29- Falalar Karanta Suratul Mulk

122 4 0
                                    

Falalar karanta Suratul Mulk (Tabarakallathi biyadihil Mulk) tazo adunqule sannan kuma Falalarta tazo kafin kwanciya bacci a kebance, *Imam *Tirmidhiy yaruwaito hadisi (2891) da Imam Ahmad a cikin musnad nasa hadisi na (7915) daga Abu huraira Allah ya kara yarda dashi* daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Akwai wata Sura mai aya talatin a cikin Alqur'ani, ta ceci wani mutum har aka gafarta masa, itace Suratu Tabarakallathi biyadihil Mulk), Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahihul Tirmidhiy "_
...•
_*Tirmidhiy ya ruwaito hadisi (2892) da Imam Ahmad (14249) daga Jabir Allah ya kara masa yarda"* Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya kasance baya barci har sai ya karanta Alif laam miim Tanzeel da kuma Tabarakallathi biyadihil "Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahih sunanul Tirmidhiy._
...•
_Abinda yafi shine mutum ya karanta Suratul Mulk kafin ya kwanta barci a kowane dare, saboda irin yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yi, da zai karanta ta a sallarsa ta isha'i to da hakan ya isar masa, saboda gamewar zancen Hadisin farko da ya zo game da ceton Suratul Mulk ga wanda ya karanta ta, domin lokacin karanta ta ba a iyakance shi ba._
...•
_Saidai ba'a shar'anta dawwama akan karanta ta cikin sallar isha'i ba, domin dawwama akan karanta ta nau'i ne na iyakancewa, ita kuma iyakancewa a cikin Ibada bata kasancewa face da dalili, amma don anyi haka lokaci bayan lokaci to babu laifi._
...•
_*Wallahu ta'ala A'alamu.*_
...•
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt