BABI NA HUƊU

241 23 21
                                    

SANADINKI NE !

BABI NA HUƊU
Mummy ne da Daddy zaune a ɗakin da aka kwantar da Khairat. Tun bayan da ta sake koma bacci bayan sallahn asuba, bata farka ba don haka suka fara tattauna yanda zasu warware wannan al'amarin . karshe dai suka yanke shawaran gwamma Daddy yakira amininsa ya fada masa abunda ake ciki. Don haka ya fito da wayanshi dake aljuhunsa ya danna ma Alh Usman kira . ya kirashi har sau uku bai dauka ba. Bai taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba ko a siyasan da yeke fatatawa bai taba tayar masa da hankali ba bai ma san yanda zai yi ba gashi dai lokaci na kara gabatowa.

" Bai dauki wayan ba Aisha , ina ga dai dole in sameshi a gida in faɗa mishi abunda muke ciki sa'annan mutattauna yanda za'ayi ."

Ajiyan zuciya Mommy tayi , fararen idonanta sun sha kuka har sun chanza launi zuwa ja. Tsakanin awanni kaɗan har tarame ta zama wani iri baza ka ganta ka ce wannan matan ita ce mommy ba mace mai son gayu. " Ba komai Habibi duk yanda kukayi , Allah yazaba mana abunda yafi alkhairi."

Tashin Daddy daga kan kujera dake ɗakin yayi dai-dai da ringing na wayansa , yana duba mai kiran yaga Alh Usman ne , "gashi nan ma ya sake ƙira" bai jira jin amsan mommy ba ya amsa kiran. Ya fada masa suna hospital don haka yana son yasa mesa a gida yanzu domin su tattauna akan wata emergency da ya taso. " eh a'a muna Nizamiye hospital , ok toh sai kazo bakomai ".

Tun lokacin da wayan yayi ringing Mummy taji zuciyanta ya tsinke. Shukran bata kyauta mana ba fisabilillah ƴaƴa zata mana haka ta kuma jefa rayuwanta cikin hatsari. kuma fa wannan auren ba tilastata muka yi ba . Sai da muka tabbatar ta amince sannan muka fara hidima. Da ta fada mani abunda take shiryawa da na san yanda nayi na sai da maganan. Hawaye ne masu zafi suke gangarowa . Daddy da yagama waya yake magana bata ji shiba yasa hannu ya share mata hawayen. " ki kwantar da hankalinki don Allah Aisha ta , ki dubi Khairat, dani da sauran yaran kaɗa kisa maganan shukran a ranki , kija mana hawan jini nasan ki da hakuri ki kara a kan wanda kike dashi."

wani kuka ne takara pashewa dashi " Daddy ya zama dole inyi kuka, Shukran bata kyauta ba , wannan ba tarbiyanmu ba.Ban sani ba ko karatun da taje tayi outside shi ya chanja tarbiyanta ?" ko sansan freedom ne na yaran yau" Murmushi yayi yaja dogon hancinta " look at you . Keɗin a ina kikayi karatu da kike cewa wai karatu a waje" hannunta ne ta hada da nashi " kamanta ni da aurena nayi karatun " . Kada
ki damu Eesha na riga da nasa anyi tracing nata insha Allah zuwa anjuma zamu ji bayani." Manya-manyan idanunta ne taware " da gaske ?" gira yadaga mata gira "of course mana dear" batasan sadda ta rungumeshi ba ya daga fuskanta yana mata murmushi dake kwantar da hankalinta, yasa yan ƴatsunsa yana goge mata sauran hawayen da ya gangaro daga idonta . Motsin da suka ji ne ya tuna musu da inda suke.

A hankali na buɗe idanuwana ban manta a inda nake ba waton a asibiti , har yanzu dai ina dakin da aka kwantar dani ne. A hankali na miƙe don
na zauna , Mummy ce ta taso da sauri tana son tayani " yi zamanki mum bakomai zan iya ," duk da haka sai da ta seya akaina .
" yajikin naki Khairat? " murmushi na mata " banajin komai Alhamdulilah naji sauki." da kaina na sauka daga kan gadon da nake kwance na wuce toilet . Bana sallah don haka brush kawai nayi, na watsa ruwa a jikina . lokacin da nafito daga dakin na tarar da baki . Uncle Usman ne da Ammie sai Anty ummi yarsu Mummy a ɗakin. Na tarar dasu suna gaisawa don haka nima na gaishesu sannan suka jajanta abunda ke faruwa.

Duk da idona a rufe bai hanani jin me suke tattaunawa ba , duk tsoronsu ɗaya ne kunyan duniya ,gashi kuma media haka kawai ma ya ake kare dasu da kirkiran labarun karya bare in an samu labari ai hadda na kari. Ga kuma baki da suka taso daga ko ina na sashen duniya don halartan auren jikokin Galadima . Alh Usman Galadima shi ne na ukun kudi a Nigeria sannan kuma na biyar a Africa. kuma daga dukkan bangaren manyan kusoshi ne biyu, ga yan jaridu, ga yan siyasa ga uwa - uba yan kasuwa. Tab akwai aiki ga social media a gefe an samu abunda za'a dinga yadawa kenan . Domin Saif dinma da kansa SOFTWARE Engineer da ake ji dashi a duniya.

Dada Sukabe ce!👌🏻

SANADINKI NE ! Where stories live. Discover now