Tawa ce

809 61 0
                                    

*YAR BABBAN GIDA*

©Khadeeja Ahmad
®Haske writers asso

For *Pherty n miemiebee*

           💕25 💕

Apology text ya shiga tsarawa me sanyaya ran masoya tunda pherty ta karanta fushi ya bar zuciyarta dama be kai zuciyar ba kawai de dan ta rikita masoyin nata ne dan ta riga da tasan waye Alee he has no other girl apart from her! Alee nata ne ita kad'ai❣

Can 'bangaren Alee kuwa bayan ya gama tura mata text tashi yayi zuwa cikin gida inda ya samu Miemie zaune ta kafa uban tagumi a rikice ya 'karasa gabanta
"Sis me" firgigit tayi

"Ya Alee?"

Kwalla ya gani kwance cikin idanunta, ai se ya kuma rud'ewa ya shiga watso mata tambayoyi, "menene? Meke damunki? Bakyajin dad'i ne?..."

Jan hanci ta shiga yi tare da rungumosa cikin muryar kuka take cewa

"Ya Alee ina tunanin rayuwa ba tare da Kai a kusa dani ba, tun da nayi wayo Kaine uwata Kaine ubana bansan nayi nesa da Kai.."

"Shhhhh..." Ya shiga shafa sumar kanta yana fad'in,

"Stop crying sis me, ba abinda ze nisanta mu kinji, ki sani shi aure ya gaji haka dole 'ya mace tabar gidan su zuwa d'akin mijinta, amma hakan ba yana nufin sun rabu da danginta kenan ba Sam! Sema sabuwar dangantaka da zata dad'u tsakani da 'Karin 'kima da zaki samu ba gun 'yan uwanki kad'ai ba a idon duniya baki d'aya, Sis me marriage is such an important step that our blessed prophet (S.A.W)spoke of marriage as being cikon addini,
'Duk Wanda yayi aure tamkar ya cika addinin sa ne therefore yaji tsoron Allah cikin dukkan abinda yasa gaba' (bayhaqi).."

haka Alee yaci gaba da yi mata nasiha me kashe jiki, kukan da take ya tsaya 'kaf haka taji wani sanyi ya malale zuciyarta tare da wani irin 'karfin zuciya.

KWANA BIYU KAFIN YAU🔙

Alee da Ansar

Ansar : "Salam, Allah yasa ban tashe ka ba"

Alee : " wslm a haba ka ganni zaune a office Ina duba wasu files ne"

Ansar : office? Ina kabar min iyalina?

Alee : yayi dariya "iyalinka na gida lafiya 'kalau"

Ansar : "to Masha'Allahu dama Abba ne ya bani sa'ko na fad'a maka.

"Inajinka Ansar fad'amin sakon Alhajin" yace da sauri
Ansar yad'an gintse "dama yace amm..."ya fashe da dariya jin yanda Alee ya bashi full attention tamkar me shirin d'aukan darasi.
Sanyaya murya yayi "haba yayanmu dan Allah ka fad'amin duk kasa narasa sukuni"

"Kwantar da hankalinka ina me farin cikin shaida maka Pa ya baka go ahead daka turo magabatanka ya baka Pherty halak malak"

"Allahu Akbar"itace Kalmar data bar bakin Alee kan ya tsugunna yayi sujjada ya d'ago 'kwalla fal idonsa wacce ni Kdeey na kira da kwallar farin ciki,
"Hello kanajina?"

Sai da ya sauke numfashi yace "ina saurarenka Ansar, yau ta kasance ranar farinciki ta biyu a rayuwa ta wanda zan Adana cikin kundina a yau an mallaka min halittar dana fi so bayan annabin Rahma da mahaifana"

"Kar ka damu nima ka shaida wa manya inason na turo dan Pa yace ranar da aka saka na d'aurin auren ta da Ubaid a ranar za'a d'aura naku nima kuma za'a had'a da nawa nan da kwana bakwai kenan, a huta lafiya.."

"Ansar ka shaida wa Pa jibi around 11 magabata na zasu zo Insha'Allahu, nagode nagode nagode Ansar" yana kashe wayar 'kanin mahaifinsa na bauchi ya kira ya shaida masa ya shiga ya tarar da Miemie waya a kunne ta rufe hannu a fuska da alama ita da Ansar ne murmushi yayi ya juya designers yashiga nema ta ta kafofi da dama dan d'an zaman sa da Pherty ze ita 'kiyasta size nata a tsayi bazata wuce 58 ba ragowar kuwa baze kasa samu gun Miemie ba haka kuwa akayi ranar da kwana biyu kaya suka iso intact cikin akwatunan su wanda suke na kamfanin Versace ko wanne akwati da farkon sunayensu *Z&A* golden seti 34. Tir'kashi wani kayan se amale..

***

Pherty ta shige side d'in Ma sede me turus tayi a harabar falon ganin yacce akwatuna sukaiwa tsakar falon 'kawanya

Ayyiririyiriri.....wata dattijuwa taja gud'a kallonta pherty tayi galala, nan fa falo ya hautsine da yan gud'a wasu suka shiga cewa barka barka amarya kaya sunyi kyau kwarai Allah yasa gidan kine yasa mijin kine har a aljannah.. Can wata tsohuwa ta jata

"Taho 'yar nan zo ki shige d'aka kada su dad'a miki gajiya"

Pherty de binsu take da ido jiki a mace tambayoyi na mata yawo a ka, band'aki ta fad'a ta shiga watsa was fuskarta ruwa a cewarta ko mafarki take ganin ba abinda ya sauya yasa ta fito ta hanyar baya ta zagaya zuwa sashen Noor da Ansar nan ta tarar a gar'kame,

"Babban Yaya ya fita, 'karamin kuma sun wuce bauchi" cewar d'aya daga cikin ma'aikatansu, kan tayi magana tuni ya bar wurin dan haka d'aki ta koma shigarta ke da wuya baba Rabi ta shigo biye da Ngozi wacce ke d'auke da tray na abinci.

Ajiye wa sukayi bayan sun mata sannu ganin yau me d'akin nasu ta lula duniyar tunani,

"Baba taron me ake haka a gidan nan? Ina Ma?, akwatunan waye wayancan kuma wace magana naji anayi a falo yanzu?"

Baba Rabi wacce har ta isa 'kofa ta juyo a nutse tare da fad'in..

©Kdeey😊

YAR BABBAN GIDAWhere stories live. Discover now