15-Nagartattun addu'o'i guda 10 daga bakin manzon tsira, Annabi Muhammadu (SAW)

296 15 1
                                    


Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbatar a gare shi ya kasance yana yawan ambaton Allah da tunawa da Shi a koda yaushe, kuma a duk halin daya samu kansa ciki.

Haka zalika yana koyar da sahabbansa yadda zasu dinga ambaton Allah da kasancewa cikin shaukin

tunaninsa. Mun dan tsakuro muku kadan daga cikin addu'o'in da Annabi ya kanyi a lokutta daban daban.

1-(Allahumma rzuqni ḥubbuka, wa ḥubba man yanfa'uni ḥubbuhu 'indak. Allahumma ma razaqtani mimma uḥibbu faj'alhu quwwatan li fima tuḥibb. Allahumma wa ma zawaita 'anni mimma uḥibbu faj'alhu faraghan li fima tuḥibb). " (Tirmidhi)

'Ya Ubangiji ka sada ni da soyayyar ka, da soyayyar sauran mutane da zata amfane ni, Ya Ubangiji ka sanya duk abinda ka azurtani da shi ya zamto zai kafafa mini kusantar ka, Ya Allah duk abinda ka hana ni kuma, Ka mai she shi alkhairi a gare ni.' Tirmidhi

2- (Allahumma atina fi dunya hasanatan wa fil akhirati hasanatan wa qina 'adhaba annar.)

Anas Bn Malik yace "addu'ar da Annabi yafi yawaita yi itace: Ya Allah ka arzurta mu da arzikin gidan duniya, da arzikin lahira, Ka kare mu daga shiga wuta." Muslim ne ya ruwaito

3- "Allahumma inni a'oodhu bika min-al-bukhl wa a'oodhu bika min-al jubn, wa a'oodhu bika min an noradda ila ardhali al omr, wa a'oodhu bika min fitnati dunya, wa 'adhabi-l Qabr."

Sa'ad bin Abi Waqqas yace Manzon Allah yana koyar damu wadannan kalamai kamar yadda yake koyar damu karatun Qur'ani.

"Ya Allah ina rokon ka da tsari daga maƙo (ko rowa), ina rokon tsari daga ragonta, ina rokon tsari daga tsufa tukuf, ina rokon tsari daga bala'in duniya da kuma azabar lahira." Bukhari ne ya ruwaito

4- Allahumma inni as'alukal l-huda wattuqa wal 'afafa wal ghina.

Muslim ya ruwaito wani addu'a mai cewa "Ya Ubangiji, ina rokon ka shiriya, da tsoronka, da tsarkaka, Ya Allah ka tsareni daga dogara da wani."

5- Allahumma ighfirli dhambi kullahu diqqahu wa jillahu wa awwalahu wa akhirahu wa 'alaniyatahu wa sirrahu.

"Ya Ubagiji ka gafarta min dukkan zunubaina, kadan ko da yawa, na farko dana karshe, na sirri dana bayyane." Muslim ne ya ruwaito.

6- Ya musarrifa-l quloobi sarrif qalbi ala ta'atik.

"Ya wanda ke sarrafa zukata, Ka sarrafa zuciyata akan yi maka da'a" Muslim ne ya ruwaito.

7- Allahumm anfa'ni bima 'allamtani wa 'allimni ma yanfa'ni wa zidni 'ilma.

"Ya Allah, ka amfanar dani daga abin daka sanar da ni, kuma Ka sanar dani abinda zai amfane ni, sa'annan ka kara min ilimi." Ibn Majah ne ya ruwaito

8- "Allahumma inni a'udhu bika min zawali ni'matika, wa tahawwuli 'afiyatika, wa fuja'ati niqmatika, wa jami'i sakhatika"

"Ya Allah ina neman tsarinka daga raguwar rahamarka a gare ni, da kuma cire kariyarka gare ni, da zuwan azabarka, da kuma aikata abinda baka so."

9- Abdullaji Ibn Mas'ud yace: "daya daga cikin zikirin da Manzon Allah yake yawaita yi itace "Ya Allah ina rokon Ka, Ka sada ni da duk abinda zai janyo min rahamar ka da samun gafarar Ka, da duk abinda zai tsare ni daga aikata sabo, kuma ya shigar dani Aljannah tare tseratar dani daga shiga wuta."

"Allahumma inni as'aluka mujibati rahmatika, wa 'aza'ima maghfiratika, was-salamata min kulli ithmin, wal-ghanimata min kulli birrin, wal-fawza bil- jannati, wannajata mina-nar."

10- Ibn 'Abbas yace "Manzon Allah S.AW yana karanta wannan addu'ar idan ya shiga cikin damuwa: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah madaukakai mai rahama, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin al'arshe, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da kassai, kuma Ubangijin Al'arshe mai girma.

"La ilaha illallahul-Azimul-Halim. La ilaha illallahu Rabbul-'Arshil-'Azim. La ilaha illallahu Rabbus-samawati, wa Rabbul-ardi, wa Rabbul-'Arshil- Karim.

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now