankali dole ta kiyaye wasu dokokin

****
  CANADA

Sukhran dai sai tunani daban daban takeyi tun Habeeb ya haura sama ya barta , ta kasa gane yanda zata warware zaren da ya dabai bayi rayuwanta duk tunaninta yanda zata gudu daga hannun Habeeb  takeyi. Ita ba bakuwar Canada bace tayi kusan shekaru shida a garin, sannan kuma ita bawai mai zama waje daya bane no tana son outing tun asalinta lokacin da take karatu once idan bata yin komai dai yawon zagaye gari take yi . Tayi zagaye  gari sosai a wani wajen ma ko yan gari basu san dashi ba tasani, lokacin da ta hadu Habeeb kuma sai Allah yasa son yawonta ya karu yana daga cikin abunda yasa halin su yazu daya da shi shima mai son yawo ne. Infact fiye da rabin rayuwanta a makarantan dashi tayi a garin. Kasan cewansa dan gari ya dinga jakoranta zuwa wasu wajajen. Ajiyan zuciya tayi da tuna da wannan taga lallai tana da hope akan guduwa ta ya kamata tafara daukan one step at a time, yakamata ta sake jiki ta nuna masa komai normal ne domin tasamu hanyan kubuta daga garesa.  tana cikin tunani wata mai aiki ta katseta, yarinyan da bata fi shekara sha hudu ba daga ganinta yar latin America ce , sanye ta ke da kayan aiki ta mata magana cikin daraja.

"Ma'am the table is set" murmushi ta yiwa yarinyan kamun ta ce wani abu har  yarinyan ta juwe da sauri ta tafi. A lokacin kuma ta daga kanta ta duba saman benen wanda yayi dai-dai da  saukowan Habeeb daga sama , yana tafiya cikin taqama da kasaita, bai ce mata komai ba ya wuce zuwa dining din haka ita ma tamike tabi bayansa, don tasamu ta cika tumbinta,  don kwanan ta biyu bata iya cin abun kirki. Duk abincin da aka hada akan teburin din favorite nata ne don haka bata seya wani bata lokaci ba tafara kwasan girki duk da dai bawai wani jin dadin taunan abincin take ji ba, ba yanda ta iya dole ta nuna ma Habeeb ba ta da matsala a gidan idan tana son ta cimma burinta . Shima dai yayi mamakin ta murmushi kawai yayi batare da yece mata komai ba .

****

Daddy ne ya shigo dakinsu yatarar da Mummy tayi tagumi da alama tunani take yi bata ji shigowan shi ba. Don tunanin da takeyi cike da tausaya wa ya iso inda take yasan yanda take close da yaran more especially Shukhran wanda tayi kusan shekaru bakwai ( 7 yrs ) kamun Allah yakara bata haihuwan Khairat . Gashi lokaci daya sun watse kuma irin rabowan nan mai zafi don haka aikin sa ne ma yafara  lallashinta kada ta jefa kanta cikin wani halin Allah yasani baya fatun wani ya samu matarsa dole ne  ya kwantar da hankalin yar lelensa.

Duk da yanda Mummyn ke nunawa bata cikin damuwa tana ta kokarin nuna abunda yafaru bai dameta ba, shi yasan matsalan na kasan ranta yana ganin ta yasan damuwa ce kaf a tattare da ita.

Da yeke gidan kwana biyu mutane da hayaniyan biki bai barsu sun zauna cikin natsuwa sun tattauna akan abubuwan da ke faruwa ba.
Waje ya nema a gefen gadon ya zauna ,hannun sa yasanya a saman kafadanta ya d'an matsa mata a hankali murmushi ta masa wanda yana gani yasan yana tattare da ma'anoni da yawa a hankali ya kawo bakinsa kusa da kunnenta har tana jin hushin numfashinsa a kunnenta" Eesha ta ya kike ?" murmushi tayi sannan ta shafa fuskansa wani irin farin ciki ne taji mara misaltuwa abu daya tasani Muntarin ta kullum zama saurayi yekeyi duk da shekaru sun ja but bata ganin sun tsofa kullum dad'a sundumata a kogin soyyaya yeke yi. Abunda takewa yaranta fata kullum sai gashi an wayi gari ba abunda kake fata ba zaka samu kullum a rayuwa. Hawayen da take kokarin matsewa ya gangaro a fuskanta abunda take kokarin dannawa ya fito. Murmushi daddyn ya mata game da janta a jikinsa gabaki d'aya a lokacin ba abunda suke bukata sai su bawa zuciyoyinsu fili don suyi magana su jajanta wa kansu sannan su lallashi juna.

***

Ciki-ciki Saif yayi sallama game da tura kofan dakin ya shigo, dai-dai lokacin kuma Khairat ta mike tseye a tsorace ganin sa da tayi a dakin . Kallon sama da kasa Saif ya mata sannan ya fara magana " I asked you simple a question ki kasa amsawa me kike nufi ne o kullum idan na tambaiki abu haka zaki gudu. Murmushin da bai kai zuciya ba yayi. Whatever dai ni ina son kisani ina da dokoki a gidan nan .

Na farko:  banda mini magana
Na biyu : banda shiga sabgata more especially dakina, gym da kuma study na.
Na uku : Duk abunda kike bukatan defawa na cikinki ki ci kina iya ci ke kadai amma banda hadawa dani.
Na hudu banda yawan hayaniya idan ina gida bana son noise da chattering a gidan nan.
Na biyar : Duk inda kiga daman zuwa kije kiyi rayuwan ki normal wannan ba matsala na bane.
Idan kin kiyaye kin tsira daga fushina ... Har ya juwe zai tafi ya juwe ya watsa mata wani kallo da batasan ma'anan sa ba yayi gaba abunsa.

Bata san sadda ta fadi ta durkushe a kasa tafara kuka ba.

Khairat wani rayuwa ne kika jefa kanki a ciki wani rayuwa zakiyi a gidan nan ?

Shin Saif wani irin mutum ne ?

****

Hello my lovey- lovey ina gaisuwa ya zaman gida hope har yanzu muna bin ka'idodi a ci gaba da wanke hannu , yin tazara da kuma saka takonkonin fuska. Allah ya kowo man saukin lamrin nan .

Pls don't forget show love 💖💖 and support for me by just pressing the star and tell me what you think and your thought  so far on the book in the comment box.

Thanks with much love ❤❤

Stay safe 😍😍

Dada sukabe ce👌

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 29, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SANADINKI NE ! Where stories live. Discover now