*YAR BABBAN GIDA*
©Khadeeja Ahmad
®Excellent writersFor *Pherty n miemiebee*
💕7💕
*Alee*
Kafin a bani gadon mu, nasa a raina bazan tab'a samun Fatima ba, ina tunanin duk sanda na fad'a mata my feeling toward her har dariya zata iya min ganina talaka mara abinyi se harkar 'karfi da sauran su, ko danginta bana jin zasu tab'a yarda duba da statues nasu,.
Hawaye masu zafi suka zubo masa tuna wa da wasik'ar mahaifinsa,*Alee kai da maryam kadai ne 'ya'yana, kai ne babba dan haka ga dukiyar ku nan, kuyi duk abinda zakuyi da ita, na yarda da kai, nasan yanzu kasan mene rayuwa, kasan babu, zuwa yanzu nasan ka dad'a girma kayi hankali , im proud of you Aleeyu, ka kula da maryam sosai dan kai kad'ai ne gatan ta a yanzu*
Jin motan ta tsaya yasa ya zari tissue ya goge fuskar sa kan ya fita cikin takun sa na isa ya shige office.
***
Tsuga gudu take tamkar zata tashi cikin sabuwar jar motar ta kirar ferari wacce take gift d'in da Pa ya bata na bday, had'e da gifts d'in kwana biyu ba tare da guards ko nannies ba, bata tsaya ko ina ba se gidan su Miemie, thou da tazara sosai tsakanin su amma haka ta taho ita d'aya duk dan taga Alee,Na yarda da son gaskiya, dan soyayyar gaskiya is hard to fnd, idan kuma ka samu dole ka jajirce mata dan ba'a tab'a replacing da wata...amma meyasa Miemie taki bani number sa, wato ita me yaya...well may be haka zanyi da nice ita.
Wani abun mamaki se najiyo karar TV tun 'karfi daga ciki, a hankali na bud'e falon inda nayi kicib'is da wasu maza biyu kallon juna sukayi kan suce dani sannu na raku'be suka shige na waiga falon inda na hango shi, my husband to be, uban yayana, my future my everything, mutumin da nake fatan aura ba ruwa na da ko wani za'bi mahaifana sukai min, zan tsaya tsayin daka dan ganin na mallaki abinda raina keso. kwance yake waya a hannunsa yana daddan nawa. Wani matashin saurayin dake zaune gefensa yace"Yallab'ai kayi ba'kuwa"
Ba tare daya d'ago kai ba yace "ita ba'kuwar bata da baki"
Matashin ze kuma magana ya d'aga masa hannu tare da cewa
"Bani wuri Abdul" saurayin ya tashi ya fita, duk kunya ta rufe ni ganin yacce ya gwanya ni gaban abokin sa, kusan tsayin minti ashirin nayi a haka kan ya d'ago narkakkun idanunsa yace"Me kika zo yi anan!"
"Inason magana da kai ne"nace had'e da gintse lips dina na kasa.
"Ba maganar da ta rage tsakanin mu"
"Ya Alee..."
"Kije gida Fatima , ban buk'atar ki a rayuwana abin da na fad'a miki mistake ne"
"Meye laifin so Ya Alee?, tamkar mayan karfe yake idan ya shige ka is hardly ya fita a zuciya, Ya Alee inajin sonka har cikin raina .."
Hannu ya d'aga, "dan Allah mafarkin naki ya isheni, ni bana sonki, abinda na fad'a miki kuma mistake ne" dariya yayi had'e da kissing screen din wayar sa,"Ke kad'ai raina ke so kuma ke zanci gaba da so har k'arshen rayuwata...kinganta wannan ce rayuwata" ya shuna mata wayar, d'auke kai tayi, had'e da dafa k'irji jin da tayi tamkar an dab'a mata wuka a kirji..dakyar nake iya jan numfashi, ya Allahu, *na tsane shi na tsaneshi*, kuka nake son yi na gudu daga wannan cin mutuncin da yayi min, can bakin kofa na hango wata kyakkawar budurwa da tasha bak'ar abaya se murmushi take min, nan da nan na had'e rai na rab'a ta gefenta na wuce...
"Princess", cak na tsaya na waiga a hankali,
wani murmushin yayi kan yace, "nasan kina da kyau hakan yasa na fad'a miki kalmar da na fad'a ma yawancin yammatan da suka halacci gurin bday party dinki kasancewar suma sun min kyau!, so don't make it a big deal!"
Cikin zafin nama na fita da sauri na shiga mota na rufe, tun 'karfi na fashe da kuka, kukan da nake gani shi kad'ai ne ze sanyaya raina na fitar da ba'kin cikin da Alee ya 'kunsa min, wani irin ciwo nake ji a zuciyata, i felt lyk dying inside.
Knockn glass a kayi, na d'ago fuskana taf da hawaye, na d'an goge da bayan hannuna kan na wining glasses d'in,
"Kyakkyawa, irin wannan gudu haka baki tsoron fad'uwa, gashi kuma kina kuka dafatan de ba wani mugun abun akayi miki ba?,"
Idona da suka kad'a na sauke kansa kan nace komai, yace, "karki damu inde Alee ne ya saba koran 'yammatan da suke kawo tallan kansu.."Tallan kansu? wato ma har da wanda ke zuwa takanas wurinsa?, kenan shine yayi treatn d'ina lyk one!, wasu sababbin hawaye suka siraro min na kauda kai gefe tare da rintse ido dede lokacin naji saukar yatsu a fuskana nayi saurin bud'e ido na bige hannun mutumin cikin 'bacin rai nayi saurin d'ora hannu zan rufe glass d'in ya ri'ke min hannu tun 'karfi ya zuro 'katon hannun sa ya bud'e motar na rin'ka kicin kicin d'in kwacewa amma na kasa,
"Dan girman Allah kar ka min komai, kayi ha'kuri zan baka duk abinda kake so amma kar ka ta'ban lafiya ta, please na shiga kuka tun 'karfi ina dukan sa amma ko gezau mutumin nan, wani irin duka aka kaiwa mutumin take ya sakeni ya zube 'kasa yana numfarfashi.Alee ne!, idanunsa sun yi jazur fuskar nan a murtuke tamkar zaki a filin daga, se numfarfashi yake, cikin 'karaji yace
"Kada ka'kara ta'bata ko da wasa" ya nuna sa da yatsa , sannan yace "tashi ka fitar min a gida kan na karairaya ka!!"
Tsam ya mi'ke ya fice, sum sum sum nima na nufi cikin mota,
"Princess.."ya kira ta cikin murya me d'auke da nadama
Banza nayi dashi na shige mota, se ya zare key ya juya zuwa cikin gidan,
K'asa na zube tamkar yarinya ina tittirza 'kafafu cikin kuka, "Allah ka bani key d'ina, tunda ba naka bane"
Tsugunna wa yayi setin fuska ta, idonsa d'auke da nadamar abinda yayi, cikin sanyin murya wacce ke bu'katar yarda yace
"Fatima..."kiran sunana da yayi tamkar ya harba mashin wuta a zuciyata naji, na runtse ido tun karfi na shiga kuka, ban damu ba if he saw how hurt i was.
" Fatima dan Allah ki saurareni...""Ka dena ta'bani da Allah.."na fad'a tare da kai kallona kan hannunsa dake kafad'a ta, saurin d'auke wa yayi, yace
"Kiyi hak'uri da maganar da na fad'a miki har ga Allah na fad'a ne kawai ba har zuciyata ba, ki yi hakuri uhm?, what can i do to make it right?"
Kin sauraren sa nayi dan ina jin ciwo a zuciyata har yanzu cox it's so deep!
Abu d'aya na fahimta shine, Alee was not worth fighting for. Ba ze yiwu nayi auren soyayya ba. Ma da Pa sunyi gaskiya Ubaid shine wanda yayi dede dana aura.©Kdeey😊

YOU ARE READING
YAR BABBAN GIDA
RomanceNa tsaneki at thesame time ina sonki, inajin tamkar na cilla ki ta saman bene na garzaya na taro ki gudun karki fad'a kiji ciwo~ *Alee* ♡ yacce kake nuna min halin ko oho yana ba'kanta raina mutu'ka~pherty ♡ kin gusar da duk wani manufata a kanki~Al...