2- Aayatul Al -Kursiy ( Fassara da Falalar karantasa)

829 25 0
                                    


بسم الله الرحمن الرحيم

الله لا اله الا هو الحي الْقَيُّوم ، لا تاخذه سنة ولا نوم له ما في السموات وما في الارض من ذَا الذى يشفع عنده الا باذنه يعلم ما بين أيد يهم وما خلفهم ولا يحيطون بشي ء من علمه الا بما شاء و سع كرسيهًُ السموات والأرض ولا يؤده حفظهما وهو العلي العظيم. (٢٥٥)

  Allaahu laa ilaaha illa Huwal- Hayyul- Qayyoom, laa ta'khuthuhu sinatun wa laa nawn, lahu maa fis- samaawaati wa maa fil-ardh, man thal-lathee yashfa'u 'indahu illa bi ithnihi, ya'lamu maa baina aideehim wa maa khalfahum, wa laa yuheetoona bishay'im-min 'ilmihi illa bimaa shaa'a, wasi'a kursiyyuhus-samaa-waati wal-ardh, wa laa ya'ooduhu hifdhuhumaa, wa Huwal-'Aliyyul-' Aziim.

FASSARA
Allah , babu wani Ubangiji face shi, rayayye, tsayayye, gyangyadi ba ya Kama shi, kuma barci baya kama shi. Shi ne da da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasa. Wanene wanda yake yin ceto wurinsa, face da Izininsa, Yana sanin abin dayake a gaba gare su da abin da yake a bayansu. Kuma ba su kewayewa da kome daga ilminsa, face da abin da ya so. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da kasasai. Kuma taste su ba ya nauyayarsa. Kuma shi ne Madaukaki, Mai girma. (Q .2:255)

FALALAR AYATUL KURSIYYI
1- Sunan Allah mafi girma wanda idan an kira shi yake amsawa yana cikin surori ne guda uku(3) ; Suratul- bakara, Al- Imran da Taha. Wani babban malamin kasar Dimashka, Hashim bin Ammar, yace a cikin Suratul - Bakara sunan na cikin:
( الله لا اله الا هو الحي القيوم)
Allahu Laa illaaha illa Huwal-Hayyul-Qayyum
Allah! Babu abin bauta ( da gaskiya) sai Shi, rayayye ne kuma tsayayye ( akan komai) Q .2 : 255
2- Itace mafi girman aya a cikin Al-kur'ani mai girma. Ubayyu bin ka'ab yace, lalle Manzon Allah (SAW) ya tambaye shi ko ya san ayar da tafi kowacce girma a littafin Allah, sai Ubayyu yace " Allah da manzonsa su suka fi sani" Amma da Manzon Allah ya maimaita tambayar da akamai sai Ubayyu yace ; Ayatul kursi. Daga nan sai Annabi (SAW) yace: "Godiya ta tabbata ga Allah da wannan ilmi daka samu, ya Abu Munzir! na rantse da wanda Raina ke hannunsa wannan aya tana da harshe da laba biyu, wanda sune take yabo da godiya ga Allah kusa da kafar Al-arshin Allah .( Imam Ahmad da Muslim).
3- Duk wanda ya karanta ya da yamma, Allah zai bashi tsars daga shaidanu har Safiya. Kuma duk Wanda ya karanta ta da safe, Allah zai bashi tsaro har yammaci. ( Nasa'i da Tabarani).
4- Idan aka karanta Ayatul Kursiy aka tofa kan wani kaya ko yara lalle shaidan ba zai yi gigin kusantar wadannan kaya ko yara ba.
5- Annabi (SAW) yace: Akwai wata aya a cikin suratul Bakarah wannan ayar itace; shugaban ayoyin ba a karanta ta cikin gidan da shaidan yake face sai ya fita daga gidan; ita ce: Ayatul Kursiy( Hakim da Baihaki ne suka ruwaito shi daga Abi Huraira (RA)).

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now