1- Gabatarwa

1.2K 37 4
                                    


🍀🌺DUA BOOK OF A MUSLIMAH 📖🧕🏻💐
                        ( Hausa version ) By M.B Allau

.بسم الله الحمن الرحيم
Muna Farawa Da Sunan Allah, Mai Rahama , Mai Jin Kai.

Dukkan Yabo ya tabbata ga Allah Muna godiya gare shi. Muna neman taimakonsa, Muna neman gafararsa, Kuma muna neman tsarinsa daga sharrace- sharracen rayukanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi babu mai batar da shi. Wanda kuma ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, babu abokin tarayya gare shi, kuma Ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne. Allah ya yi tsira a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyakkyawan kwaikwayo har zuwa ranar kiyama , kuma yayi musu aminci, Aminci mai yawa.

Bayan haka, wannan littafi mai suna " DUA Book OF A MUSLIMAH" na hausa version na rubuta ne a matsayin sadakatul jariya zuwa ga yan uwana muslimai wanda karatun turanci da larabci yake basu wahala da kuma duk wani wanda zai amfana da wannan littafin.
Wannan littafi ya kunshi zikirai , addua daga littafi daban daban kamar su" Husnul Muslim", " 40 Rabbana , Durood da Sauran zikirai wanda ba ako wani littafin addua ake samu ba

Ina neman alfarmar duk Wanda ya karanta wannan littafi ya sakani cikin adduarsa.

Allah ya biya mana bukatunmu na alkhairi ya kare mana imaninmu.
Allah ya Bamu ikon sarkake niyyarmu ,zuciyonmu ya karemu da riya .
Allah ya jikan Musulmai ya shirya manah yaranmu
Allah ya kyautata karshenmu
Allah ya sa Aljannah ce makomarmu
Allah ya karawa Annabi daraja.❤️❤️❤️

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now