4- Lakad Jaa'kum ( Fassara da Falalar karantasa)

846 17 0
                                    

بِسْم الله الرحمن الرحيم

لقد جاءكم رسول من انفسكم عزيز عليه ما عَنِتُّم حريص عليكم بالمؤمنين رءوف رحيم . فان تولوا فقل حسبي الله لا اله الا هو عليه توكلت و هو رب العرش العظيم.
  Laqad jaa'akum rasuulun min anfusikum aziizun alaihi maa anittum hariisun alaikum bil mu'uminiina ra'ufun rahim(un) . Fa' in tawallau faqul hasbiyallahu la ilaha illa Huwa alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul  arshil-aziim.

FASSARA:
Lallai tabbas Manzo ya zo muku daga cikinku, duk abin da kuka wahala a kansa mai buwaya ne a gare shi, kuma shi mai kwadayim (samun shiriya) a gare ku, kuma shi mai tausayi ne, mai Jin kai ne ga muminai. To Idan suka ba da baya ( ga barin shiriya) to ka ce Allah ya isar min, babu abin bautawa da cancanta sai shi, a gare shi na dogara kuma shi ne Ubangijin al'arshi mai girma. ( Tauba: 128).

FALALAR LAKAD JA'AKUM:
Duk wanda ya karanta ta ko ayarta ta karshe wato, " Hasbiyallahu la ilaha illa Huwa alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-arshil Aziim". Lalle Allah ya isar mani, babu abin bauta sai shi, gare shi na dogara, kuma shine ubangijin al'arshi mai girma. " Duk wanda ya karanta ta sau bakwai (7) kowace rana da safe da yamma, lalle Allah (SWT) zai isar masa dukkan damuwa ta duniya da lahira ( Ibn Sunni).

DUA BOOK OF OF A MUSLIMAH ( Hausa Version)Where stories live. Discover now