3- Aamanar Rasoolu ( Fassara da Falalar karantasa)

575 17 0
                                    

بِسْم الله الرحمن الرحيم

ءامن الرسول بما أنزل إليه من ربه والمؤمنون كل ءامن بالله و ملئكته و كتبه ور سله لا نفرق بين أحدٍ من رسله و قالوا سمعنا وأطعنا غفرانك ربنا و إليك المصير ، لا يكلفُ الله نفسا الا و سعها لها ما كسبت و عليها ما اكتسبت ربنا لا تؤاخذنآ ان نسينآ أو اخطأنا ربنا ولا تحمل علينا إصراً كما حملتهُ علي الذين من قبلنا ، ربنا ولا تحملنا ما لاطاقه لنا به وأعف عنا واغفرلنا وارحمنا انت مولٰــنا فانصرنا علي القومِ الكفرين .
(البقرة:٢٨٥-٢٨٦)
 
Aamanar-Rasoolu bimaa unzila ilayhi mir-Rabbihi wal-mu'minoon, kullun aamana billaahi wa malaa-'ikatihi wa kutubihi wa Rusulihi, laa nufarriqu baina ahadim-mir- Rusulihi, wa qaaloo sami'naa wa ata'naa ghufraa-naka. Rabbanaa wa ilaikal-maseer. Laa yukallifullaahu nafsan illa wus'ahaa, lahaa maa kasabat wa alaihaa maktasabat, Rabbanaa wa laa tahmil alainaa isran kamaa  hamal-tahu 'alal -latheena min qablinaa, Rabbanaa wa laa tuhammilnaa maa laa taaqata lanaa bihi, wa'fu annaa, waghfir lanaa warhamnaa, Anta Maulaanaa fansurnaa 'alal-qawmil-kaafireen.

FASSARA :
"Manzon Allah ya yi  Imani da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da muminai. Kowannensu ya yi Imani da Allah , da mala'ikunsa da littattafansa, da manzanninsa. Ba mu rarrabewa a tsakanin daya daga Manzanninsa. Kuma (muminai) suka ce, "Mun ji kuma mun yi da'a :( muna neman) gafararka, ya Ubangijinmu , kuma zuwa a gare ka makoma take. Allah ba ya kallafa wa rai face abin da zata iya; tana da kadai abin da ta tsirfata, kuma a kanta akwai zunubin abin da ta aikata: "Ya Ubangijinmu ! Kada ka kama mu, Idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskura. Ya Ubangijinmu! Kuma ka aza mana nauyi a kanmu, kamar yadda ka aza shi a kan wadanda suke a gabaninmu. Ya Ubangijinmu! Kada ka sanya mu daukar abin da babu iko gare mu da shi. Kuma ka yafe mana, kuma Ka gafarta mana , kuma ka yi Jin kai gare mu. Kai ne Majibincinmu, saboda haka ka taimake mu akan mutanen nan kafirai".

FALALAR AMANAR RASOOLU :
1- Lallai Allah ya kare suratul Baqara da ayoyi biyu wadanda ya saukar mana dasu daga taskarsa da take karkashin Al'arshi, don haka sai ku sansu kuma ku koyawa matan ku da 'ya'yanku domin addu'a ce, kuma karatu ne. " (Imam  hakim ya ruwaito daga Abu Zar (RA)...
2- Annabi (SAW) yace: "Akwai wasu ayoyi guda biyu na karshen Suratul Baqara , duk wanda ya karanta duba dare sun isheshi kariya". ( Ahmad da Bukhari da Muslim da dan Majah ne suka ruwaito shi daga dan Mas'ud (RA).
3- Ibn Abbas ya ruwaito cewa: " lalle Manzon Allah (SAW) yana tare da Mala'ika jibril, sai yaji wani sauti daga sama, sai jibril ya duba saman, sai yace Wannan wata kofar ce aka bude ta a sama yanzun nan a sama, kuma ba'a taba bude ta kafin haka". Sai wani Mala'ika ya sauko ta wannan kofa zuwa Manzon Allah yace : " Ka amshi wannan labarin na haske guda biyu wanda aka baka kuma babu wani Manzo gabanin ka da aka bashi su: Fatihatul Kitab da ayoyi biyu na karshen Suratul Bakara . Ba zaka karanta harafi daya ba daga cikin su face an baka ladansu".
( wannan hadisi Muslim ne ya faitar da shi, da Nasa'i amma wannan lafazi na Nasa'i ne).

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now