25- FATAWA AKAN AZUMI

72 3 0
                                    

FATAWA AKAN AZUMI
GABATARWA
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalan gidansa, da sahabbansa.  Bayan haka, wannan dan karamin littafi ya kunshi fatawowi game da Azumin Ramadhan, mai Albarka, wanda Sheikh Abdulwahab Abdallah ibn Muhammad, yayi a yayin karba tambayoyi da suka shafi wannan babbar ibadah mai muhimmanci.  An yanke shawarar maida wannan aiki zuwa littafi saboda bukatar dake akwai cewar mutanen da basu samu halartar darasin basu samu gamsassun amsoshi da suka kunshi hukunce hukunce, na wannan azumi da abubuwan dake cikinsa kamar Sallar Asham/Tahajjud, I'tikafi, lailatul Qadri, da kuma Zakatul Fidri.  Kuma Mallam yayi kokarin bada amsoshi bisa gwargwadon fahimtarsa da koyarwar littafin Allah, sunnar Manzonsa (S.A.W) da fahimtar magabata na kwarai.  Da fatan Allah ya kyautata niyyarmu, kuma ya sanya wannan aiki ya zama karbabbe a wurinsa.  Sannan ya yafe kura kuran dake akwai a ciki.
Q. WANE IRIN ALBISHIR MANZON ALLAH YAKE YIWA SAHABBANSA KAFIN AZUMI?
Ans:- Ya tabbata wajen manzon Allah (S.A.W.) ya kasance yana yiwa sahabbansa bushara zuwan Ramadan yana basu labarin cewar a cikin watan Ramadan ana bude kofofin Rahama da kofofin Aljanna, kuma ana rufe Jahannama, sannan ana daure shaidanu, kamar yadda yazo a hadisin Abi Huraira (Sahihul bukhari, hadisi na 1899).
Q. YAUSHE NE WATAN RAMADAN YAKE TABBATA?
Ans:- watan Ramadan yana tabbatane da zarar anga jinjirin watan ko cikar watan Shaaban kwana talatin. Domin hadisi ya tabbata daga Abi Huraira yace Manzon Allah (S.A.W.) yac" kuyi azumi domin ganin wata, kuma kusha ruwa domin ganinsa. Idan kuma wata ya faku a gareku to ku cika Shaaban kwana talatin".
Q. SHIN ZAA IYA AMFANI DA KIRGEN KALANDA KO LISSAFIN TAURARI WAJEN TABBATAR DA WATAN RAMADAN?
Ans:- Daukar Azumi akan lissafin kalanda ko lissafin taurari bidiane domin haka bai tabbata ba daga bakin Manzon Allah (S.A.W.) ko magabata, ko ijimain malamai (duba fatawa na Ibn Taimiyya).
Q. SHIN WATA SAI KOWA YA GANSHINE SANNAN A DAUKI AZUMI KO KUWA?
Ans. Ana iya daukar Azumi ko da mutum dayane yaga wata. Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi dan Umair (R.A.) yace Mutane sun rigen ganin jinjirin wata sai na gayawa Manzon Allah (S.A.W.) cewar ni na ganshi sai Manzon Allah (S.A.W.) yace: "suyi azumi (duba Abu Dauda 2340, hakin da Ibn Hibban suka ingantashi, Hakim 423 Ibn Hibban 3438). Amma mafi yawan malamai sun ce ganin lallai mutumin daya ga watan ya zamanto adali watau wanda bazai yi karya ba.
T. SHIN IDAN ANGA JINJIRIN WATA A WATA KASA, MUTANEN DAKE A WATA KASA DABAN SUMA ZASU DAUKI AZUMI?
Ans. Hadisin Manzon Allah (S.A.W.) ya tabbata cewa ko ina aka ga wata ya shafi dukkan Musulmi ne gaba daya. Domin Manzon Allah (S.A.W.) yace idan kunga jinjirin wata, to ku azumceshi idan kun ganshi kuma to ku bude bakinku (Bukhari babi na sha daya Kitabus-Siyam). Idan kun gani anan yana nufin alummarsa gaba daya. Amma akwai sabanin malamai akan mafitar wata, wasu sunce ana iya ganinsa a wani wuri kamar Najeriya amma baa ganshi a Saudiyyaba don haka wasu malamai suka ce kowane gari ya dogara da ganin watansa amma mu mun runjayar da mun rinjaya akan maganar Manzon Allah cewa a wuri daya ya wadatar ga dukkan alummar Musulmi. Dalilin "fadar Allah Madaukakin Sarki" Zaa tambayeka game da jinjirin wata, kace masu shi lokutane ga mutane da Hajji. Kuma baa taba jin wadansu mutane sunce zasu yi amfani da ganin watansu ba daban wajen zuwa Hajji.
Q. MENENE MAANAR AZUMI?
Ans. Maanar azumi a Sharia shine kamewa daga dukkan abubuwan da suke bata azumi kamar ci da sha, jimaI da sauransu daga famar alfijir zuwa faduwar rana da niyyar bautawa Allah.
Q. MENENE DALILIN WAJIBCIN AZUMI?
Ans. Daliln wajibcin azumi shine fadar Allah Madaukaki yaku wadanda kukayi imani an wajabta muku yin azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka gabaceku ko kunji tsoron Allah." Kwanakine kididdigaggu. Kuma hadisin daya gabata na Abi Huraira ya nuna wajibcin domin Manzon Allah (S.A.W.) yace kuyi azumi idan kun ganshi.. wannan kuwa umarni ne.
Q. SU WANENE AZUMI YA WAJABA A GARESU?
Ans. Azumin Ramadan ya wajaba akan dukkan Musulmi baligi mai hankali kuma wanda yake da ikon yi, sannan mazaunin gida ba matafiyaba. Amma azumi baya wajaba akan wadannan.
1. Kafiri:- Azumi baya wajaba akansa, hakanan ramuwa bata wajaba a kansa idan ya musulunta a gaba.
2. Yaro:- wanda bai balagaba. Amma zaa umarceshi domin ya saba kamar yadda magabata suke yiwa yayansu.
3. Mahaukaci:- Azumi bai wajaba a kansa ba. Dalili kuwa Manzon Allah yace an daga alkalami akan mutum uku wanda  mahaukaci da yaro na cikin ukun daya ambata saboda haka idan mahaukaci sai ya rama azumi to yaro ma kenan zai rama azumin da yasha idan ya balaga. Haka ma mai bacci da yayi jimaI saboda haka malaman da sukace mahaukaci ya rama azumi basu da wata madogara daga Alkuani ko maganar Manzon Allah (S.A.W.).
4. Wanda ya gaza yin azumi saboda tsufa zai sha azumi kuma ba zai rama ba sai dai zai ciyar.
5. Mara lafiya wanda ba zai iya azumi ba to shi zai rama bayan ya warke. Amma cutar da ake tabbatar bazata warke ba, to wannan ma zai rika ciyarwa.
6. Matafiyi:- Azumi bai wajaba a kansa ba amma zai rama.
7. Mai haila to jinin biki:- baza su yi azumi ba, amma zasu rama.
Q. YAUSHE NE AKE DAUKAR NIYYAR AZUMI?
Ans:- Ana daukar niyyar azumine kafin ketowar alfijir idan ya kasance azumin farillane, domin fadar Manzon Allah (S.A.W.) wanda bai dauki niyyar azumi da dare ba (kafin ketowar alfijir) baya da azumi" Nana Hafsa ta ruwaitoshi (R.A.) Sheikh Albani yayi tahakikinsa a sahihu jamiu Sagir lamba na 6535 ko kuma sahihin NisaI, tahakikin Sheikh Albani lamba 2199).
Q. YAUSHE NE LOKACIN BUDA BAKI (SHAN RUWA)
Ans. Buda baki yana tabbatane da zaran rana ta fadi ko da mutum yayi buda baki ko bai yi ba. Dalili kuwa shine, hadisin Abdullahi Ibn Awfa yace mun kasance cikin tafiya tare da Manzon Allah {S.A.W.} alhalin cewa yana azumi, yayin da rana ta fadi sai yace wa wani daga cikin sashen sahabbansa ya kai wane ka tashi ka shirya mana abin buda baki  (farau-farau) sai yace ya Manzon Allah ina ma mun kara yammata (shin yana kokwanton faduwar rana ne) sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki sai yace ya Manzon Allah ina ma mun kara yammata sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki sai yace ya Manzon Allah ai akwai sauran rana sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki sai ya sauka sai ya shirya musu sai Annabi {S.A.W.} yasha ruwa sannan yace idan kuka ga dare ya gabato daga nan hakika mai azumi ya bude baki (ana nufin ko yasha ruwa, ko bai shaba) (Bukhari 1958 Kitabussiyam) kuma ya tabbata a cikin Bukhari daga Sahal ibn Saad Yace hakika Manzon Allah (S.A.W.) yace mutane baza su gushe cikin Alkhairi ba, matukar suna gaggauta bude baki. Amma abin mamaki a yanzu sai kaga mutane sun yi salla ba su sha ruwa ba, ko kuwa su bari har sai taurari sun bayyana, sannan su yi bude baki, tsammanin su yin haka shine dai-dai, alhali yin hakan ya saba ma sunna kamar yadda ya tabbata a hadisin da ya gabata.
Q. YAUSHE NE YAFI DACEWA AYI    SAHUR?                                                                           
Ans. A sunnace anaso a Jinkirta yin sahur zuwa kusan ketowar Alfijir. Hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik, daga Zaid bin Thabit (R.A.) yace "Mun ci Sahur tare da manzon Allah (S.A.W.) bayan wannan sai manzon Allah (S.A.W.) ya tashi zuwa sallah. Sai Anas ya tambayi Zaid bin Thabit minene tsakanin cin sahur da yin sallar Asuba? Sai ya ce gwargwadon Aya 50 (watau mutum ya karanta Aya 50)". (Bukhari, 1921, muslim 1097). Akwai kuma hadisin Sahl ibn Saad yace:- "Na kasance ina yin sahur cikin iyalina bayan wannan sai in yi gaggawa domin samu Sujada (Sallah) da manzon Allah (S.A.W.)". Wannan ya nuna cewa ana yin sahur ne dab da ketowar Alfijir (Bukhari, 1920).
Q.  IDAN MUTUM YANA CIKIN SHAN ABIN  SHANSA LOKACIN   SAHUR SAI YAJI KIRAN SALLAH YAYA ZAI YI?
Ans- Anan mutum zai karasa abin shansa ne. Domin hadisi ya tabbata daga Abi Hurairata (R.A.) yace:- Manzon Allah (S.A.W.) yace: "Idan dayan ku yaji kiran Sallah alhali kwarya tana hannunsa kada ya ajiye ta har sai ya biya bukatar sa (sai ya gama sha)". (Abi Dauda ya rawaito shi, Babi na 18, hadisi na 2060) Hadisin Sahihine, kuma Sheikh Albani ya ingantashi a cikin Sharhin Abi Dauda hadisi na 1350. Amma mutane suyi hattara kada su mai da wannan ya zama Aladar su kullum.
Q. MINENE BAMBANCI TSAKANIN AZUMINMU DA AZUMIN YAHUDU DA NASARA?
Ans- Bambancin Azumin Alummar Annabi Muhammad (S.A.W.) da na Yahudu da Nasara shine yin sahur da gaggauta bude baki. Hakika manzon Allah (S.A.W.) ya fada a cikin hadisin Amr bin Ass (R.A.) yace:- Abin da yake bambanta Azuminmu dana mazowa littafi shine cin sahur (Abi Dauda 2059, Muslim) Sheikh Albani ya ingantashi.
Q.   MINENE FALALAR YIN SAHUR
Ans- Hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik (R.A.) yace:-  Hakika manzon Allah (S.A.W.) yace Kuyi sahur, hakika yin sahur akwai albarka a cikinsa.(Bukhari 1923) saboda haka duk abin da manzon Allah ya ambace shi da Albarka mutum zai yi wasa da shi kuwa?
Q. DAMI AKAFISO MUTUM YA FARA BUDA BAKI?
ANS:- An fiso ya fara buda baki da danyen dabino, idan har bai samu ba sai yayi da busasshe, idan bai samu ba sai yasha ruwa. Dukkan wannan zai zama kafin yayi sallah ne, kuma an fiso yayi shine a mara (1,3,5,7,9,..).Domin hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik (R.A) yace manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana bude baki da danyen dabino kafin yayi sallah, idan bai samu danye ba, ya kanyi da busasshe, idan kuma bai samu busasshe ba sai ya kamfaci ruwa yasha.(Abi Dauda, Babin Bude Baki,2065). Hadisi ne  ingatacce.
Q. WACCE ADDUA CE TA TABBATA DAGA MANZON ALLAH (S.A.W) YAYIN BUDA BAKI ?
ANS:- Abdullahi dan Umar yace:- Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan ya bude baki sai yace Kishin ruwa ta tafi jijiyoyi sun jike, lada ta tabbata in Allah ya yarda.
" "
Hadisine Hassan idan aka hada hanyoyinsa (Sheikh Albani ya ingatashi a tahakikinsa na Dauda, Hadisi na 2066) amma mutum zai iya karawa da rokon Allah akan bukatunsa na duniya da lahira bayan yayi wannan Adduar.
Q.YAUSHE NE YA KAMATA AYI ADDUAR BUDA BAKI?
ANS:-Ana yin Adduar buda baki ne da zarar mutum yasha ruwa saboda hadisin daya gabata na Abdullahi bin Umar yace manzon Allah (S.A.W) yanayin Adduar ne bayan yasha ruwa (buda-baki).
Ans. Anan yin adduar buda baki ne da zaran mutum ya sha ruwa saboda hadisin da ya gabata na Abdullahi Bin Umar yace Manzon Allah {S.A.W} yana yin adduar buda baki bayan yasha ruwa (buda baki).
Q. MENENE FALALAR WATAN RAMADAN
Ans. Azumin Ramadan yana da falaloli da ywa. Daga cikin falalar azumin sun hada da:-
a. Yana kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Manzon Allah {S.A.W} yace "fitinar  mutum a cikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu". (Bukhari).
b. Yazo a hadisi, dukkan aikin Dan Adam nasane Malaiku suke rubuta shi, amma azumi wannan na Allah ne Shi Yake saka shi (hadisin ya tabbata a targhib wattarhib, juzI na farko shafi na 75).
c. Hadisi kuma ya tabbata daga Jabir dan Abdullahi (R.A.) daga Manzon Allah {S.A.W.} cewar azumi garkuwane da dan Adam zaiyi garkuwa dashi daga wuta. sannan hadisi ya tabbata daga Muazu dan Jabal (R.A.) cewa hakika Manzon Allah {S.A.W.} yace dashi shin bazan nuna maka kofofin alheriba? Sai yace naam ya Rasulullah sai yace azumi garkuwane kuma akwai hadisin Abi Umamata (R.A.) yace, "Nace wa Manzon Allah ka umarceni da waani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzuI na farko shafi na 578).
d. Azumi kuma shine sababin tsoron Allah.
e. A lokacin azumin Ramadan ana bude kofofin Aljanna, kuma ana kulle kofofin Jahannama sannan a daure shaidanu kamar yadda ya tabbata a hadisin Abi Huraira (Bukhari, 1899).
f. Hadisi ya tabbata wanda Imam Tirmizi ya ruwaito cewar Manzon Allah {S.A.W.} yace "Bashin bakin mai azumi yafi kamshi fiye da turaren miski a wurin Allah" hadisine sahihi. Sannan wani hadisin ya tabbata daga Sahl bin Saad (R.A) daga Manzon Allah {S.A.W.) yace a cikin Aljanna akwai wata kofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi zasu shigeta ranar tashin kiyama, babu wanda zai shigeta sai su. Idan sun shiga sai a kulleta babu wanda zai sake shiga (Bukhari 1896) Tirmizi ya kara bayani a cikin riwayarsa cewar wanda ya shigeta bazai ji kishin ruwaba har abada 
T- MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI YI?
A. Aikin da yafi falala ga mai azumi shine
1. Karatun Al'Kurani, ma'ana ya lazince shi dare da rana, kuma ya dinga izna da abin da yake karantawa.  Amma idan bazai iya karatun Al'Kurani ba, to sai ya rinka lazimtar inda ake karatun Al'Kurani ko fassarashi domin hadisi ya tabbata daga nana Fadima da Abu Huraira yardar Allah ta tabbata a garesu sun ce:
"Mala'ika Jibrilu ya kasance yana bijirowa da Annabi (S.A.W.) Al'Kurani sau daya a kowace shekara, sai ya bijiro masa dashi sau biyu a shekarar da zai yi wafati.  Bukhari da Muslim ne suka ruwaito (1).
______________________________________
(1)  Bukhari  K = 66, B = 7, H = 4998 da Muslim K = 44,  
      B = 15, H = 2450.
Wannan yana nuna cewa karatun Al'kurani shine mafificin ibada a cikin watan Ramadhan.
Allah madaukakin Sarki yace, "Lallai mun saukar dashi a daren Lailatul Kadari(1).
2. Kyauta:  Ya kamata mai Azumi ya yawaita kyauta wajen ciyar da jama'a, da sadaka, da taimakon gajiyayyu da makusanta.  Kamar yadda ya tabbata a hadisin ibn Abbas cewa: "Annabi (S.A.W.) yafi kowa kyauta, kuma mafi alkhairinsa yana yinsa ne a ramadhan yayin da yake saduwa da Jibrilu. Kuma ibn Abbas (R.A) yace Alkhairin Manzon Allah (SAW) yafi sakakkiyar iska".  Bukhari ne ya ruwaito shi (2).
(1)  Suratul Kadari Aya 1
(2)  Bukhari K = 1, B = 5, da Muslim K = 43, B = 12, H = 2308.
3. Nafil fili:  Ana so mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman kiyamul laili, saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara tabbata a gareshi yace:  Manzon Allah (S.A.W) yace: "Duk wanda ya tsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada; an gafarta masa zunubansa da suka gabata".  Bukhari ne ya ruwaito shi(1).
Haka kuma Manzon Allah (S.A.W) yace: Wanda yayi sallah dare tare da liman har
yagama za'a rubuta masa ladan kiyamullaili(2).
Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A) yace: 
_____________________________________
(1)  Bukhari K = 31, B = 70, H = 2009, da
      Muslim K = 6, B = 25, H = 760.
(2)  Targib Wattarhib wanda Albani yayi wa
        tahkiki lambar (1078).
"Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana tsawaita karatu a sallar dare a watan Ramadhan fiye da sauran sallolin dare, yace: Manzon Allah (S.A.W) yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a daya, kuma baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikin ta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari. Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A) yazo yana neman izni ayi sallar Asuba.  Ahmad ya ruwaito wannan hadisin kuma ya ingantashi.
4. Yawan Zikiri da Salatin Annabi (S.A.W):  Abune mai matukar falala mutum ya ya waita Zikiri da Salati ga Shugaban Halitta irin wanda ya tabbata daga bakin Manzon Allah (S.A.W).
5. Ciyar da mai Azumi abin Buda baki:  Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum yayi kokari wajen bawa dan uwansa abin Bude baki saboda hadisin da Annabi
(S.A. W) yake cewa:  "Duk wanda ya ciyar da mai Azumi abin da zai yi bude baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda ya ciyar ba".  Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih(1).
6. Umrah:  Yin umrah a cikin watan ramadhan ga wanda Allah ya bashi iko yana daga cikin Aiyukan da ake kwadaitar da mai Azumi yayi.  Amma duk da haka bai kamata mutum yatafi umrah ya bar makwabtansa da danginsa da sauran mabukata a cikin yunwa da halin kakani kayi ba.
Kuma ya kamata mu fahimci cewa, ciyarwa itace abinda Annabi (S.A.W) yafi ba muhimmanci a ckin watan Ramadhan.
T. WADANNE HALAYE YA KAMATA MAI AZUMI YA LAZUMTA?
1.  HAKURI:  Ya kamata mai Azumi ya lizimci hakuri, domin shine zai hana mutum bin soye soyen zuciyar sa, kuma shine zai bashi juriyar bin umarnin Allah. Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) cewa:  "Idan dayanku ya kasance yana Azumi, kada yayi maganganun fasikanci ko rafasu, kuma idan wani ya zageshi ko ya yakeshi yace:  Ni Azumi nake".  Bukhari ne da Muslim suka ruwaito(1).
_____________________________________
(1)  Bukhari K = 30, B = 2, H = 1894 da Muslim K = 13, B = 29,
      H = 1151
2.  RIKON AMANA:  Ya kamata mai Azumi ya kasance mai rikon amana, domin rikon amana zai taimaka masa wajen bada hakkokin da Allah ya umarce shi ya bayar.
Anan ya zama wajibi mu jawo hankalin wadansu daga cikin yan kasuwa wadanda suke amfani da watan Ramadhan wajen cutar da al umma wajen tsawwala farashin kayayyakin masarufi, da kuma yin algus ko yaudara a cikin ciniki, domin duk abinda aka samu ta hanyar haram shi zai sa cinsu da shansu da tufafinsu ya zama haram. Kuma wannan shi zai sa Allah yaki karbar Addu'arsu.
Anan ma muna kara jawo hankalin shugabanni wadanda Allah ya danka dukiyar Al'umma a hannunsu da su ji tsoron Allah su rike Amana, kada su dinga diban dukiyar al'umma suna yin umrah ko kuma su biya wa wasu mutane, domin Allah baya karbar ibadar da akayi da dukiyar haram.
3.  RAHAMA:  Ana son mai Azumi ya zama mai jin kai, karimi, mai yalwar zuciya da hannu, kuma mai son biyan bukatar Al'ummah gwargwadon hali. Domin Manzon Allah (S.A.W) yace:  "Duk wanda ya ciyar da mai azumi yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage ladan wanda aka ciyar din ba".
4.  NASIHA:  Ya kamata mai Azumi ya zama mai nasiha wajen hana munkari da umarni da kyakkyawan aiki. 
5.   SULHU:  Ya kamata mai Azumi ya zama mai yin sulhu a tsakanin mutanen da basa ga maciji, musamman tsakanin dangi, domin ya tabbata cewa:  kiyayya tana hana karbar ibada da addu'a, har sai masu adawar sunyi sulhu a tsakaninsu.
6.  RINTSE IDO DA KAME FARJI:  Ya kamata mai Azumi ya rintse idonsa ya kuma kame farjinsa daga dukkanin abinda Allah ya hana, musamman kallon matan mutane, da zina.
7.  KAME HARSHE:  Ya kamata mai Azumi ya kame harshensa daga giba (yi da mutane) da zagin mutane da cutar dasu da karya wacce ta zama ruwan dare a tsakanin al'ummah.
8.  IKHLASI:  Ya kamata duk mai azumi yayi domin neman yardar Allah, ba don mutane su yabe shi ba, kada kuma yayi don Allah da waninsa.
Anan muna jan hankalin yan uwa masu bada sadaka ko ciyar da masu Azumi da masu tafsirin Al'Kurani mai girma, da masu zuwa umrah, da limamai masu rera tilawa a sallar tarawihi, da masu sauran aiyuka na gari da su rinka yi domin neman yardar Allah.
9.  BIN SUNNAR MANZON ALLAH:  Ya kamata mai Azumi ya rinka koyi da sunnar Manzon Allah (S.A.W) sau da kafa a duk ibadar da zai yi.  Ya kuma nisanci dukkanin bidi'o'I, musamman bidi'o'in da ake yin su a cikin watan Ramadhan, kamar nafil fili da falaloli da ake bayarwa wadanda basu tabbata daga manzon Allah (S.A.W) ba,  ko magabata nagari.
10.  TARBIYYAH:  Ya kamata mai Azumi ya kula da tarbiyar gidansa musamman kangararrun yara wadanda basa Azumi ko kuma masu shaye shaye.
Kuma ya kamata iyaye su yawaita yiwa ya yansu addu'a, a cikin watan Azumi, domin Allah ya shiryesu.
T. YAUSHE AKE FARA SALLAR ASHAM?
A. Ana fara sallar Asham a daren da aka ga watan ramadhan, domin wannan daren daren ramadhana ne.
T. RAKA'A NAWA AKE YI A SALLAR ASAHAM?
A. Raka'oi goma sha daya ne suka tabbata daga Manzon Allah (SAW).  Wadannan raka'oin sun hada harda Wutiri.  Domin hadisi ya tabbata a cikin Bukhari, yayin da aka tambayi nana Ai'sha radiyallahu anha, yaya sallar Annabi (S.A.W) take a Ramadhan?
Sai tace:  "Manzon Allah (S.A.W) baya huce raka'a goma sha daya a ramadhan ko waninsa.". Bukhari ne ya ruwaito(1)
_______________________________________
(1)  Bukhari K = 21, B = 1, H = 1213
Kuma Nana Aisha taci gaba da cewa:  Kar a tambayi irin kyan sallar wajen (kyakykyawan) ruku'u, da Sujjada, kuma yakan dade har kafafunsa su kumbura.  Saboda haka duk wanda zai takaita akan raka'a goma sha daya, to ya kyautata sallar wajen koyi da manzon Allah (S.A.W) wajen tsawaita ruku'u da sujjada da tsayuwa.
T. SHIN AKWAI BANBANCI TSAKANIN SALLAR ASHAM DA TAHAJJUDI, DA KIYAMULLAILI?
A. Duk nafilar da akayi bayan sdallar Isha'i, ana iya kiranta asham, ko tahajjudi ko kiyamullaili.
Amma akwai wasu malamai da suke ganin ba'a kiran nafila tahajjudi sai wadda akayi bayan an tashi daga bacci, sai dai wannan ijtihadinsu ne kawai.
T. IDAN MUTUM BASHI DA HADDA ZAI IYA DAUKAN AL'KURANI YAYI WA MUTANE LIMANCI?
A. Na'am, domin Asar ya tabbata daga nana Aisha cewa: "tana gabatar da bawanta (Zakwan) yana duba Al'Kurani yana musu limanci a sallar tarawihi"(1).
Amma babu wani dalili akan mamu ya rinka duba Kur'ani yana bin liman, wannan wasane a cikin sallah.
T. MENENE HUKUNCIN AL'KUNUTI A KOWANE WUTURI NA SALLAR TARAWIHI?
Bukhari K = 10, B = 54
A. Yin kunuti a cikin wuturi ya tabbata Daga manzon Allah (S.A.W) a ramadhan ko waninsa, amma a kebance Kunuti a cikin Wutiri a ramadhana kawai, musamman goman karshe, wannan bai tabbata daga manzon Allah ba, ko magabata na kwarai, amma za'a iya yi wani lokaci wani lokaci kuma a huta.
*   Akwai Karin bayani akan wannan mas'alar wanda zamuyi nan gaba In Sha Allah.
T. MENENE I'TIKAFI?
A. Iitikafi ma'anar sa a larabci itace, Lizimtar wani Abu, da tsare kai.
Amma ma'anarsa a shariah, itace, lizimtar masallaci ga mutumin daya kabance kansa a wata siffa kebantacciya don yin ibadah.
I'tikafi ya tabbata a cikin littafin Allah da Sunnar Manzon Allah da Ijma'in Malamai.
T A'INA AKE YIN I'TIKAFI?
A. Ana yin Iitikafi a dakin makdisi, da sauran masallatai a bisa zance mafi rinjaye.  Saboda fadin Allah:  Kada ku kusance su (Iyalanku) alhali kuna masu Iitikafi a masallatai.  Kuma imamul Bukhari ya bude babin Iitikafi da cewa:  "Iitikafi a dukkanin masallatai" sai kuma ya kafa hujja da ayar da ta gabata.
Hafiz ibn Hajar yace anayin I'tikafi a dukkanin masallatai batareda kebance wasu masallatai ba, kuma yaci gaba da cewa jamhurun malamai sun tafi akan za'a iya yin I'tikafi a kowane masallaci.  Sai dai Imamu Shafi'I da wasu malamai sunce ana son (mustahabbi) wanda Juma'a ta wajaba a kansa yayi Iitikafinsa a masallacin Juma'a.
Amma Huzaifa ibn Yamani sahabin Manzon Allah (S.A.W) yace ba'a yin I'tikafi sai a masallatai guda uku;
Adda'u yace ba'a I'tikafi sai a masallacin Makka da Madinah;
Saidu bn Musayyib yace ba'a I'tikafi sai a masallacin Madinah(1).
Amma Hafizu ya danganta hadisin zuwa ga Manzon Allah (S.A.W), kuma Sheikh Albani ya inganta hadisin kuma yayi raddi ga wadanda suke ganin cewa hadisin maukufi ne.  Wannan hadisin shine dalilin Sheikh Albani akan cewa ba'a yin Iitikafi sai a masallatai guda uku (Masallacin Ka'abah, da Masallacin Manzon Allah (S.A.W), da Masallacin Baitil Makdisi)(2).
Amma wasu  magabata daga cikin sahabbai sun ce Huzaifa yayi wahami daga cikin su akwai Abdullahi bn Mas'ud sahabin Manzon Allah (S.A.W).
 
_______________________________________
(1)  Fathul Bari 4/319
(2)  Silsilatul a hadisussahiha (1/667) kashi na shida bugu
      na karshe maktabatu darul ma'arif Riyadh.
Domin Huzaifa ya ga almajiran ibn Mas'ud suna Iitikafi a tsakanin gidan Abdullahi bn Mas'ud da gidan Abu Musal ash ari sai yace bazaka hanasu ba?  Hakika kasan Manzon Allah (S.A.W) yace: "Ba a yin Iitikafi sai a masallatai guda uku, sai ibn Mas'ud yace: 
Watakila ka manta su kuma sun kiyaye, ko kuma kayi kuskure.  Su kuma sun yi dai dai(1).
Kuma kowa dai yasan Abdullahi bn Mas'ud wajen tsananin riko da sunnar Manzon Allah (S.A.W) amma duk da haka bai hana almajiransa yin Iitikafinba, domin yana ganin wata kila Huzaifa yayi wahamine ko ya manta.
_______________________________________
(1)  Al Mukniy Ash Sharhul Kabir na ibn Kudama al Mukaddasi, wanda Dr. Abdullahi Atturki Yayiwa Tahliki Juzi Na (7/577).
Abisa wadannan dalilai da suka gabata, duk wanda yake ganin cewa Huzaifa yayi wahami, kamar yadda Abdullahi bn Mas'ud Sahabin Manzon Allah (S.A.W) yayi nuni, to zai iya yin Iitikafi a kowane masallaci ba tare da ka'ida ba.
Hakanan duk wanda yake ganin cewa Khuzaifa baiyi wahami ba, kuma hadisinsa ya inganta, to sai ya takaita I'tikafinsa a masallatan nan guda uku.
Saboda haka muna jan hankalin daliban Ilmi musamman wadanda suketa jayayya ko kafirta juna akan wannan mas'ala da suji tsoron Allah su san cewa wannan mas'alace ta ilmi kuma akwai sabanin magabata a kanta.
T. YAUSHE AKE SHIGA I'TIKAFI?
A. Ana shiga I'tikafi bayan Sallar Asuba domin hadisi ya tabbata daga Nana Aisha yardar Allah ta tabbata a gareta tace:  "Idan Manzon Allah (S.A.W) yayi sallar asuba sai ya shiga gurin I'tikafinsa.  Bukhari da Muslim ne suka ruwaito(1).
Manzon Allah (S.A.W) yana shiga Iitikafinsa a daren ashirin da daya bayan yayi sallar asuba.  Amma wadansu malamai suna ganin cewa mai I'tikafi zai shiga masallaci kafin ketowar Alfijir.  Kuma bayan yayi sallar asuba sai ya shiga wajen daya tanada domin Iitikafinsa.
Amma mazahabar malikiyya sun fahimci cewa mai Iitikafi zai shiga Iitikafi kafin faduwar rana, bayan yayi sallar asuba sai ya shiga wajen daya tanada domin I'tikafinsa.  Amma sauran malamai irin su Auza'I, da thauri da Laith, suna ganin mai I'tikafi zai shiga wajen I'tikafinsa da zarar yagama
_______________________________________
(1)  Bukhari K = 33, B = 14, H = 2041, da Muslim
      K = 14, B = 1, H = 1172.
sallar asuba domin su sunyi amfani da zahirin hadisin ne. 
Kuma wannan shine zance mafi rinjaye, saboda lafazin hadisin Muslim ma yana karfafa shi(1).
T. SUWAYE YA KAMATA SUYI I'TIKAFI?
A. I'tikafi sunnar Manzon Allah (S.A.W) ce wadda ta shafi maza da mata, domin Manzon Allah (S.A.W) yayi, kuma iyalansa sunyi, harma matar datake da jinin istahala (Mataccen jinni) zata iya yin I'tikafi domin hadisi ya tabbata daga Nana Aisha Allah ya yarda da ita tace:  "Wata daga cikin iyalan Manzon Allah (S.A.W) tayi I'ikafi tare dashi kuma ta kasance tana cikin jinin Istihala".(2).
__________________________________
(1) Mai neman Karin bayani sai ya duba Al istizkar na ibn abdulla bar, (10/311) da sharhin mushin na kadhi iyadh ikmalul mu'allim fi fawaidil muslim (4/154).
(2) Sahihi sunanu Abi Dawuda wanda albani yayi wa tahaliki (2/469) ladisina 2476.
Amma Abin mamaki an manta da wannan sunnar mai albarka, wadda Annabi (S.A.W) ya lizimceta tsawon rayuwarsa, matan sa kuma suka ci gaba da rayata bayansa.
Maimakon Malamai masu kira zuwa sunna su tsaya su rayata, sun bar yara matasane kawai sune suke rayata.
  Ina masoya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) masu da'awar khalwa?
To ga khalwar Manzon Allah wadda ta tabbata daga mafificin halitta Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), ba khalwar shaidanu wadda take haukatar da yara ba.
T. MENENE YA KAMATA MAI I'TIKAFI YA SHAGALTU DASHI?
A. Anfi son mai Iitikafi ya shagaltu da karatun Al'Kurani, da Zikiri da hailala, da Nafil fili da salatin Annabi (S.A.W).  Ba'a son mai I'tikafi ya fita daga cikin masallaci saida larura kamar fitsari ko bayan gida, ko kawar da datti kamar wanka, ko cin abinci ga wanda bai sami wanda zai kawo masa ba.
Yakamata mai I'tikafi ya daina giba da namima da shagala da jin rediyo da surutun banza.  Nana Aisha tace:  "A Sunnah, mai Iitikafi bazai jana'izaba bazai sadu da iyalansa ba, ba zai rungumesu don sha'awaba, kuma bazai fita ba sai larurar da bata da makawa".
Kuma ba'a I'tikafi sai da Azumi kuma sai a masallaci juma'a(1).
______________________________________
(1)  Abu  Dawuda ne ya ruwaito shi maukufi akan Nana
      Aisha, Hafiz bn Hajar ya Ingantashi kuma Albani
      yace hadisine hasanun sahih, sahihisunan
      Abu  Dawuda na Albani (Hadisina 2473).
Babu laifi akai wa mai I'tikafi ziyara.  Musamman iyalansa, don hadisi ya tabbata  iyalan Manzon Allah (S.A.W) sukan kaima sa ziyara ya rakasu zuwa kofa amma baya fita, wasu malamai sun halattawa mai I'tikafi sauraran Ilmi a cikin masallacin da yake I'tikafi, domin Ilmi yana cikin ibadah(1).  Kuma ya kamata mai Iitikafi ya yawaita yin Addu'a musamman dararen da ake saran samun daren lailatul kadari,  saboda burin mai Iitikafi shine dacewa da daren lailatul kadari.
Domin Manzon Allah (S.A.W) ya taba yin I'tikafi a goman tsakiya, da wahayi yazo masa cewa lailatul kadari yana gaba sai ya sake komawa domin ya dace da ita(2).
Mai yin I'tikafi zai iya yin kwana Ashirin, kuma zai iya yin kwana goma ko kwana daya.
Amma abun mamaki yanzu wurin Iitikafi ya zama dandalin surutu, da shagala, da yin labarai, da fita shakatawa a harabar masallaci ba tare da lalura ba, da jayayya, da fada a tsakanin mutane da dauke dauken hotuna, da shiga wajen I'tikafi da mata, da musayar wasiku, duk wadannan sun sabawa sunnar Manzon Allah (S.A.W).
T. YAUSHE NE AKE FITA DAGA I'TIKAFI?
A. Iitkafi yana karewa ne daga watan karamar sallah.  Amma idan mutum ya tsaya a masallaci, to zabinsa ne amma ba I'tikafi yake ba.  Kodayake mazahabar malikiyya  sun fi son yayi hakan, amma suma basuce I'tikafi yake yiba.
_____________________________________
(1)  Duba Sharhin Muslim na kadi iyad 4/157.
(2)  Bukhari
T. YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL KADARI?
A. Ana sa rai da daren lailatul kadari a dararen 21, 23, 25, 27 da 29.  Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi bin Umar (RA) yace, Manzon Allah (S.A.W) yace:  "Ku nemi daren lailatul kadari a wutiri na goman karshe"(1).  Amma hadisai da yawa sun karfafa daren 27.
An karbo wani hadisin daga Abdullahi bin Umar (RA) yace: Manzon Allah (SAW) yace:  "Kuyi kirga don lailatul kadari a bakwai na karshe".(2)
______________________________________
(1)  Muslim (207)
(2)  Muslim (206)
T. SHIN GASKIYANE A DAREN LAILATUL KADARI ANA GANIN KOMAI YANA YIN SUJADA, KAMAR BISHIYOYI DA GIDAJE HARMA MUTUM YA RINKA HANGO KA'ABA DAGA DUK INDA YAKE?
A. Wannan bai tabbata ba daga manzon Allah (SAW) ko magabata na kwarai; ijtihadin wasu mutane ne ba tare da wani dalili na sharia ba.  Amma ya tabbata wasu daga cikin sahabbai "An nuna masu a mafarki cewar daren lailatul kadari yana cikin bakwai na karshe(3)" Wannan hadisin ya nuna cewar an nuna masu ranar ne amma ba wani abu suka gani ba.
Amma ana ganin alamomin daren lailatul kadari kamar yadda Annabi (SAW) ya bada labari cewar
(3) Muslim (Sharhin khadi iyad, 1165)
"Ranar daren lailatul kadari takan fita batayin zafi(1).  Kuma Manzon Allah (SAW)  yace:  "A cikinku wa zai tuna daren da wata ya fito kamar rabin akushi?  Ana fadin daren lailatul kadari sai Annabi (SAW) ya fadi haka"(2).
T. WACE ADDU'A MUTUM ZAI YI A DAREN DA AKE SA RAI DA LAILATUL KADARI?
A. Hadisi ya tabbata daga nana Aisha ta tambayi Manzon Allah (SAW) "Idan naga daren lailatul kadari me zance?
Sai Annabi (SAW) yace mata kice:-
 
Ma'ana "Ya Ubangiji, hakika kaine mai afuwa, kuma kana son afuwa, kayi min afuwa"(3).
_______________________________________
(1)  Muslim, (Sharhin Khadi iyad, 762)
(2)  Muslim (1170)
(3)  Abu Dauda, Tirmiji da hakim suka ruwaito
       shi, Tirmizi ya ingantashi.
T. MENENE HUKUNCIN ALKUNUT, NA KOWANE WUTURI NA SALLA TARAWIHI?
A. Yin kunuti a cikin wuturi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW)  a Ramadhan ko waninsa, amma a kebanci kunuti a cikin wutiri a Ramadhan kawai, musamman a goman karshe wannan bai tabbata daga Manzon Allah ba, ko magabata na kwarai,.  Amma za'a iya yi a huta wani lokaci.
T. MENENE MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI?
A. Zakkar fidda kai sunna ce daga cikin sunnar manzon Allah (S.A.W) Manzon Allah da kansa ya aikata ta, hakama sahabbansa sun aikakata.  Za'a iya fidda ita kafin ganin wata da kwana biyar zuwa goma, domin sahabbai sun aikata haka.
Ana fitar da zakkar fidda kai ga kowane musulmi, yaro da babba, mace da namiji, da ko bawa, kowane mutum mudun nabi hudu.  Amma abin mamaki mafi yawan mutane basu damu da fitar da ita ba saboda da'awar talauci.
T. SHIN YA TABBATA WANDA BAI FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAI BA, ZA'A RATAYE AZUMIN SA, BA ZA'A KARBA BA HAR SAI RANAR DA YA BAYAR.
A. Wannan hadisin bai tabbata daga bakin manzon Allah ba; hadisi ne mai rauni, kuma duk mutumin da ya bari aka sauka daga idi, hukuncin zakkarsa kamar sauran sadaka ne ba zakkar fidda kai bace.
Q.  MENENE HUKUNCIN YIN AZUMI SHIDA A CIKIN WATAN SHAWWAL (SITTI SHAWWAL).
Ans Yin Azumin sitti Shawwal sunnace wadda Manzon Allah (S.A.W) ya aikata, sahabbansa ma suka aikata ta magabata na gari ma suka aikata ta.  Domin hadisi ya tabbata daga Abu Ayubal Ansari yace Manzon Allah (SAW) yace: "Wanda yayi Azumin watan ramadhana, sannan ya bishi da azumi shida a cikin watan Shawwal to kamar yayi Azumin shekara daya  ne (1).  (Akwai wadanda suke ganin karhancin wannan azumin kuma suna jingina wannan Magana zuwa Imam Malik, amma shi (Malik) bai yi inkarin wannan hadisin ba.  Sai dai yana inkari ne ga wanda ba zai iya bambancewa tsakanin azumin ramadhana da sitti Shawwal ba, ma'ana ya hadasu yace duk wajibaine saboda jahilci.  Shi yasa ma ya kara da cewa labari baizo min cewa magabatan Madinah suna yin wannan azumi domin tsoron wannan fitina ta kasa bambancewa.(2).
_______________________________________
(1)  Muslim H. 1164
(2)  Koma Sharhin Muslim na kadi iyad mai
        suna Ikmalul muallim 4/139 muwatta
        kitatussiyan babi jami ussiyam Al istikar na
        ibn Abdul Bar 10/259
Q. MENENE HUKUNCIN WANDA YA DAUKI AZUMI A KASARSA, SAI KUMA YAJE WATA KASAR DA GANIN WATANSU YA BANBANTA DA NA KASARSA MISALI, KAMAR MASU ZUWA UMARA KASAR SAUDIA WANI LOKACIN YA TARAR DA NASU YANA ASHIRIN DA TAKWAS KO NASHI YA CIKA, KO KUMA NASU YA CIKA NASA YANA ASHIRIN DA TAKWAS YAYA ZAI YI?
Ans Binsu zai yi koda nasa zai wuce talatin.
Idan kuma nasa bai cika ba,  kamar ya tsaya ashirin da takwas su kuma sun cika nasu, zai ajiye nasa yayi sallah tare dasu, daga baya sai ya rama abin da bai riska ba, domin hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah yace, manzon Allah (SAW) yace: "Bude bakinku shine ranar bude bakin mutane layyarku itace ranar da mutane suke layya".  Hadisi ne ingantacce.(1).
_______________________________________
(1)   Sunan Abu Dawud H. 2038 Sheikh Albani
            ya ingantashi, a cikin Sahih Abu Dawud
Hakama wajen aikin hajji idan yaje sai ya bisu  koda ako wane irin aiki, kuma koda ganin watan su ya banbanta.
Q.   MENENE HUKUNCIN WANDA YA HAU JIRGIN SAMA DAGA KASAR SA, RANA TA KUSA FADUWA, AMMA BAYAN YA TASHI SAI YA RINKA GANIN RANA?
Ans Ba zai buda baki ba har sai rana ta fadi a idanunsa.
Hakama kuma idan ya tashi akwai sauran rana a kasarsa amma sai ya shiga wani garin wanda yanayin kasarsu ya sabawa na kasarsa.  Ma'ana su a wurinsu rana ta fadi, to sai yayi buda baki. 
Domin hadisi ya tabbata daga Abu Umamata Albahiliy yace, naji manzon Allah (SAW) yana cewa "Naji sauti mai tsanani a bayan wani dutsi sai na Tambaya wannan wane irin ihu ne?  Sai akace kukan wadanda ake yiwa azabane a cikin wuta domin suna yin buda baki kafin rana ta fadi".(1).  Anan ma'ana tunda yana ganin rana to a wurinsa rana bata fadi ba kenan.  Kuma Allah (S.W.T) yana cewa "sannan ku cika azumi zuwa dare"(2).

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now