12- Addu'ar Istikhara da yadda ake yinta

519 17 10
                                    


Abunda ake nufi da ISTIKHARA shine bawa Allah (S.W.T) zabi, duk lokacin da mutum musulmi ya himmatu da niyyar aikata wani aiki wanda bai san hakiban wannan abun ba mai zai zo masa ba alheri ne ko shari ne toh wannan na so mutum ya bawa Allah zabi a kan abunda zai aikata don Allah shine yasan kashen al'amaru wato kasuwanci, tafiya ce, mu'amala ce ta kudi ko wani abu makammancin wannan, toh yana da kyau mutum ya baiwa Allah madaukakin sarki zabi don Allah ya zaban ma ka abunda yafi alheri.

Jabir ibn Abdullah, Allah ya yarda dashi da Maihaifinsa ya ce:Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koya mana yin Istikhara (nemanzabin Allah) a cikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kan ce:

"Idan dayanku yayiniyyar yin wani al'amari to yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannan ya ce:

ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺘﺨﻴﺮﻙ ﺑﻌﻠﻤﻚ
ﻭﺃﺳﺘﻘﺪﺭﻙ ﺑﻘﺪﺭﺗﻚﻭﺃﺳﺄﻟﻚ ﻣﻦ ﻓﻀﻠﻚ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢﻓﺈﻧﻚ ﺗﻘﺪﺭ ﻭﻻ
ﺃﻗﺪﺭﻭﺗﻌﻠﻢ ﻭﻻ ﺃﻋﻠﻢ ﻭﺃﻧﺖ ﻋﻼﻡ ﺍﻟﻐﻴﻮﺏﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻛﻨﺖﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ
ﻫﺬﺍ ﺍﻷﻣﺮ ‏) ﻭﻳﺴﻤﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ ‏( ﺧﻴﺮ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ ﻭﻣﻌﺎﺷﻲﻭﻋﺎﻗﺒﺔ
ﺃﻣﺮﻱﻓﺎﻗﺪﺭﻩ ﻟﻲ ﻭﻳﺴﺮﻩ ﻟﻲ ﺛﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻲ ﻓﻴﻪﻭﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ
ﻫﺬﺍ ﺍﻷﻣﺮ ﺷﺮ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ
ﺃﻣﺮﻱﻓﺎﺻﺮﻓﻪ ﻋﻨﻲ ﻭﺍﺻﺮﻓﻨﻲ ﻋﻨﻪ ﻭﺍﻗﺪﺭ ﻟﻲ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺛﻢ ﺭﺿﻨﻲ ﺑﻪ .
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﻣﺮﻓﻮﻋﺎ

"Allâhumma inni astakhiruka bi ilmika wa astaqdiruka biqudratika wa as'aluka min fadlikal-azimi, fa innaka taqdiru walâ aqdiru wa ta'lamu walâ a'lamu wa anta allamul ghuyubi. Allâhumma in kunta ta'lamu anna hâdhal amra khayrun li fi dini wa ma-ashi wa aqibati amri faqdir-hu li wa yassir-hu li thumma barik li hihi wa in kunta ta'lamu anna hâdhal amra sharrun li fi dini wa maâshi wa aqibati amri fasrifhu anni wasrifni anhu waqdir liyal-khayra haythu kâna thumma ardini"

Ma'ana: "Ya Ubangijina! ina neman zabinka da iliminKa, ina neman tabbatuwar ikonKa, ina rokan falalarKa Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi, Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai ne masanin abin da yake boye.
Ya Ubangiji na! In kana ganin wannan abu (sai ya fadi abin da yake istiharan a kai) shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min da shi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka a cikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri ne gare ni a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma ka juyar da ni daga gare shi, ka qudurtarmin da alkhairi sannan ka amintar min da shi" [Bukhari].
.
Duk wanda ya nemi za6in Mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba Insha Allah. Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce:
.
"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka quduri aniya, to ka dogara ga Allah".

Ba mafarki ake yi ba kamar yadda mutane dayawa suka dauka, ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, idan aure ne sai kajizuciyar ka ya qara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kake so ka fara sai kaji zuciyar ka yanutsu da sana'ar. Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana, ba dole sai da daddare ba, sannan ka yi tayi ne daga lokaci zuwa lokaci har sai ka sami biyan buqata.

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now